← Book details Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 19

Sashe 16

Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Matar nan ta jima tana cutar da ita, da harshenta, da bakin ta, da hannunta, da komai nata. Don ma dai kowa ya tabbatar cewa ba ta yin asiri ta tabbata da in akwai abin da ya fi shi sai ya Gumsu ta yi mata. Wannan sai Hibbani, shi ya sa ita din ba ta wasa da addua da tsayuwa gaban Sarki Allah a tsakiyar kowanne talatainin dare.
Ta nisa ta dubi yarta Saade, ta ce, Saadatu marriage is not a bed of roses. Babu wani aure da ba shi da kalubale, ki sa a ranki Gumsu ita ce kalubalen aurenki, kuma ga yadda abubuwa ke tafiya na fahimci tsoron Allah ya kama ta. Ki cire ta a ran ki ki yi wa mijinki mai sonki biyayyah, komai za ta yi miki ta yi kadan ta raba wannan auren tunda har ga zuria a tsakani.
So ni da Ya Gumsu yanzu mun zama JINI DAYA. Kun riga kun yi tiding wannan barakar da ke a tsakani. Ni kuma ko me ta yi mun a baya na yafe mata. Allah ni ma ya yafe mini, ina kuma rokonsa ya ba ta lafiya ta koma taka kafafunta a doron kasa.
Kuma tunda kin warware ki soma shirin komawa dakinki tun kafin Yareema ya zubar da kawaici da kunyar da ke tsakanina da shi.
Dazu ya roke ni Fanna ta raka ki dakinsa na gidan nan yana son gaisawa da babynsa tunda Askirama ya hana shi shigowa nan. Ni kuma bazan yi abunda in Askirama ya ji zai yi fushi da ni ba.
Tunda har ya cire kunya ya fadi gaisawa da baby kin ga daga hakan wata rana abin da zai gaya min sai ya fi haka.
Saade ta soma tirjiya, har da buga kafa na shagwababbun yaya,
Ni wallahi ba yanzu zan koma ba, abin da jinyar Ya Gumsu suke yi? Ko na koma ba shi da lokacina.
Fulani ta ce, Duk inda yake in dare ya yi ai zai dawo gidansa ne Saadatu. Dare mahutar bawa, don haka na gaya miki ki soma shiri, ba za ki kara kwana uku a sassan nan ba. Yau din nan zan bai ma Askirama baki, har ga Allah Yareema tausayi yake bani don ba shi da laifi.
Saade har da hawayenta ita ba za ta koma yanzu ba sai Ya Gumsu ta warke.
Warkewar da babu wanda ya san ranarta sai Allah?
In ji Fulani cikin lallashi.

Kamar yadda ta alkawarta da yake yau ita ke da Mai Askira, tare suka je suka duba Ya Gumsu. Da lokacin kwanciyarsu ya yi ta yi ta ba shi hakuri kan ya sassauta wa Yareema, cikin alamarin nan ba ta ga laifinsa ba, tunda shi bai ma san Ya Gumsu za ta je Abuja ba, kuma sanda ta je din Saadatu ta tabbatar mata shi ba ya gidan, sannan abin da ya faru da Ya Gumsu kadai ishara ce babba, Allah ya nuna musu su dukkansu a daina jayayya, a bar wa Allah ikonsa.
Zuciyar Maimartaba ta tausasa, shi ya sa yake son Bilkisu amma matansa sai su ce wai kyawunta ne. Me ake da kyau in ba hali? Ai ga Hibbani nan kyau har kyau, amma ban da gulma, tsugudidi da daukar zance ba ta iya komai ba.
Ya ce ya yarda a je a gyara musu gidansu kafin su koma. Ya kuma kira Yareema don ya ji yaushe za su koma Abuja. Yareema bai boye ba, ya ce da Askirama ya ajiye aikinsa da NTNU, wani zai nema.
Cikin mamaki Mai Askira ya ce, A kan me?
Yareema ya runtse ido, tuno cewa Ziyad ya ga tsiraicin Saade kadai yana kona zuciyarsa yana tafasa ta ba dan kadan ba.
Ya ce, Allah ya kara maka yawan rai a taya mu addua Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare mu bakidaya. Zan yi mata transfer zuwa babban reshen jamiar tasu da ke Ankara (capital of Turkey) ta karasa shekara biyunta. Ni ma zan yi wasuprojects (applied research) da jamiar na tsawon shekara daya.
In mun gama sai mu dawo Askira da zama gabadaya, bazan kumazama a garin da ba Askira ba, ina so in bude jamia tawa ta kaina (private university) tunda ni da ita duka fanni daya muke karanta sai mu hadu mu tafiyar da jamiar. Kafin in samu lasisin budewar (licence) shi ne abu mai wahala,domin a nan Askira nake so in bude jamiar ba a maraya ba.
Askirama mutum ne mai ilmi kuma wayayye, sosai ya fahimce shi, yana alfahari da haihuwarsa a kullum. Da daya ne tamkar da goma wanda yake barranta kansa da sarauta when it comes to neman ilmi, duk ya fi yan uwansa maza talent da jajircewa a kan harkar ilmi. Ya yi addua ya sa musu albarka, ya ce, gobe insha Allah za su je Abuja su mika neman visa da neman tranfer din shi da Saade, in sun gama komai zuwa sati daya za su tashi zuwa Turkiya daga Abuja ba za su dawo Askira ba sai bayan shekara daya.
Askirama ya ce bai yarda ba, idan watan haihuwa ya kama wa zai kula da ita? Yareema ya yi alkawarin zai kula da Saadatu kamar yadda zai kula da kansa. In watan haihuwar ya kama zai daukar mata Fanna, in kuma ta kammala karatun kafin nan tunda semester biyu ne kawai zai dawo da ita ta haihu a gabansu.
All he need is to be isolated shi da Saadatunsa. Shi kadai ya san irin ragaitar da ya shiga a wadannan kwanakin da suka yi nesa da juna. Ba ya son hayaniyar gidan Sarauta ko kadan. Da kyar Maimartaba ya amince da wannan tsarin na Yareema, amma yana adduar ta gama karatun kafin watan haihuwar ta ya tsaya ta zo ta haihu a gaban su. Yana da jikoki kusan guda 20 amma na Yarima isspecial domin babu kamar sa cikin duka jikokin da zai haifa ko ya haifa a baya. Yana masa adduarsamun nasara akan duk abinda ya sa gaba kuma ya gama rubuce-rubucen da zai je ya yi na tsawon shekara guda a ANKARA UNIVERSITY wanda zai bashi damar hawa Professorial Chair.
*****
Kin faya nawa, kin faya yanga Saade, don kin ga Askirama na biye miki, shin sau nawa zan aiko Fanna ta gaya miki Yareema na cikin mota tun dazu yana jiran ki zaku wuce ne? Duk wani shiri da za ki yi meyasa tun jiya baki yi shi ba?
Saade ta cuno baki hadi da marairaice murya Fulani gashi na fa nake gyarawa kawai, ya ce baya son ganin sa a cukurkude, nikuma bana so kowa ya taba min kai, shine nake tajewa da kaina.
Fulani ta karbi katon matajin dake hannun ta tace bari ni in taje miki, in ba haka ba zaki yi awa guda kina abu daya. Ta taje mata, ta tufke mata shi da murtukekiyar kalbaa tsakiyar ka. Ta kawo katon hair-bound kalar kayan jikin ta wato sky-blue ta zagaye mata shi. Fuskar Saade ta fito tsam, tayi cute da ita. Fulani ta taimaka mata ta nannada laffayar. Sannan suka fito.
Ko kusa bata gaya mata kasar zasu bari ba don ta san halin shagwabar Saade da rigimar ta, cewa zata yi bazata iya shekara babu Fulani ba.
Sun bata lokaci suna sallama, kamar kada su rabu,finally suka rabun. Saade na kwallah Zarah na kukan sai ta bi ta, da kyar Fulani ta rarrasheta da cewa asibiti zata je ta dawo, kafin Fanna ta raka ta wajen Ya Gumsu.
An jinginar ta jikin pillow bakin da ya karkace ya sha gashi ya koma daidai. Amma har yanzu bata motsa daya hannun yadda ya kamata amma kana iya gane abinda take cewa. Sauki dai yana ta samuwa cikin yardar Ubangiji da kulawar yayan ta.
Idan Allah ya baka yaya masu jin kan ka ya baka komai na duniya. Kishiyoyin ta ma baa bar su a baya ba wajen nuna kulawar su akan iftilain da ya same ta.
Ya Gumsu na ganin shigowar su ita da Fanna ta mika mata hannun ta mai lafiya, da sauri Saade ta karasa ta zube gaban Ya Gumsu. Hannu ya Gumsu ta dora a kanta tana shi mata albarka tare da cewa cikin harshen barbarci.
Wa gafurne kla awodune nyiro dikkuna samma so ro, Nadimtikna.(Ki yafe min na yi nadama a akan duka abinda na aikata, na yi nadama).
Saade tace baki yimin komai ba sai alkhairi Ya Gumsu, Allah ya baki lafiya.
Ta mika hannun ta mai lafiya kasan filon ta ta dauko warwaron zinare guda uku ta zura a hannun Saadatu. Saade ta rike hannun Ya Gumsu tana godiya.
Daga nan Fanna ta rakata unguwar Yaa Kirjiloma da unguwar Yaa Hibbani duk tayi musu sallama, kowacce da dan abin arzikin ta na sallama don tun faduwar Ya Gumsu jikin kowacce yayi lakwas, musamman Hibbani ta rage daukan zancen kowa ta kaiwa Askirama.
Chapter 16 · 0% Book details