← Book details Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 19

Sashe 17

Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Impatientlykuma admiringlyYareema Sageer ya dubi Saadeda hanzari, lokacin da aka bude mata motar da yake ciki mai duhun glassai ta yadda baka iya hango wanda ke ciki.
Zaquwar son ganin ta na tsayin wannan lokacin da ya dauka ba tare da ita ba yasa ya hadiye fushin sa na jiran data bar shi yana yi a mota.
Data shigo ma aka rufe kofar motar jikin kofa ta koma ta makure ta juya masa keya.
Da ta san yadda zuciyar sa ke racing a cikin kirjin sa sabida excitement din ganin ta finally by his side da bata juya masa keyarnan ba.
Yarima ya girgiza kai yace ki yi lokacin ki ne Maman Chiroma, ko ba haka Askirama yace sunan Baby ba?
Ba ta san ya san da wannan maganar ba don haka ba shiri ta sunne kanta cikin cinyoyintadireba na barin kofar masarautar sai taji sanyin hannun Yarima a gadon bayanta a janyo ta sosai barin jikin sa sannan hannun sa ya kurda kasan marar ta yana shafawa cikin a hankali, ya sunkuyo daidai saitin cikin nata yace.
Stay blessed Chiroma.
A ranta tace shin in kuma ya mace ta haifa fa? Yarima da Baban sa zasu yi farin ciki? Yadda Mai askira da Yarima suke ta ambaton haihuwar da namiji? Zata so ta yi wa Yarima wannan tambayar, amma jin nauyi bazai bar ta ba. Kamar ta yi azarbabi in tayi maganar nan tun yanzu amma curiousity na cewa ta daure ta tambayi Yarima tun yanzu.
A dan zamanta gidan sarautar ta fahimci burin kowacce mace a gidan shine ta haifi da namiji har murna suke da Fulani Bilkisu ta haifi Zarah. Kuma a karan kanta gani take Askirama bai damu da Zarah ba kamar sauran yayan sa. Bata ji yana fadin a kawo ta fada ba. A ganin taHaihuwar dai ta janyewa Fulani Bilkisu gorin rashin haihuwa ne kawai a gidan amma da ita da babu sammakal.
Direba ya ja mota suka dauki hanyar Abuja. Inda zasu yi visa su tashi zuwa Ankara. Basu tsaya ba sai lokacin sallahr Azahar a gidan mai. A motar ma Yarima bai bar ta sakat ba da nauikan soyayyar sa mai tsayawa a zuci wato (sumba). Ta amince shi din expert ne a wannan fannin, ta yarda yayi missing din ta fiye da yadda zai iya bayyanawa, ta ga hakan cikin emotions dinsa da rawar da jikin sa ke yi a kan ta, tun da shi mai karancin magana ne sai dai actions da shaukin dake cikin zuciyar sa su fadi halin da yake ciki.
Sai dare suka shiga Abuja, kuma ba gidan su suka nufa ba kai tsaye hotel din (Fraser Suites)Yarima ya baiwa direban umarnin shiga.
Tuni ya sa an kwashe komai na su daga gidan malamai na NTNU dama gidan mallakar jamiar ne. Suna shiga dakin da suka kama Yarima ya maida kofar ya yi azamar rungume Saadeverytightly,
this seems like eternity! Ya Allah! Na roke ka, kada ka hora laifuka na ta hanyar nesanta ni da abinda na fi son kasancewa da shi a rayuwata. I missed you Saadatu!.
Ta kara narkewa a jikin Yarima sai yanzu ta san itama tayi kewar wannan kulawar ta Yareema Sageer, zaman ta tare da jamaa ne yasa bata gane hakan ba, ajiyar zuciya take saukewa a jejjere, tace
Prince, ina cikin damuwa, an ce ina da ciki, kuma na ji kuna ta kiran sa Chiroma tun ban haifa an ga me na haifa ba..
Ina cikin damuwar idan mace kuma na haifa fa? Wata zaka auro ta haifa maka namiji? Ko kuwa ita din bazaka so ta ba tunda bazata yi sarauta ba?
Yadda ta karasa maganar cikin karaya sai da ta sanya Yarima Sageer dariya. Ya dago fuskarta bisa tafukan sa. Ya ce
Saadatu in kin so ki jero min dozen na yaya mata, ki gani in zan so su ko ba zan so su ba, ki gani in zan kara auren wata matar don ta haifo min namiji.
Namiji baya alkawari akan aure musamman Basarake wanda ya gaji aure-aure amma ni Sageer! A yau ina mai tabbatar miki da cewa idan harba kaddara ce ta bi raayin kan ta ta aura min wata ba, na gama aure a rayuwa ta.
Abin da baki sa ni ba niSageer shaanin sarauta ba ya gaba na, Maimartaba na so in haifi namiji ne don ya tabbatar ba zan yarda in karbi sarauta ba. Amma ba don in kin haifi mace ba zamu so ta ba, ko hakan ne zai sa a kara yi min aure.
Mun dade da gane illar hakan cikin gidan mu wato fifita haihuwar maza akan ta mata don haka in kina tunanin hakan, to ki dai na.
Ajiyar zuciya Saade ta yi, a kalla yanzu ta samu peace of mind don ta san Yarima ba ya fadin abinda ba haka yake a zuciyar shi ba. Daga nanwanka su kayi kasancewar sun yi duka sallolin su a hanya.
Suna idarwa ya yi musu odar abinci mai rai da motsi, amma kallo daya Saade ta yi wa abincin tace bazata ci ba, dan wake take so mai manja da yaji.
Dan wake Saadatu? Yarima ya fada cikin damuwa. To yanzu ina zamu nemo shi a daren nan? Ta yarfarda kai ta ce mu je mu zazzzaga na san bazaa rasa mai dan wake ba.
A take Yarima ya mike ya dau mukullin mota, Bukari ya kwanta yanzu (direban da ya kawo su) mu je mu nema.
Ko dama so take ta fita din ta shaki freshair, ta gan ta Yariman Askira na tuka ta a mota da kan sa, wannan priviliged yana sanyata nishadi, shiyasa ta kakalo dan wake, in tace haka kawai su fita cewa zai yi ya gaji kuma dare yayi, yanzu kuwa ko don dan sa ya samu abinda yake son ci ta san ba shi da zabi banda su fita din.
Shiga wannan titi fita wancan suna tafe suna hira har ya samo mata danwaken a wani karamin eatry.
Basu dawo ba sai 11 na dare, tun daga bakin kofa Saade ta soma tausayin kanta, domin Yarima bai yi duka wannan wahalar neman danwaken ba sai da ya fanshe ta. A hakan ma yana tausayin ta sabida cikin jikin ta amma ta biya duka basussukan sa da ta ci tun kafin barin ta Abuja zuwa yau da kyakkyawan reward.
Washegari suka nufi Turkish Embassy suka shigar da neman visa. A kwanaki bakwai da suka yi suna jiran fitowar visar su ta tafiya Ankara sai suka zama kamar renakun honeymoon cikin hotel din Fraser Suites. Abin ki da mace mai yaron ciki, komai na jikin ta ya canza, don haka mannewar da Yarima yake mata har tsoro yake bata tamkar bai taba aure ko kusantar mata a rayuwar sa ba.
Auren sunnah daban yake, kuma macen alfarma daban Allah ke halittawa mijin ta ita. Shikansa ji yake kuruciyar sa na karuwa, lafiya da kuzari na kara shigar shi. Auren kananan yara ga maiyawan shekaru yana da wannan advantage din.
Yayi amfani da zaman hotel din ya nema mata transfer ta yanar gizo daga NTNU zuwa ANKARA UNIVERSITY.
A ranar da visar su ta fito transferdin Saade ma ya samu. Washegari suka bi Turkish Airlines zuwa kasar Turkiya.
Duk wasu memories na zaman ta a kauyen Tsanyawa tare da Baban ta, zuwan ta Askira wajen mahaifiyar ta, zuwa Abuja zaman gidan Dr. Sageer da yayi sanadin auren ta da Yarima Sageer din,ta kasa manta ko daya. Ta yi musu kundi (littafi na musamman).
Wato shi bawa tun haihuwar sa an rubuta masa dukkan kaddarorin sa. A hankali zaici karo da kowanne.Ta debo duka memories dinta taho dasu Ankara cikin kundin adana tarihin ta.
Kuma bata san shirin Yarima ba sai bayan saukar su a babbanfilin jirgin saman birnin Istanbul wato HavalimanıİşletmesiA.Ş. Istanbul Airport.Cewa ita da gida sai ta gama karatun digirin ta, ko ta haihu ko kafin ta haihu. Zai aika a dauko mata Fanna.
A lokacin da Yarima ya gaya mata hakan a filin jirgin ne suna tafiya zuwa terminal, hannayen su sarke cikin na juna. To ko taji damuwa ba kamar yadda ya zata ba, sabida a halin yanzu shakuwar da suka kara yi a dan tsukin ta zarce ta baya, a dan takaitaccenzaman su na kwanaki bakwai a Hotel dinFraser Suites, a halin yanzu tafi son kasancewa da shi har fiye da kowa a rayuwar ta.
Daga Istanbul suka bi jirgin kasa (Turkish Railways) daga Halkali wanda zai kai su zuwa Ankara (capital of Turkey).
******
Chapter 17 · 0% Book details