← Book details Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 19

Sashe 14

Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kwanan Ya Gumsu da iyalanta uku a National Hospital, sauki na samuwa a hankali. Ya Maira ta kira Yareema gefe ta ce tunda jikin da sauki, kuma an ce gashi ya rage za a dinga yi mata, ko zai nema musu sallama su koma gida? Sai a yi hiring professional din da za ta dinga yi mata gashin a gida?
Sun yi yawa a asibiti, kuma ba wanda zai yarda a ce ya koma gida. Don wani hotel suka kama a nan kusa da asibitin mazansu da matansu.
Yareema ya amince da shawarar Yaa Maira, ya nema musu sallama a washegari. Daga asibitin koyarwa na Maiduguri aka dauko physiotherapist din da za ta dinga kula da Ya Gumsu a gida ana biyanta.
Yareema bai samu nutsuwa ba tun saukarsa Abuja, don haka bai kira Fulani Bilkisu ba. Amma ko me yake yi Saadatu na manne cikin ransa. Minti bayan minti, sakan bayan sakan son Saadatu karuwa yake a zuciyarsa. Tamkar nisa da suka yi da juna wani medium ne na linking zuciyoyinsu wuri guda.
Haka kuma yake ga Saade, wadda ke can tana fama da kanta, amma kullum hankalinta yana kan mijinta Yareema Sageer. Ko yana cin abinci? Ko yana cikin irin damuwar da ta ke ciki? Ko shi ma Ya Gumsu ta mare shi a kan ta? Tambayoyin da ta ke yawan yi wa kanta ke nan ba ta da mai amsa mata. Domin Fulani ta lafiyarta ta ke ba ta mata zancen Yarima sam-sam.
Sun dukufa ita da Fanna wajen kula da ita da dafa mata duk abin da suka san za ta iya ci ko da loma daya za ta yi masa.
Dr. Zainab ma na kokari a kanta matuka, ta taimaka aman ya tsaya, amma kullum cikin tashin zuciya ta ke, don haka Fanna ta samo mata goro tana taunawa.
Ta rame ta yi duhu, da ganinta za ka san a satin nan ta yi jinya ta sosai. Tana kwance a dakinta suna labari da Zarah Fulani ta shigo ta same su. Ta ce,
Saade su Yareema sun dawo fa, an sallamo Ya Gumsu, don haka ki daure, ki kwarara jikinki yanzun nan ki je ki duba ta, ko da kuwa ba za ta amsa ba.
Saadatu ta fiddo ido cikin razana, Fulani ta lumshe mata ido tare da girgiza mata kai, ta ce,
Do as I said, sai Fanna ta raka ki.
A sanyaye ta mike ta soma daura laffaya a jikinta.
Fanna ce ta yi mata jagora suka tafi unguwar Ya Gumsu. Wata kuyangarta ta shiga ta yi musu iso, sannan ta fito ta shiga da su har tankareren falon da Ya Gumsu ta ke kwance. Gabadaya yayanta maza da mata suna zaune a falon tun daga kan Yaa Maira har zuwa auta Ahmad.

Yareema Sageer na zaune a gefen Ya Maira daga kan tattausan kilishi, ya mike santala-santalan kafafunsa da waya a hannunsa yana latsawa. Sanye yake da alkyabba ruwan zuma wadda ta sha aiki da zare ruwan gwal. Duk hirarrakin da suke yi ba ya sanya musu baki domin gabadaya hankalinsa yana ga son ganin Saadatu, da sabon matsayin da zai kalle ta da shi na mother of his children.
Lokacin da wata baiwa ta shigo ta isar da sakon cewa ga matar Yarima nan za ta shigo duba Ya Gumsu ko kadan bai ji su ba. Text messages yake rubutawa yana aikawa wayar Saade mai dauke da alkawurruka na soyayya da kauna masu wuyar samuwa daga bakin mazan aure a wannan zamanin. Duk da ya san cewa ba ta tare da wayar tata ta baro ta Abuja.
Kamar cikin mafarki, kamar daga sama ya tsinkayi sassanyar muryar Saaden na sallama a falon. Ya riga kowa dagowa a rikice, a mamakance, sannan excitedly yake dubanta. Da shi ta fara hada ido, ta yi saurin sunkuyar da kanta. Idanuwan yayye da kannen Yareema suka yi mata caaa wanda hakan ya sa kafafunta hardewa kamar za ta fadi. Kafin Fanna ta riko ta Yareema ya riga ta. Babu wanda ya ga sanda ya mike cikin zafin nama ya taro Saade, ya ruko ta har gaban Ya Gumsu, ya zaunar da ita daidai kafafunta yana fadin,
Ya Gumsu ga Saadatu ta zo duba ki!.
Kunya a wurin Saade kamar ta ce kasar ta tsage ta shige. Amma da yake dukkaninsu wayayyu ne ko a jikinsu, murmushin kauna suke mata dukkansu.
Yaa Maira ta ce, Barta ta zo nan kusa da ni ta zauna Yarima, dawo nan gefe na Saadatu.
Cikin jin nauyi ta zame daga hannun Yarima ta tsugunna har kasa ta ce, Ya Gumsu sannu da jiki, Allah ya kara afuwa.
Ya Gumsu ta daga mata kai alamar ta amsa, sannan ta rike hannunta cikin nata. Tana ta motsin maganarta wanda da alama so ta ke ta bai wa Saade hakuri.
Saade ta girgiza mata kai tana hawaye, Allah ya ba ki lafiya Ya Gumsu, da yardar Allah za ki fadi duk abin da ki ke son fada. Mun yi laifi a yafe mana.
Sai kuka, Yaa Maira ta zo ta kamata ta tayar da ita daga gaban Ya Gumsu, ta ja ta suka zauna tare, ta ce, Ba ki mata laifin komai ba Saadatu kin ji, kuma ta yafe muku duniya da lahira, Allah ya yi muku albarka.
Chapter 14 · 0% Book details