← Book details Kida A Ruwa Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 27

Sashe 17

Kida A Ruwa Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

     “Amma ke dai baki da zuciya wlhy. Yanzu kina nufin komawa zakiyi?. Ke ko kishin kanki baƙyayi da Dad. Duba fa tunda kika baro gidan uwarsu ta kira taji nan kika zo babu wanda ya sake kiran mu har ita”.
           “Ni dai babu ruwan ka. In ma bani da zuciyar ai tawa ce ko. Kai ko bance zan koma ba ai kace na koma. Jiba fa inda muke a ɗakin hotel guda ɗaya jal mu huɗu. Ni kaɗai mace a cikinku. Duk da kuke ƴan uwana idan son zuciya ya raya muku cutar da ni fa, tunda Dad ma ba kullum muke ganinsa ba.”
       “Amma Hanoon baki da hankali. A cikinmu ubanwa ya taɓa yi miki wani abu mara ƙyau?”.
      “Idan bakuy min ba ai wataran zakuyi min. Ince kai randa nazo a bayi na sameka da yarinyar mai aikinmu ta da. Ka iya zama ka lallaɓeta ta kawo maka kanta shegiya ko sisi bata samu sai wahala. Ƙarshe ma itace ke baka kuɗin. Sannan gashi nan abinci ma sai mu yini bamu ci ba muna wahala. Ko ɗakin Hotel ɗin badan Dad ya jima da biyan maƙudan kuɗi ba a kansa mun isa mu zauna?. Ai har ku ɗin dole ku koma can. Dan haka ni dai ba zan zauna ba. Gara na koma.”
         “Humm munafuka, kedai kice zaki koma saboda wannan tsohon dattijon da girman jikinsa ke kwasar ki”.
         “In ma dan haka ɗin ne ina ruwanka. Kaji da taka damuwar”.
     “To wa zai baki kuɗin jirgi?”.
   “Ina ruwanka koma wazai bani tunda banzo nace kai ka bani ba”.
Hanoon ta faɗa tana jan akwatinta ta fice ta bar su Afeef da Dayyan da kallon juna baki sake..........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
[25/05, 8:05 pm] Halima KW BZ: *_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 4_*
_Chapter 13_

__________________
__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

...........Har masu tafiya massalaci suka gama shiryowa suka fito tare da yara da aka ɗakko school babu Dadah babu labarinsa. Nimrah dai nata dannewa, bata yarda kowa ya lura da halin da take ciki kan son ganin ta ina zai ɓullo ba. Sannan ta hana zuciyarsa yin dogon tunanin hasaso mata yana tare da matarsa ne. Da hakan yazo mata a rai sai tai a'uziyya ta ture gurɓataccen tunanin da faɗin (Inama ruwana idan haka ne?).
         Sai da taga har su Uncle Ma'aruff na shirin wucewa massalaci ta kasa daurewa ta ɗauki wayarta. Gajeren saƙo ta tura masa kamar haka.
       (Kowa ya tafi massalaci amma banda Dadah na. Idan Babyna ya rasa sallar juma'a naga Boni). Daga haka ta ajiye wayar suka wuce kitchen ita da su Ruky. Dan dole a haɗa abinci mai yawa kamar yanda sauka saba duk irin wannan ranar ta juma'a da dama su Aunty Mimi ke yini gidan..

    .....★★

           Saƙon Nimrah ya iso wayar Dadah ne a dai-dai lokacin da yake tsaye gaban mirror yana fesa ma jikinsa turare. Yayi matuƙar ƙyau cikin yadi mai laushi fari tas daya zauna masa a jiki ɗas. Ga hula ya mirza masha ALLAH.
        Ta notification yaga sunan Little Shadow kamar yanda yay saving. Ya ajiye turaren daya gama fesawa ya ɗauka wayar ya shiga saƙon. Murmushin da bai shirya ba ya suɓuce masa. Ya sake maimaita saƙon har sau uku sannan ya saka wayar aljihu yana juyawa ya kalla Nabeeha dake barcin wahala a gadonsa. Komai bai ce ba ya ɗauka takalma ya saka sannan ya fice.

        Tun kafin ya gama bayyana mayataccen ƙamshinsa ya gama gauraye sashen. Cikin rawar jiki Rayhana dake a babban falo zaune tana dakon jira numfashinta yay wata kalar fusga kafin ya dawo da ƙyar. Dan sai da ta haɗa da iskar baki wajen jawo shi.
        Da rawar lips data murya take masa sannu da zuwa. Hannu kawai ya ɗaga mata ya wuce batare da ko kallonta yayi ba. Ita ko kamar mayya haka take binsa da kallo idanunta na cika da ƙwalla. Wani abu mai ɗaci ya ƙara tokare mata ƙirji ganin har ya nufi ƙofar fita ya dawo ya nufi sashen Nimrah. Cikin sauri da son yay mata ko magana ne ta ce, “Dadah bata nan”.
     Cak ya ɗan tsaya. Sai kuma ya juyo zai wuce batare da yayi maganar da take so ɗin ba. Dan ya san Nimrah bazata wuce sashen Mammah ba. Lips ta cije da ƙarfi, zuciyarta tamkar zata kama da wuta. Komai a duniya bawan ALLAHn nan yayi birgeta yake tun a shekarun baya bama yanzu ba. Ita kaɗai tasan girman darajar abinda take ji game da shi a zuciyarta. Yayinda a yau wani kishi mai tsanani na duka matan nasa ke neman halaka ta. Musamman Nimrah da duk wanda ya kalleta ya kalla Dadahn yasan ba ƙaramar shoshalewa akayi a tafiyar nan ba. Ji take kamar bazata iya cigaba da zaman gidan nan ba. Amma dole ne ta daure kodan samun cikar burinta kamar yanda First Lady ta tsara mata da kuma yima First Lady ɗin aikinta....

       •==•===•==•

             Kasancewar guri yana gab da ƙurewa, ga Imran na jiransa su wuce massalacin bai shiga sashen Mammah ba. Drivern Daddy Imran ya fito da sauri ya buɗe masa murfin, sai da ya shiga kusa da aminin nasa dake ƙare masa kallo yana murmurshi tunda ya fito sannan. Securitys ɗin dake tare da Imran ɗin ne suka buɗe gate. Dan su Malam Almu sun wuce sallar juma'a tare da su Bilal. Harda Mole kuma da Sanda da basu san Dadah ya dawo ba.
          “Surukina ba gaisuwa? Anya bazan ƙwace yarinyata daga hannunka ba koda na sati ɗaya ne?”.
     Daddy Imran ya faɗa cike da tsokana. Batare da Dadah ya kallesa ba ya ce, “Idan ma kayi hakan kunya zata baka”.
        Cikin dariya Imran ya ce, “Kar dai ka cika baki ta baka mamaki. Dan ita ba irin matarka bace mai tafiya ta dawo da kanta.”
       Murmurshi kawai Dadah yayi batare da ya sake cewa komai ba. Shima Daddy Imran bai sake magana ba kasancewar sun kusa isa massalacin. Dan Central mosque suka zo...
Chapter 17 · 0% Book details