← Book details Kida A Ruwa Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 27

Sashe 9

Kida A Ruwa Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       A hanya su Dadah suka haɗe da su Imran dake cikin wata zuƙeƙiyar mota baƙa wulik. Dan duk da tasu Dadan ma nada shegen ƙau wadda su Daddy Imran ke ciki ta fita.
        Leƙowa kawai Imran yayi ta window ya miƙoma Dadah tab. Daga haka kowa ya maida gilashinsa ya zuge suka tafi a jere. Gida ne kyakkyawan gaske, sannan katafare bana wasa ba, dan kai tsaye zamu kirashi da Mansion ne. Yanda suna isowa aka wangale musu gate zai baka tabbacin an san da zuwan su.
         Akwai securitys a gidan sai dai ba masu yawa ba. Dan da'alama gida ne na sirri. Security ɗaya dake tsaye a ƙatuwar ƙofar shiga cikin gidan ya matso gaban motocin, dan basu tsaya a ko ina ba sai gaban ƙofar.
    Ido suka haɗa da Dadah. Yay masa signal da nashi idon da ake gani kaɗai. Dan akwai facemask daya sanya. Dadah ya kawar da nashi idanun sannan ya fito dan security ɗin harya buɗe masa. Suma su Imran dun fitowar sukai. Sai dai yanzu ɗaya ya ƙaru a cikinsu. Su duka sun rufe fuskokinsu da mask suma. Dan shima Dadah ya saka, sanda yake fitowa kuma ya sake ɗora baƙin gilashi daya lulluɓe ainahin ƙwayoyin idanunsa. Dama ga kayan jikinsa komai baƙi, hatta hannayensa akwai safar hannu a jikinsu.
       Zaratan mazajen huɗu suka rufa masa baya. Dan ɗayan da ya sake ƙaruwa a cikinsu yasa su zama huɗu bayan Imran, Faro, T-Dalha. Sai dai kasancewar fuskokinsu a rufe suke bazamuce waye shi ba. Suna isowa ƙofar ta rabe biyu a hankali. Wani azababben luxury parlor ya bayyana. Kai da gani kasan kuɗi sun jigata. A bakin ƙofar computer ce zatai searching nasu kafin su wuce, ai ko Dadah ya danna agogonsa a kaikaice. Na'urar ta gama zuƙe-zuƙenta ta sanar da babu komai a tare da shi tana danna green danja. Hakama su Imran ɗaya bayan ɗaya sai da ƙofar tai musu. Suma kuma babu wani damuwa suka wuce.
        Wata kyakkyawar doguwar farar mace dake sanye cikin jar doguwar riga da akai ma wata shegiyar tsaga tun daga ƙasa har ƙarshen cinya ta taso tana wani kalar juya siririn jikinta mai kama dana tarwaɗa. Daga sama kuwa rabin ƙirjinta a bayyane yake. Cikin wani kallo dake bayyana ainahin fitinar dake ranta tabi Dadah da kallo. Shi kam bamace kallonta yake ba ko a'a. Dan idanunsa na cikin gilashi. Cikin yarfar da hannu da karya jiki tai musu baraba da zuwa da harshen turanci.
        Dadah ya ɗaga mata yatsu biyu kawai. Sai ta saki wani mugun murmushi. Sannan tai wani juyi da jikinta ta fara tafiya. Babu wanda yay magana suka take mata baya. Ƙayataccen staircase ɗin dake tsakkiyar falon ta fara takawa, daga gani kasan akwai zinari a kwalliyar dake wajen. Ta tsaya a step ɗin farko tana juyowa. Cikin wani irin kaɗa yatsunta a jikin gilashin staircase ɗin da salo irin na iskanci ta ce “Shi kaɗai zai haura”. A take Imran ya zaburo zai yi magana amma sai Dadah ya ɗaga masa hannu. Wani alama yay musu da yatsunsa batare da yace komai ba yay mata nunin suje.
        Tayi murmurshi mai haɗe da lumshe idanu. Sai kuma ta botsare ta fara wata banzar tafiya. Dadah ya kawar da kansa cike da takaici yana jan tsaki a zuciyarsa. Eh shi mai yawan buƙata ne. Amma a kan halattacen nama. Shifa ko mace zatai zir a gabansa in har ba halak ɗinsa ba koda yana cikin yanayi ne baya jin ta birge shi. Dan a rayuwarsa zina da shaye-shaye suna cikin abubuwan da yafi tsana a ruhinsa. Sai dai hakan baya hana shi yin addu'a ga masu yi da musu fatan dainawa idan suna da rabo. Tare da nema wa wanda basayi da shi kansa kariya wajen UBANGIJI na har abadan. Dan wasu mummunar ƙaddararsu ce ke musu jagora fara aikatawar. Shima mutum ne kuma kamar kowa bashi da tabbacin tsallakewa sai da yarda da kariyar ALLAH...........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
[22/05, 8:12 pm] Halima KW BZ: *_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 4_*
_Chapter 7_

__________________
__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

..........Ashe falon ƙasa wasan yara ne. Na upstairs ɗin ne ainihin luxury. Idan kaji ana faɗin gidan gilashi da gilashi to shine anan. Sai dai babu abinda ya ɗauki hankalin Dadah a ciki balle shagaltar da shi ga abinda ya kawo shi.
       Sai da suka iso tsakiyar falon bayan hegiyar nan ta sake ma Dadah wani salon iskanci ta hanyar kwarewar manyan karuwan duniya irinta tai tafi. A hankali kujerar dake juye ta shiga juyowa. Ta tsaya cak a facing da Dadah. Sai dai hayaƙin sigari ya mamaye fuskar wanda yake a zaunen. Sai da mintina biyu suka shuɗe hayaƙin ya kore sannan fuskar Oga Jush ta bayyana. Oga Jush dai na ƙungiyar duhu da kuka sani.
      Tsabar iskanci da tantiranci zir yake zaune sai ɗan kamfai baƙi. Abinka da jar fata ga tsufa sai yayi kamar irin jikin tsoffin aladun nan da suka gaji da duniya, duniyar ma ta gaji da su.
       Da yatsu biyu yayma Dadah alamar wai ya cire mask ɗinsa. Dadah ya ɗan kalla sashen matar nan. Ai ko sai tai wata zabura tana isa inda Oga Jush ɗin yake. Cike da iskanci ta wani duƙe a kansa tana masa wasu abubuwan banza a jiki. Cikin harshen turanci tai masa maganar da Dadah bai jiba. Oga Jush ya kama lips ɗinta ya ciza, tai ƴar ƙara. Sakin mata yayi yana dariyar ƙeta. Ita kuma ta zauna a cinyarsa, sai kuma taima Dadah alamar ya zauna.
      Zaman yayi, Oga Jush kuma bai sake maganar ya cire mask ko gilashi ba. Riga ya fara saɓulema yarinyar a hankali, sai kuma ya dakata cike da iskanci ya furta. “Kai mai sa'a ne. Dan bayan ita da guards ɗina guda goma babu wanda ya taɓa taka wannan gidan. Saboda ta yarda da kai nima na yarda da kai. Na kuma amince zamuyi harƙallar zinare tare da kai. Sai dai ina da sharaɗi....”
        A karo na farko Dadah ya ce, “Miye sharaɗin naka?”.
       “Zaka kasance da ita, nima zan kasance da kai”.
     (Anzo wajen)
Dadah ya faɗa a zuciya. A fili kam sai ya ce, “Why?”.
     “Sharaɗi na biyu, ba'a tambayata abinda na zartar”.
      Oga Jush ya faɗa cike da gadara. Sigina yarinyar tai masa. Dan haka ya amsa da.
       “Na amince”.

    Cikin matsanancin tsoro T-Dalha ya kalla su Imran. Dan su dukansu suna da connecting da Dadahn ta hanyar wani mitsilin bluetooth dake kunnuwan su.
        Da hannu Faro yay ma T-Dalha alamar cool down. Badan T-Dalha yaji nutsuwar ba ya jinjina kai kawai. Dan shi tunda suka shigo ma ya gama saduda. A zahiri dai gidan babu securitys, amma yasan dole akwai cemaras boyayyu bayan na zahiri da suke gani...

        {××}{××××}{××}
Chapter 9 · 0% Book details