← Book details Kida A Ruwa Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 27

Sashe 21

Kida A Ruwa Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
[01/06, 1:46 pm] Halima KW BZ: *_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 4_*
_Chapter 14_

__________________
__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Yanda ya fuske bazaka taɓa cewa ya aikata wani abu ba. Sai ma ɗan leƙata da yay a dake tare da faɗin, “Spoon ɗin ya ɓata ne?”.
     Ƙaramin murmushi Nimrah tayi, yana kawo fuskarsa ta sumbace shi. Lips ɗin nata ya ɗan shafa kawai yana sakin ƙaramin murmushi shima. Sai kuma ya gyara fuskarsa yana gyara zama saboda amsar data bashi da kowa ya jita.
       “Gashi na ganshi, ya shige ne da yawa”. Tai maganar da mintsinar masa ƙafa kaɗan. Yana jinta ya maze. Sai ta miƙe da spoon ɗin hannu, shima ya saki mata ɗayan hannunta daya riƙe. Itama dai ta fiske kamar komai bai faru ba. Ta ajiye cokalin gefe ta ɗauki wani ta saka masa sannan ta saka miya a ƙaramin bowl na plate ɗin. Ta saka masa ruwa dan shi baya sha drinks. Garama wanda aka tace daga fruits shima banda sugar balle wani flavor.
       Wajen ta bari zuwa inda su Ruky suka koma a falo. Tana zama Ruky ta mata raɗa a kunne. Mintsini ta bata suka sanya dariya. Sai kuma da sauri suka rufe bakuna. Duk kallonsu akai, banda Dadah da yay kamar ma bai jiba, amma har Daddy Imran sai da ya juyo. Dada Abincin sa kawai yake ci hankali kwance. Dan yana matuƙar son tuwon alkama.
         “Munafukai miya baku dariya?”.
   Cewar Asma'u dake kusa da su.
Biebah tace, “Ke kuma da son gulma”.
    “Small Mom ai gara muji. Kin san yaran nan sun iya sa ido”.
       Cikin haɗa baki sukace, “Aunty Ma'u indai kin tsargu dake muke”.
     Filo ta jawo zata wurwura musu suka miƙe da sauri. Tai kwafa tana ajiyewa. Suma sai suka canja waje...

       Bayan su Dadah sun kammala cin abinci basu zauna ba, acewar su zasu je gaisuwar juma'a. Addu'a Mammah da Gwaggo Khadijah tai musu. Sun zo zasu wuce Nimrah dake yima su Naseer wasa suka haɗa ido da Dadah. Yatsunta babba da manuniya na duka hannun ta haɗe tai shape ɗin love tamkar tanama su Khadijah wasa. Suna sake haɗa ido ta ɗaga masa gira ɗaya alamar da shi take.
         Dadah da ke kallonta ƙasa-ƙasa amma sai ka rantse hankalinsa nakan Afrah dake masa shagwaɓar zata bisu ne. Ƙaramin ɓoyayyan murmushi yayi. Sannan ya ɗauki Afrah yana gaya mata abinda babu mai ji. Sai gani kawai sukai yarinyar na dariya. Koda ya ajiyeta kuma alamar ta haƙura sai ta sheƙa inda su Nimrah suke ta haye saman jikinta.....

        %%%%%

    “Yau lafiya naga kana haɗa kaya?”.
“Akwai matsala ne, zanyi tafiya taa kwana biyu.”
      Mamaki ya sake kama Malam Almu. Cikin kasa haƙuri ya ce, “Kwana biyu? Amma kasan akwai matsala yin hakan? Musamman tunda ba'a sanar da masu gidan ba.”
        Wata uwar Harara Sanda ya watsa ma Malam Alamun. Sai dai kafin yace wani abu Malam Buba ya shigo ɗakin, dole yay shiru. Shima Malam Almu sai ya wayance da ɗakko wani zancen dan kar malam Buba ya tsargu. Biye masa Sanda yayi, suka cigaba da tattaunawa akan abinda bashi suke magana ba da farko. Dan haka Malam Buba bai fahimci komai ba....

      Lokacin da su Dadah ke fitowa ma sai da sukai horn malam Almu ya fito ya buɗe gate. Daddy Imran na ficewa ya ɗan kalla Dadah dake gefensa yana danna waya. “Ina muka nufa?”.
       Dadah ya ajiye wayar yana furzar da iska. Shima Imran ɗin ya ɗan kalla, sai kuma ya kauda idanun nasa. “Mu fara gaida Baffah da Hajjo. Sai dai kira min Yusuf”.
        “Okay”.
   Imran ya faɗa yana ɗaukar wayarsa. Yusuf ya kira, bugu ɗaya ya ɗaga. Cike da girmamawa yay sallama tare da gaisuwa. Maimakon yaji Imran ya amsa sai yaji Dadah. Cikin ƴar rikicewa ya sake faɗin, “I'm sorry Boss. Barka da dawowa”.
       Dadah bai kula ba. Sai ma tambaya daya jeho masa.
    “Kana ina?”.
“A yanzu haka ina barrack Sir?”.
“Ina yaron nan da nake yawan ganinku tare?”.
       “Maina! Yana nan, yanzu haka tare muke kiran Oga ya shigo na tashi”.
     “Ka yarda da shi?”.
  “Wlhy ɗari bisa ɗari Sir. Dan ban taɓa kamashi da wani abu mara ƙyau ba. Sannan Soja ne mai ƙwazo da kishin ƙasa”.
       “Good. Ka sashi ya shirya akwai aikin da zai min za'a tura maka komai yanzu”.
     “An gama boss”.
  Dadah bai sake cewa komai ba ya ma yanke wayar. Imran da ke kallonsa ya ce, “Kamashi zaka sa ayi?”.
       “Dole muyi hakan da gaggawa, idan ba haka ba zai gudu”.
     “Zaki nawa maganin ƴan iska”.
Ƙaramar harara Dadah yay masa yana ɗauke kai. Shima sai ya tada motar yana dariya. Shima waya ya ɗauka kawai ya tura ma Yusuf saƙo....

         |•|•|•|•|•|•|•|

    Cikin sanɗa Rayhana da tun ɗazun take auna yanda zata shiga sashen Dadah ta samu nasarar shiga yanzu. Ba ƙaramin ƙyau da tsari falon yay mata ba kuwa. Amma yanzu bata ƙyawun falo take ba. Ta samu damar aiwatar da abinda ya kawota ne barinta. Cikin waige-waigen rashin gaskiya duk da ta sakama ƙofar falon key ta ƙarasa inda bedroom ɗin ƙarshe yake. Sai dai koda ta murɗa handle ɗin sai taji ƙofar a rufe. Da sauri ta bar wajen ta dawo na farkon. Tana taɓa nan ta buɗe. Wani irin sauke numfashi tai da tura ƙofar.
     Har yanzu Nabeeha na kwance kuwa tana shaƙar barci. Ta ɗan bi bedroom ɗin da kallo. Ƙmnshin turaren mai shi daya zama iskar shaƙa a ɗakin na ratsata. Komai tsaff  kamar ba'ai amfani da shi ba. Gudun kar Nabeeha ta farka dan tasan bata da nauyin barci sosai ta duƙe, da tafiyar sanɗa sannan a duƙe ta ƙaraso gaban gadon. Barci sosai kuwa Nabeeha dake mamuƙe da filo keyi. Sai taji kamar ta cakama banza wuƙa, dan ta gama fahimtar abinda take zargi ne ya faru. Hawaye suka cika mata ido. Tadai daure bata bari sun zubo ba. Ƙaramin fright dake bedroom ɗin ta buɗe, ta ajiye goron ruwan data naƙalo guda biyu bayan ta kwashe na ciki da suka rage guda huɗu, cikin sake ballama Nabeehan harara ta rarrafa ta fice da su....

        Fitowarta a sashen gaba ɗaya tayi dai-dai da shigowar Nimrah da Ruky, sai Small Mom da Asma'u dake bayansu. Small Mom ce tazo taga ɗakunan su. Shine suka fara zuwa nan kafin su je nasu Ruky dan su Aunty Ummi sunce su haɗe a sashen su Shariffa zasuyi magana da su. Basa kuma son su Mammah su fahimta shiyyasa akai abin cike da tsari. Ita Ruky hankalinta nakan charting da Ammar, lallaɓata yake wai tazo zai bata saƙo a sashen su. Ita kuma tace taƙi wayon. Shine ya sake turo mata “Please Baby”.
       Tana bashi amsa ne suka shigo babban falon sashen su Nimrah dake kallonta baki sake. Zatai magana idonta ya sauka akan Rayhana dake sakkowa daga sashen Dadahn. Sai dai tana ganinsu ta wayance ta hau danna waya kamar a tsaye take wajen kawai.
     Nimrah sarkin tsarguwa. Tuni ta sakama Rayhana alamar tambaya. Sai dai batace komai ba suka wuce. Rayhana kuma tabar wajen tana saka waya a kunne cike da bariki tana magana cikin ɗaga murya ita a dole kar su Nimrah su zarge ta...
Chapter 21 · 0% Book details