Sashe 1
Masarautar Mu Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read
MASARAUTAR MU!
4.
SUMAYYAH ABDULKADIR
[email protected]
[email protected]
SADAUKARWA
Ga 'yar uwar da muka rasa a TAKORITES. Allah ya jikan ki da rahma HASNA'U yasa aljannah ce makomar ki. Ya bamu guzurin tadda ke. Takorites bazamu taba mantawa da ke ba. Da zaman amincin da muka yi tare. Muna son ki Hasna.
JINJINA
Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah.
GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga radio, youtube, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali.
MASARAUTAR MU 4
Saadatu na gyangyadi bisa dardumar da ta yi sallahr asubahi, kamshin turaren Yarima ya ziyarci hancinta wanda ya durkusa a gabanta kamar ita ce Yareemar shi subordinate. A hankali ta bude idanunta sai suka sauka cikin na Yareema. Wanda ke kallonta da dukkan kauna da soyayyar duniya cikin idanunsa. Sannan kwayar idanun sa sun nuna submissiveness wato karbar laifin da ya san ya yi. Ta maida idanunta ta lumshe don ba ta san me za ta ce masa ba, ya bata mata rai da yawa, har ba ta son ganinsa. Don jikin ta ya bata ko daga ina yake, to tare yake da Aisha-Sultana tunda ta ga fitar su tare.
Ranar ta ta farko a gidan sa, ranar alfaharin kowacce amarya, ita nata angon ya tafi da matarsa hotel ne ko wane waje bata sani ba ko sallama bai yi mata ba, idan ta ce ba ta ji ciwon hakan ba hakika ta yi karya. Ita bazata ce kishi take ba amma taji ciwon abun a can kasan zuciyarta yadda bazata iya kwatantawa ba.
Im sorry Princess!.
Dr. Sageer ya fada cikin lallashi. Da karyayyar murya mara amo. Ba shi da kalaman kare kansa, so he admit kawai cewa ya yi laifi. Ya sake cewa, Im so sorry Saadahtouh, yanzu taso mu je mu yi sallama da su Fulani mu raka su filin jirgi sai mu dawo a yi min bulala goma sha biyar.
Ai da jin haka ta yi maza ta mike ta nufi kofa batare da ta kalle shi ba, da ma da hijabinta jikinta. Yareema bai mike ba, ya ci gaba da durkuso a inda ta barshi. Sai ta ja ta tsaya daga bakin kofa tana kallonsa questionably. Ya lumshe mata shanyayyun idanunsa ya ce,
Saadatuh, not even a good morning kiss?
Saade ta juya masa baya cikin jin haushi, zuciyarta na tafasa, ita wane kiss ta iya? Meyasa bai samo can a wajen tubabbiyar baturiyar sa da ya dauka suka tafi hotel suka bar ta ba? Tana mai tambayar kanta wai dama ashe haka Uncle Yareema yake tana masa kallon salihi duk da abinda matar sa ke fade a kansa mafi muni?
Daga sanda ya taso ya tako zuwa gaban ta, zuwa sanda ta ji saukar hannunsa ya zagaye bayan ta gabadaya ya rungume ta tsam-tsam, ba ta tantance ba.
Im sorry Saadah, very sorry. Ban yi da niyya ba, uzuri ne mai karfi ya rike ni. Amma ko ina nake, cikin kowanne hali kina rai na Saadahtuh.
Saade bata san yaya aka yi ba ta sunne kai cikin kirjin Yareema, zuciyar ta tayi wani irin sanyi da yadda Yareema ke lallashin ta, daga can kasan makoshin ta ta ce,
Ni ai ban ce komai ba Yaya Yareema, ko ka ji na yi complaining? Na riga na san mijin wata aka aura min, don haka I should expect things like this. Don Allah mu bar zancen nan mu je wajen su Fulani. Sai hawaye.
Wadanda tuntuni suke son samun damar zubowa, bata basu dama ba, sai yanzu da weakeness din ta na kishi ya nuna a cikin sautin furucin ta.
Ya ce, Don zuwa za mu je, amma kafin nan he began to kiss her passionately, wani irin zazzafan kiss wanda ya sa Saadatu gigicewa da ficewa a hayyacin ta. Har yanzu ta kasa sabawa da sumbar Yareema Sageer mai tsirgawa har cikin ruhin ta, she always feels it strange a tare da ita. Sai da ya yi mai isarsa amma ko taya shi bata yi ba, sannan ya kama hannunta suka fito. Ya rasa kuma ta hanyar da zai bi ya goge laifin sa.
A hotel din hilton sun samu Fulani da Maimartaba sun shirya, direban Yareema kuma ya debo su Fanna, don haka ba su bata lokaci ba kuma bata samu damar yin wata magana da Fulani ba sabida Askirama yana wajen, da ta yi mata korafin abinda Yareema yayi mata jiya; ya tafi ya bar ta ita kadai ranar ta ta farko a gidan sa (the first challenge), don haka basu bata lokaci ba suka wuce filin jirgin saman Nnamadi Azikwe. Ta hadiye bacin ran ta ita kadai.
Da kyar Saadatu ta saki Fulani lokacin da jirginsu zai tashi, tana kuka Fanna na yi. Sai da suka ga tashin su Yareema ya kama hannunta suka koma gida, jikinsa a sanyaye don har zuwa lokacin Maimartaba ya ki sakar masa fuska. Kuma bai yarda sun yi musayar kowacce kalma ba har jirgin su ya tashi. Sannan Saade ma ta ki sakar masa fuska har yanzu fushi take.
Suna shigowa gida ya janyo daya daga cikin jakunkunanta da ta dawo da su ya soma fidda mata kaya da kansa. Sai da ya fidda kala bakwai ya ce ta dauki duk abin da ta san za ta bukata na kwanaki bakwai, yana rike da kafadun ta bayan sun shiga dakin ya ce,
Za a yi refurbishing gidan nan kafin ki fara zama a cikin sa. Zaa fidda komai dake ciki a kawo wanda Maimartaba ya yi miki ki tsara shi yadda ki ke so.
Ita dai ba ta ce komai ba, ta gane so yake ya wanke laifinsa. Ko ina zai kai su kuma? Oho! Bai jira amsarta ba ya tafi nasa dakin don ya hada nasa kayan.
Har ya janyo madaidaiciyar trolley ya fito zuwa dakinta Saadatu ba ta motsa daga inda ta ke ba. Da alama wanka ya kara yi ya canza kaya zuwa wani danyen yadin boyel fari kal mai shara-shara har tana iya hango singlet dinsa. Ya tsaida trolley din a kan tayoyinta ya karaso cikin dakin, cikin sanyin murya ya ce,
Saadatuh mu je ko?
Ta sunkuyar da kai hawaye na son zubowa, kewar Fulani, Fanna da Zarah ke damun ta. Yanzu kuma Dr. Sageer na cewa zai kwashe ta su yi wani wurin har tsayin kwana bakwai.
Ni ba inda za ni, jibi za mu koma makaranta.
Dr. Sageer ya harare ta, ya ce, Ko yanzu za ku koma ke ba za ki koma ba, gara tun wuri ki sani, da da yanzu ba daya ba ne, lokacin da babu nauyin kowa a kanki. So ki bi ni a hankali in na ga dama sai in soke karatun gabadaya.
Hawayen da ta ke ta tattali kada su zubo suka zubo din. Ta mike cikin fushi ta dauki handbag dinta. Ba abin da ta dauka bayan ita, shi ya ja mata tata jakar suka fito.
A cikin motar Yareema 4Maticsuke tafe, babu mai magana daga shi har Saade, tuki kawai yake cikin nutsuwa da kwarewa. Tun tana tsammanin cikin Abuja ne inda za su je din har ta ga ya kama hanyar barin gari. Mikakkiyar tafiya sosai suke yi akan titin Jos, uffan ba ta ce masa ba. In ma sayar da ita zai yi ya sayar, Fulani da Maimartaba su suka jawo mata.
Sai wajejen azahar suka shiga garin Jos, ya nemi wajen sallar matafiya a gefen hanya wanda mata za su iya amfani da shi ya yi parking. Kwarai ta ke son shiga toilet don haka har ta riga shi fitowa.
Sai da suka yi sallar azhar (kasaru) sannan suka sake daukar hanya.