← Book details Kida A Ruwa Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 27

Sashe 3

Kida A Ruwa Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin barci zafin jikin Nimrah da wahalallen numfashinta dake fita da nauyi ya farkar da Dadah. Da ƙyar ta yarda ya cire ta a jikinsa ya tashi.
“Dadah sanyi ka rufeni. Wayyo Mammah na shiga uku”.
Bargon ya rufa mata, cike da lallashi yana shafa kanta. A gadon ya sauka gaba ɗaya, ya samo mata riga mai dan kauri ya sanya mata. Hawayen da suka gagara tsayawa ya share mata, muryarsa da sanyi sosai ya ce, “Bana son kukan nan Kiddo. Kiyi shiru kar ya sa miki ciwon kai. Yanzu zan miki allura zazzaɓin ya tafi. ALLAH yay miki albarka, yay miki tukuyci da mukulun aljanna maɗaukakiya”.
Taji daɗin kalamansa, dan haka ta shiga sassauta kukan ta. Sai jan ajiyar zuciya da saukar hawaye kawai. Sake kwantar da ita yayi ya miƙe. Bai wani jima ba ya dawo da kofin tea. Kamata yay ya zaunar, sai dai yanda ta kasa zama da ƙyau ya ɗan zuba mata ido. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Zauna da ƙyau mana”.
Kanta ta sunkuyar hawaye na sake zubowa. Murya a dasushe ta ce, “Dadah bazan iya ba. Ina jin ciwo sosai”.
Zuciyarsa ta harba. Sam baya fatan ace ya raunata ta. Baiyi magana ba ya kamata ya kwantar, jin ya cire bangon da take rufe a ciki ta runtse idonta da ƙarfi. Matsananciyar kunya ta lulluɓeta, mamakin yanda sam Dadah baya jin kunyar mata abu yanzu ya mamayeta. Sai taga kamar yana mantawa da itace fa Nimrah. Ajiyar zuciyar da taji ya sauke a hankali ya sata buɗe idonta kaɗan ta kallesa. Da ace zata iya sai ta tambaye sa miya faru? Amma Dadah ne hakan bazai yiwu ba.
Dadah daya samu nutsuwar ganin ba abinda ya faru bane a ransa yake jinjina ga Nimrah. Eh lallai yanzu ya ƙara fahimtar kalmar nan ta Hausawa dake faɗin ɗan hakkin daka raina... Sannan fankan-fankan bata kilishi. Zakanayar da ake kiran Nimrah ɗin da shi ta tabbata zakanayar ce, dan ya fahimci yarinyar nada juriya, sannan jikinta nada jarumta. Idan har zata iya ɗauka a farkon yaƙi bada raunata ba inaga ta zama cikakkiyar mayaƙiya nan gaba?.
Da wani slow down look ya sake binta. Baki ta tura tana sinne kai. Ya ɗan murmusa kaɗan. Sarai Nimrah taga murmushin nasa, dan haka itama ta murmusa a zuciyarta. Da kansa ya bata shayin tasha, sai kuma ya sake miƙewa, box ya ɗakko ya dawo inda take, ya zauna a kusa da ita bakin gadon inda ya tashi. Allura ya fiddo ya haɗa, duk da halin da Nimrah ke ciki sai da tai mamakin dama Dadah ya iya allura?. Ɗagotan da yay ya katse mata tunani, sai da ya sakata a jikinsa sannan yay mata. Ta sauke ajiyar zuciya dan babu wani zafi. Sai dai ganin yana zuba wasu alluran a drip ta ɓata fuska.
“Dadah na waye?”.
“Naki”.
“Uhm-uhm ni bana so”.
“Ai shi magani basai ana so ba Little One. Jikinki yayi zafi da yawa gashi kince yana ciwo. Kina buƙatarsa dan ki samu ƙarfi. Ko baƙya so anjima mu sake nemo aljanna ɗin?”.
Batare data fahimta ba ta ce, “Ina so”.
Murmushi yayi mai yalwa. Ya kamata ya miƙar tsaye. “Muje bayi kiyi alwala. Lokacin zuhur yayi”.
Ganin yanda tafiyar tata sai a hankali ya ɗauketa kawai. Da ruwan ɗumi tai alwala kamar yanda ya sakata tai tsarki, shima yayi sannan ya sake ɗakkota suka dawo. Jam'i yay musu Nimrah nata mutsu-mutsu a duk sanda zasu zauna. Dan haka suna idarwa bai tsaya doguwar addu'a ba ya maidata saman gadon ya saka mata drip ɗin. Bayi ya koma ya jiƙo ƙaramin towel ya dawo ya fara goge mata jiki. Tanata faman sakin ajiyar zuciya saboda sanyin ruwan. Sai da yaji zafin jikin nata ya ragu sannan ya lulluɓeta dan har barci ma ya ɗauketa.
Sai a lokacin ya ɗan ji nutsuwa ta saukar masa. Kimtsawa yay shima ya rage mata hasken ɗakin ta hanyar sakin labulaye sannan ya fice. Ko'ina yayi fayau da hasken rana. Mamakon ruwan da suke ciki sai walƙiya yake da ɗaukar idanu. Ga wata iska mai saka zukata nutsuwa na kaɗawa. Yanzu kam sun ƙara yin nisa da gari sosai, dan acan nesa ake hango dogayen gine-ginen. A cikin ruwan kam akwai jirage da yawa dake kai kawo. Sai irin mashinan nan na wasan ruwa suma da mutane akai.
Idanunsa ya lumshe tare da sake buɗewa. Ya sake gyara hannunsa ɗaya dake aljihu, ɗayan riƙe da kofin coffee daya fito da shi. A hakanli yake kaisa bakinsa zuciyarsa na fara dawo da tattaunawar su ta jiya da Kawu Tanimu. Sunan BABA abu mafi girma dake tsaye ƙyam a ƙirjinsa. Da wannan sunan yay barci, da shi ya tashi, yana kuma buƙatar yin nazari mai faɗin gaske a kansa.........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

[21/05, 5:45 am] Halima KW BZ: *_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 4_*
_Chapter 3_

__________________
__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________
Chapter 3 · 0% Book details