← Book details Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 19

Sashe 7

Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Za ta dauke dukkan kwadayinka daga kan sauran mata, in dai Bilkisu ce ta haife ta.
Allah ya saka da alkhairi Alanguburo. Allah ya kara yawan rai, Allah ya ba ni ikon rike amanar da ka damka min da gaskiya da amana, har zuwa ranar da muka daina numfashi.
Kalaman da Yareema ke yi a fili kenan, yana kankame da matar sa Saade, ruwa na sauka a jikkunansu daga saman shower. Ba ta san adduar me yake yi ba har da sunan ASKIRAMA a ciki, daga baya ta fahimci gode masa yake da ya mallaka masa ita ta zama cikon farin cikin sa.
Ko ita a yau tana gode masa da ya mallaka mata gwarzon dansa mafi soyuwa a gare shi, wato Dr. SAGEER YUSUF ASKIRA,Basaraken Askira daya cikin dubu, sadauki kuma jarumi a fanninnunawa matar sa kauna da soyayya.
A baya gani ta ke Mai Askira ya katse mata rayuwa, yayi mata aure ba a lokacin da ta shirya ba. Yanzu kuwa ta gane Askirama ya cika rayuwar ta ne, ya ingantata.Ya suturtata cikin alfarmar aure. Aure suttura ne, cikar mutunci ne, garkuwa ne kuma rufin asiri ga diya mace, sannan gata ne da ba kowacce mace Allah yake yi wa Rahmar sa ba. Don haka godiyar ta ga Allah madaukakin sarki da kuma godiyar ta ga Mai Askirainfinite ce.
Kaunar ta mijinta ta gama ratsa koina na sassan jiki da zuciyarta. Ta fara tantamar ya ya rayuwa za ta ci gaba da kasancewa ranar da babu wannanmuhimmiyar soyayyar ta Yareema Sageer a cikinta???

*****
DR. ZIYAD SAHEEB
Ya kasa zaune ya kasa tsaye a dakin barcinsa, ya rasa inda zai sa kansa. Shaidaniyar zuciyarsa na ci gaba da kawata masa surar sullubebiyar matar abokinsa, yarinya danya sharaf! Irin Africans din da kalar fatar jikin su ke da wuyar samu a cikin matan Nigeria. Ka kasa gane half-caste ne ko kuwa shuwa-arab ne?
Dr. Ziyad ya kudire a ransa, ko ta tsiya ko ta arziki sai ya samu rabonsa a tare da matar Dr. Sageer, da ma ai sun saba sharing yammata, ya san Sageer bai taba neman matar aure ba, amma shi kam zai gwada saarsa a kan tasa, zina ai duk sunanta zina, kuma su ma wadanda yake neman a baya ai wani za su aura watarana.
Don haka don an yi masa abin da shi ma yake yi ba laifi ba ne.Dole ya juyawa harkar su baya yana da wannan precious gem din a cikin dakin sa.
Ya san ba zai sha wahalar samun kan yarinyar ba, yadda yake farin balaraben Turkish. Ya fi Sageer kyau nesa ba kusa ba, ya kuma san yadda matan Nigeria ke son fararen fata.
Karfe takwas na dare ya kira Sageer a waya. Dr. Sageer na makale da Saade a lokacin suna karatun Organic Chemistry ana yi ana soyayya tamkar sun cinye juna wayar Dr. Ziyad ta shigo masa.
Kamar ba zai dauka ba, sai kuma ya dauka.
Akwai abinci ne a gidanka in shigo in ci? Cook dina ya yi tafiya.
Sageer ya ce, Za mu bai wa Uche ya kawo maka yanzu, ka daina zuwar min gida, ba gidan Sultana ba ne yanzu, gidan Saadatu ne.
Saadatu!
Dr. Ziyad ya fada a hankali, wane irin suna ne mai tafiyar da ruhi haka? Duk wayonka sai na dandana abin da ka ke dandanawa.
O.K no problem, a kawo.
Da haka suka ajiye wayar.
Yareema ya yi tsaki, sannan ya dubi Saade da ke kalmashe cikin jikinsa. Da ya sani bai daga wayar bama balle ya bata masa mood din sa.
Kin yi ragowar abinci ne?
Ta ce, Eh. Ba ta son abin da zai tada ita daga jikin Yarima sam a daidai wannan lokacin, tana cikin amarcinta, suna yi suna karatun su. Karatun ma ya fi shiga a haka (inji Saade). Ta ji wayarsu da abokinsa, kuma ta tabbatar dole sai ta tashin.
Daure ki hada masa abinci a basket ki ajiye a kitchen, zan kira Uche ya kai wa Dr. Ziyad.
Tana cuno baki ta mike tana fadin,
Ba shi da mata shi?
Ya yi dariya, ya ce, Yana da ita.
Me ya sa ba ta ba shi abincin ba?
Ba ta nan ne, tana Istanbul har yayan sa, ki taimaka.
Ta sake turo baki gaba, sannan ta mike zuwa kitchen din, wandon three quarter ne a jikin ta da yar farar shimi (armless) ta je ta yi yadda Yareema ya bata umarni ta dawo. Shi kuma ya kira Uche a waya ya gaya masa abin da zai yi.

Da safe Dr. Ziyad ya sake kiransa, Karfe nawa za ka shiga ofis yau kuma karfe nawa za ka dawo?
Wannan wata tambaya ce da Ziyad bai taba yi masa ba. Nan da nan ya sha jinin jikinsa.Hausawa suka ce wai Shege shi ya san makwantar shege.
“Why are you asking?
Zan zo mu yi lunch ne tare.
Yareema ya daure fuska sosai, ya ce, Look Dr. Ziyad, gidana gidan aure ne, ko da can ni nake zuwa gidanka ba kai ka ke zuwa gidana ba. Sabida ba matar aure a gidan ka. Ni ba zan hana a ba ka abincin gidana ba, amma na gaya maka gara ka dawo da Guneet Nigeria ya fiye maka wannan rayuwar.
Maganar gaskiya matar da nake so nake kishi nake aure yanzu, don haka ba zan kai abokai gidana ba. In waccan rayuwar ce ni na bari, na gaya maka na kara gaya maka na bari. Don haka muamalarmu yanzu za ta koma ne strictly official, (ta tsaya a ta ofis kadai).
Wani maketacin murmushi Dr. Ziyad ya yi, ko dama shi ya sake dulmiyar da Yareema a harkar neman mata bayan aurensa da Aisha-Sultana kuma ba karamin shaidani ba ne. Ya riga ya rantse sai ya kwanta da matar abokinsa ko da hakan zai kawo karshen abotarsu. Ya gani kuma ya yaba. Ko ana ha-maza-ha-mata kuma sai ya yagi rabon sa.

Tun daga ranar yake studying shige da ficen Dr. Sageer da Saadatu zuwa cikin makaranta da lokutan dawowarsu ta tagar dakin barcin sa. Tsayin sati biyu yana hankalce da duk wani motsinsu, ya fahimci duk ranar alhamis yana dawo da Saade da wuri wajen karfe biyu na rana, shi kuma ya koma ofis ba ya sake dawowa sai shidda na yamma.

Ranar wata alhamis wadda Saadatu ta kira fateful day, watanninsu ukku kenan da aure, a duka wadannan watannin ba su je Askira ba amma kusan kullum suna waya da kowa nasu.
Yareema ya dawo da ita gida, ya ci abinci sannan ya dau keys dinsa ya fice yana ce da ita zai rufe gidan ta waje, ko an buga kada ta bude, shi in ya dawo zai bude da kansa.
Uche zai kawo mata cefane ta kofar baya zai shigo, in ya gama shigar da su zai rufe ya koma baskwata.
Bayan fitarsa Saade ta shiga wanka, wankan ma a gurguje ta yi shi don hankalinta na kan karatun paper din da za ta zana gobe, wadda ta kasance last paper ta kammala aji biyu (level 2).

Ta fito wanka kenan daure da towel iya gwiwarta, ta shiga dakin barcinsu ta zauna a kan stool din mudubi ta janyo lotion dinta na Makari ta soma shafawa, kanta cikin shower cap. Tana yi tana bin wakar balarabiya Nancy Agram cikin wayarta da ke gefe, ta ji an murda kofar dakinta an shigo.
Tana juyawa da sauri don a zatonta Yarima ne ya yi mantuwa ya dawo, sai ta ga wani balaraben mutum. Ya ma fi larabawa kyau. Ba ta taba ganinsa ba, yana sanye da jallabiyya, kawai sai ta sa a ranta aljani ne.
Wata kara da Saade ta tsandara sai da Uche ya jiyo ta daga baskwata, ihu ta ke tana neman a kawo mata dauki da dukkan karfin muryarta. Dr. Ziyad ya karasa da sauri ya toshe mata baki, ya buga kanta da bango, sannan ya sa kafa ya tadiye ta ta fadi kasa.
Duk da ta ji azaba ba yar kadan ba har cikin kwakwalwarta hakan bai sa ta kasa hobbasar ceton kanta ba. Bedside lamp da ke kusa da hannunta ta dauka ta kantara masa a ka. Fitilar ta fashe a kan Dr. Ziyad jini ya wanke masa fuska, shi kuwa Uche tuni ya kira Ogansa a waya tun karar farko da ya ji Saade ta kwallara.
Chapter 7 · 0% Book details