← Book details Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 19

Sashe 12

Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel · about 5 min read

kara maka yawan rai). Ina kan layi. Muryar Askirama mai zurfi da kauri (husky) ta bakunci kunnuwanta. Bana zaton Yareema ya gaya miki sakona. Cewa na yi ki share dakin Saadatu ki zauna, don ba ki da daki yanzu a gidana. Cikin gatsali ta ce, Allah ya kara yawan rai wani abu aka ce na yi? Ziyara fa kawai na kawo musu. Ta fashe da kuka, kukan da daga ji za ka san bana gaskiya ba ne. Don takaici Mai Askira sai ya kashe wayarsa, kada ya yi abin da zai zo daga baya yana nadama. Ya Gumsu ta shiga bandaki a washegarin ranar za ta yi wanka. Ta sa kafa a cikin bahon wanka ba ta lura da jikakken sabulun da ke ciki ba, kafarta ta sauka a kan sabulun ta zame ta tafi gabadaya ta yi wata irin mummunar faduwa. Faduwar da sai daukanta aka yi ranga-ranga zuwa asibiti baki ya karkace yana ta fidda kumfa. Idan Ubangiji ya nufi alamari, bawa ya nuna ja da hukuncin Ubangiji, sai Ubangiji ya barshi da dabararsa, amma idan Ya ga dama talalar da zai maka ta dare daya ce. Wani rabon sai ya kawar da kai dagadoron duniya gabadaya. A ci gaba da rayuwar babu kai, babu mai tuna ka da kyakkyawar zuciya balle ya yi maka addua. Don haka Gumsun Askirais lucky that shes alive a daidai lokacin da Saade ke jikin mahaifiyarta tana ta kelaya amai kamar da bakin kwarya. Tunda ta iso ta ke zazzabi da ciwon kai, kafin wayewar gari kuma sai haraswa, ta kasa cin komai, gabadaya ta fige ta yi zuru-zuru. Fulani da Fanna suna tsaye a kanta tun jiya. Shi ma Maimartaba ba ya rufa awa guda bai kira Fulani ya ji me Saade ta ke ciki ba. A karshe ya turo likitar matan gidan don ta zo ta duba ta a san takamaimai me ke damunta. Ita dai Fulani tuni ta sha jinin jikinta. Tun daga sanda Saade ta ce ba ta son warin turarenta. Amma kuwa Yarima bai kyauta ba, ya saba alkawarin da ya yi mata. Saade is too young da haihuwa wani matsanancin tausayi ya kama ta. Amma da ta tuna ba haramci suka aikata ba sai ta rage wa kanta damuwa. Wannan rabo na kurkusa da kofar daki ina Ya Gumsu za ta kai shi? Ko kusa abin da Ya Gumsu ta yi wa Saade bai sa ta ji tana so a raba auren ba, ko don ganin halin bacin ran da Askirama ke ciki, wanda ko ita da ta haifi Saaden abin bai tabata har haka ba. Ta sa a ranta Ya Gumsu za ta yi fiye da wannan in dai a kanta ne. Kuma a washegarin ranar bayan fitar Dr. Zainab da ta duba Saade ta tabbatar wa Fulani akwai ciki na sati Shidda, ta shiga don ta yi wa Askirama wannan albishir ta ji yana amsa waya. Sai kuma ta ji ya ce, Stroke? Cikin tsananin mamaki. Gumsun da ko jiya na yi magana da ita a waya lafiya lau? Aka yi magana daga daya bangaren wanda ita ba ta ji ba, sai ta ji ya ce, Ai shi ke nan, Allah ya ba ta lafiya. Yayanta sai su je Abujar su yi jinyarta, amma Allah ya gani ni ba zan zo ba Daja, yar uwarki ta girma ba ta san ta girma ba. Na dade ina hakuri da halayenta ta kasa gane gata na yi wa rayuwar Yareema da shi bakidaya da na aura masa Saadatu. Babu yadda ban yi da ita ba ta karbi hukuncin Ubangiji, ta nuna min ta hakura har za ta kai musu ziyara, shi ne ta yi tattaki har dakin yarinya, ta ci zarafin marainiyar Allah ta koro ta tun daga Abuja har Maiduguri da Askira ita kadai a wannan marrar ta satar dan mutum kamar satar takalmi. Don haka ina nan a kan bakana, Gumsu ta ci gaba da maye gurbin Saadatu wajen Yareema Sageer. Babu Saadatu babu danta, sai ranar da ta yo tattaki har dakin Bilkisu ta ba ta hakuri a kan cin zarafin da ta yi wa yarta. Ta kuma furta da bakinta cewa ta amince su ci gaba da zaman aure da bakinta. In ba haka ba shi ma Yariman kada ya sake ya tako min gida. Yana gama fadin haka ya kashe wayarsa yana maida numfashi cikin bacin rai. Fulani Bilkisu ta karasa ta gurfana a gabansa, tafukan hannunta bisa tafin kafarsa. Cikin muryar lallashi da son kwantar masa da hankali ta yi masa albishir din da ke bakinta. Da gaske? In ji Askirama. Cikin excitement din da ba zai misaltu ba. Ta kashe shi da lallausar murmushi, ta ce, Da gaske Dr. Zainab ta tabbatar da ciki na sati shidda a jikin Saade. Sabida haka Askirama ka yi hakuri da duk wani bacin rai, tunda Ubangiji ya nuna mana ayarsa. Idan ta warware kwana biyu a manta da komai a mayar wa da Yarima matarsa. Mai Askira ya girgiza kai ya ce, Ayoyi kam ai muna ta ganinsu. Yanzu kanwarta ta kira ni ta shaida min cewa, suna asibiti da Gumsun Gari, ta fadi a bayan gida ta samu stroke. Innalillahi wainna ilaihi rajiun. In ji Fulani. An gaya wa Yarima da su Yaa Maira? Cikin damuwa ya ce, Yarima ya taho tun jiya ta mota, babu jirgi, amma Awaisu ya gayaminya samu minor accidentahanya, bai ji ciwo ba amma ya bugu, kuma motar sa ta jikkata, ya iso Askira tun jiya, ni na ce da Awaisu ya gaya masa kada ya sake in ganshi gabana ko bangarenki. Ya Maira kuma sun kama hanyar Abujan. Cikin dimbin alhini Fulani ta ce, innalillahi wainna ilaihi rajioun. Zama bai ganmu ba, ya kamata a shirya mana tafiya mu uku, ni da Yakirjinoma da Hibbani. Yareema na tabbata Awaisu zai bashi duk kulawar data dace, amma don Allah Askirama ka bar shi ya dawo gidan nan. Ya yi ajiyar zuciya, wannan karon cikin muryar sa akwai sassauci, ya ce, Su za su je, amma ban da ke. In kin tafi wa zai kula min da Saadatu da Chiroman Gari? Ta yi murmushi kadan, jin har ya bai wa dan cikin Saade Sarauta tun kan ya iso duniya. Ta ce, Fanna za ta kula da su sosai. Bai kamata a ce su sun tafi ni na zauna ba, sai ta dauka sabida abin da ta yi wa Saade ne wanda ni sam bai shafe ni ba. Ta kare zancen ta da cewa. Ai Saade yarta ce! Koda bata auren Yarima.
Chapter 12 · 0% Book details