← Book details Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 19

Sashe 2

Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

What do you want to eat? (Me ki ke so ki ci). Yareema ya tambayi Saade.
Shiru ta yi masa kamar ba da ita yake magana ba. Ya yi kwafa ya ci gaba da tuki. Ya rasa gane inda ta sa gaba, in laifin da ya yi mata jiya ne ai ya ba ta hakuri, ya kuma karbi laifin sa. Yayi duk irin lallashin da ya kamata. Wannan shirun da ta ke masa yana ci masa rai. Ya ci gaba da tukinsa yana tunanin ta inda zai billo mata.
A hanyar fita garin Jos ya tsaya ya saya musu gasasshen nama mai laushi, kuma mai yawa, ya hada musu da gorar ruwan swan mai sanyi, sannan suka sake daukar hanya.
Ya bude naman ya ajiye a gefenta, kamshinsa ne ya tado mata da tsohuwar yunwa kuma da ma dai akan abinci ba ta iya filako. Don haka ta yi fuska abinta ta hau cin nama cikin yanga.
Ta gefen ido Dr. Sageer ke kallonta yana murmushi, komai na Saade burge shi yake ba tun yau ba. Suna cikin tafiya wayarsa ta yi kara, da ya duba sunan Ya Gumsu ne. Sai da ya ji gabansa ya fadi, har fargaba yake magana ta sake hada su. In dai alkawarin da ya yi mata ne ai ya cika.
Saade ido kawai ya zuba mata sai dan abin da baa rasa ba, wanda dan Adam ba shi da iko a kansa. Tsoro yake kada ta yi masa maganar Hajjaju shi ya sa da ya je mata sallama bai gaya mata tare da Saade zai taho ba.
Amma ya san bai isa ya ki daga kiran mahaifiyarsa ba. Duk irin rigimar ta, wadda ta diga masa jinin haihuwa ta dauki cikin sa watanni tara ta haife shi cikin wani hali na kaka-ni-kayi ba tareda taimakon kowa ba.
Don haka ya rage gudun motar ya amsa kiran Ya Gumsu da sallama cikin tsantsar ladabi. Ko amsawa ba ta yi ba ta jefo masa tambaya.
Da gaske da yarinyar nan ka tafi Abuja?
Yareema Sageer ya yi shiru cikin rashin sanin abin cewa.
Ya Gumsu ta yi kwafa, cikin tsananin hushi ta ce,
Watanni uku na ba ka ka zo a yi maganar auren ka da yar Sarkin Bauchi (Hajjaju) kuma watanni uku na ba ka ka sako mata yarta, idan ba haka ba ALLAH YA ISA haihuwarka da na yi, na sallama ka ga Bilkisu da yarta.
Tana gama fadin hakan ta kashe wayarta.
Yarima ya ja wani irin birki a tsakiyar titi, ji ka ke kuuuu! Saura kadan ya buga wa motar gabansa. Daga shi har Saade suka jirkito sannan suka koma mazauninsu daidai kasancewar duk da belt a jikinsu.
Da sauri ya sa wa motocin bayansa signal, sannan a hankali ya sauka gefen titi, ya danna wani abu gilassai bakake (tinted) suka maye gurbin masu haske. Saadatu ba ta yi aune ba sai ji ta yi Yareema Sageer ya jawo ta jikinsa da karfi ya rungume ta, cikin kunnuwanta yake rada mata.
Cikin kowanne hali kada ki rabu da ni Saadatuh!
Shiru ta yi, bugun zuciyoyinsu na bugun kirjin juna. wani irin moment ne mai wuyar fassarawa ga Saade komai na Yareema ratsa ta yake har cikin kwakwalwa his gentle touches, his sexy voice, and everything da yake yi a yanzun. Kasa magana ta yi, domin gabadaya Yareema ya gama rikirkita duniyarta da zuciyarta cikin dan lokaci kalilan.
Ta ga ba shi da niyyar ci gaba da tukin motar ga yamma na yi musu, ga shi ba ta san iya inda za su je ba, don haka ta janye gefe tana regaining consciousness. Lokacin ne ya ja motar suka ci gaba da tafiya. Amma sabanin lokacin tahowarsu ta lura wannan karon akwai babban abin da ke damunsa tun wayar da ya amsa.
A hankali kuma barci ya dauke ta. Ba ta farka ba sai da suka shiga garin Bauchin Yakubu. Nan ma ta dauka masauki zai nema musu musamman tunda dare ya yi, amma sai ta ga ya kara nikar hanya.
Ba ta so Yareema ya ji muryarta balle ya yi tunanin ko ta huce daga fushinta (sunan littafin Takori mai zuwa, NAHUCHE), shi ya sa ta yi masa shiru. Ba su dade suna tafiya ba ya karya kan motar suka hau titin da ta ga sign board dinsa zai kai mutum ne YANKARI GAME RESERVE.
******

Yankari game Reserve and Resort na nan a Wikki Camp. Yankari na daya daga cikin Nigerias Foremost Tourist attractions, ana kuma kiransa (home of wild life) saboda wadatar manyan namun jejin da ke cikinsa.
A ciki akwai hotel domin maziyarta wato Marshall Suit a nan Yareema ya kama musu daki V.I.P Room.
Kwarai attraction na Yankari ya dauke hankalinta har ta manta fushi ta ke da Yareema, duk da cewa dare ya yi musu amma koina haske yake da fitilu kamar rana. Ba ta san lokacin da ta dora hannunta a kan na Yareema ba, wanda ke bisa birkin mota.
Uncle au? (ta toshe baki da ta tuna ya hana ta kiran sa Uncle) Prince, kwana za mu yi? Kwana nawa za mu yi a nan?The place is quite attractive and I like it.
Mutane da yawa na kiransa Prince, musamman abokai, amma bai taba jin wanda ya fada with correct accentdawankakken harshe da makogaroirin Saade ba. Bai san sanda ya yi murmushi ba don ya ji dadin sunan da ta canza masan. Ya dube ta da gajiyayyun idanunsa irin na wanda ya sha tukin mota ya gaji,
In kin yarda za ki yi min tausar tukin nan da na sha, kuma za ki ba ni baby in sa masa suna Dan Yankari, ko kwana nawa ki ke so mu yi sai mu yi abinmu, tunda babu mai jiran mu ko neman mu.
Da sauri Saade ta kai tafukanta ta rufe fuskarta, kunya kamar ta yi ya ya, da ta san abin da zai fada kenan da ko kusa ba ta nuna shaawar wajen ba har ya gane ya nemi reward.
Reward din da duka cikin biyun da ya ambata babu wanda ta ke jin za ta iya, don sosai ta ke ganin girman Yareema Sageer, ta kasa accepting reality na kasancewarsa miji a gare ta har zuwa yanzu. Har gobe kallon matsayinsa na baya ta ke masa (Uncle/Guardian) duk da he seldom kisses hera duk lokacin da ya bukaci hakan a kwanaki bakwan su tare, cikin siga mai nuna tsananin bukatuwar miji zuwa ga matarsa (physical urge).
Suna shiga dakin nasu ko zama ba su kai ga yi ba Saade na ajiye handbag dinta akan kujera wayar Sultana ta shigo wayarsa. Bai ki amsawa ba, amma da ya daga wayar bai ce komai ba, sauraron ta yake yi.
Sultana ta ce cikin fushi.
Sageer ina ka shiga ne har yanzu ban ganka ba? Na dawo aiki tun dazu ga Uche baya gidan
Ina inda ki ka aike ni tare da amaryata. Ke da ganina sai ranar da ki ka karbi addinin musuluci da gasken-gaske, sai kin tuba kin bar giya gabadaya, if not ki kama hanyar Korea ba ni da ranar dawowa.
Wani ihu Aisha-Sultana ta saki a cikin wayar, You are lying you cant do this to me Sageer remember Im your Rose, wadda ta bar kasarta da addininta ta shigo wani saboda kai.
Ya ce, sabida jiki na dai. Notbecauseofme, in sabida ni ne you can sacrifice everything for my sake, you will give me children. Abu daya nake dubawa da ya sa ban sake ki ba a jiya; mahaifi na baya barin saki.
You hurt my father ko gaisuwa ta ya daina amsawa. Sultana ina yi miki sallama, na gaya miki in bazaki iya barin giya ba zaman mu ba zai taba dorewa ba, kin cire mahaifa ba da sanina ba, kin dauke ni kawai a matsayinsex slave ban yarda da wannan soyayyar taki ba. Na ba ki zabi, ko barin GIYA ko komawa Korea ne ko Amsterdam ke ki ka sani....
Yana gama fadin haka ya kashe wayar gabadaya ya ajiye ta gefen bed side-lamp. Saadatu tuni ta shige toilet da ta fahimci sensitive magana yake yi da matarsa.
Chapter 2 · 0% Book details