← Book details Kauyen Yar Kadde Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 26

Sashe 7

Kauyen Yar Kadde Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zama tayi kusa da ita tare da cewa "besty zani islamiya, zanje na dawo nasha labari domin da alama dai wanan murmushi da ake saki zanji labari mai dad'i".
Ta'ba baki tayi tare da mi'kewa " sai ina kuma besty? inace zaki jirani na dawo ne?" "Uhu'um" tace da ita tare da riga ta barin d'akin.
Sometimes tana mamakin 'kawar nata, "wata irice ita gadai tanan".
Fito wa tayi lokacin har takai 'kofar gida, 'kofar gidan su ta tsaya tana kallon gidan Auwal.
Fitowan Aisha yasa ta kauda fuskan ta daga wurin ta maida kan Aishan.
" Besty sai na dawo ko?" d'aga mata kai kawai tayi, ita kuma ta wuce makaranta ta.

"Baki gajiya kedai, kullum makaranta, ina zan iya wannan wahala, ga wani abu biyabiya dashi".
Tace tana ta'be baki tare da barin kallon 'kawar tata.

Tsawon lokaci tana tsaye a wurin kafin tayi cikin gida.

Koma wanta da kad'an maman ta ta dawo, saukan ta a mashin Auwal ya fito daga gidan sa, da murmushi ya'ke yace "sannu da zuwa, yauwa yaron kirki" tace dashi "Joy ta dawo kuwa?".
Wani 'kululun ba'kin ciki ya tokare masa, amma ya daure yace " uhmm".

Shiga gida tayi shi kuma ya wuce inda zashi.

****

Watan Auwal shida a 'KAUYEN 'YAR KADDE, abubuwa da dama sun faru, daga ciki akwai yawan shige masa da Joy keyi, kamar idan ta gansa ta gaishe sa da dai sauran su, ta rasa maike damun ta dangane dashi, kuma sau goma zata masa magana bazai tanka taba, duk sanda ya ganta idan a hanya ne canza hanya yake, idan kuma ta tasame sane sai ya d'auke kai yayi kamar bai ganta ba.

******Auwal kwance yana waya da mami sai faman narke mata yake tana biye masa "mami don Allah ki ro'ki Dady ya yarda na dawo, wallahi mamina nayi missing d'in ki, ga 'kauyen ko dad'i babu, har yanzu ban saba dashi ba".

" Ga sister zata dawo nan da sati mai zuwa,".
"Ni Auwal bansan yadda zanyi ba, nayi nayi koni nazo na ganka ya'ki, bansan yadda zanyi ba nima inason naga boy d'ina" tace tana murmushi.

Turo baki yayi tare da cewa "mami niba boy bane gaskiya na girma" "da gaske my son? uhum".
"Amma mami na haka zanta zama sai na shekara sanan zan ganku?, eh son tunda haka Dadyn ku yake so".
" Haba sai kace mara gata, mara galihu? hab fisabilillahi kamata haba mami na, do something ".

" Hmmm, bari zan jaraba Allah sa adace, amin mami na, ko kuma kawai kisa 'yan gaban goshin sa agaba nasan suna cewa zaiyi na'am".
"To bari suzo muga" "yauwa mamina shiyasa nake tsananin 'kaunar ki, love you mum" yace tare da sakin masa kiss ta wayar.

Dariya tayi tare da kashe wayar, shiko wani farin cikin da yadad'e baiyyi ba yaji ya mamayeshi smiling kawai yake.
Tashi yayi daga kwancen tare da shiga toilet yayi wanka, T-shirt mai ratsin baki da fari yasaka da ba'kin wando, kayan sun matu'kar kar'ban sa.

Kallon kansa yayi a mirror shi kansa yasan ya had'u, smiling yayi tare da cewa "yaron mami ka had'u" tare da cewa yima kansa kiss ta mirror d'in.

Bayan ya kintsa ya fito domin le'ka asibiti lokacin la'asar ne sakaliya.
Yana rufe gida ya juyo yaga mutum a bayan sa, kauce wa yake ninyan yi ta tare, tace tana ya mitsa fuska "doctor cikina na ciwo ko zaka taimakamin please?".
Kansa na kallon gefe yace " nan ba asibiti bane, baya ga haka kije kinemi wani not me".
Kallon sa take ta 'kasan ido, "zaki iya bani hanya na wuce" yace fuskan sa kamar wanda bai ta'ba dariya ba.

"Kayi Kyau" tace a hankali tare da matsa masa a kan hanya.
Ya fara tafiya yaji kamar ana binsa a baya, bai waigo ba sai da yaje 'kofar asibiti sanan.
Ganin wace ke bayan sa ya had'e rai tare da shigewa.
Cigaba da bin nasa tayi har 'kofar office d'in sa, bud'e wa yayi tare da shiga, zai rufe ta turo jikin ta.

"Kibar wurin nan", " doctor nazo fa domin lafia tane, da gaske banda lafia ka yarda dani" ganin kallon da yake mata yasa tace haka.
Bud'e mata yayi ta shiga, zai duba ta kodon maman ta.
Zama yayi a kujeran sa, ita kuma tana nan tsaye, nuni yayi mata da hannu alaman ta zauna.
Zaman tayi sa'an nan yayi shiru yana jira daga gare ta.

Tasani sarai tagane nufin sa amma ta share sai ma 'kare masa kallo da take.

Gajiya yayi ya mi'ke domin zuwa duba marasa lafia, itako tana nan zaune ko motsawa batayi ba.
Fita yayi ya barta ba tare da yace da ita komai ba.

Kallon office d'in take lungu da sa'ko, ba wani babba bane tunda na 'kauye ne, amma da yake na d'an gata ne ba laifi yayi Kyau.

Tashi tayi taje kan 'karamin bed d'in marasa lafia da yake office d'in ta kwanta tana mai lumshe ido lokacin ne taji ciwon ya taso mata, don haka sai ta fara mur'kususu.
Dai-dai nan Auwal ya bud'e 'kofar, ganin bata a kujeran da take yasa shi ajiyan zuciya tare da cewa "mayya kawai ta tafi......." Bai 'karisa zancen saba yaji nishi .

Waigawa inda yake jiyowa yayi kwance ya ganta a gadon.

Tana mur'kususu, d'auke kansa yayi kamar bai ganta ba, abinda yazoyi yayi ko ya gama don haka sai ya tattara abinda yazo dashi domin koma wa gida.

Aje key d'in office d'in ya aje tare da ninyan fita yana cewa kamar mai ciwon baki "idan kin tashi sai ki rufe musu office d'in su".
Kuka mai had'e da ehu ta saki tare da cewa " wayyo doctor zan mutu kataimakeni please, mama tace nazo ka dubani".
Dawo wa yayi tare da cewa idon sa na kallon gefe "meke damun ki?" "tunjiya da dare nan kemin ciwo, ina kenan?" yace ba tare da yajuyo ya kalle ta ba.
"Nan" tace, shi kuma yace cikin gajiya da 'kufula "shi wurin baida suna ne?" shiru tayi tana mai cigaba da kukan ta.

Haushi yaji zai fita, itako ta dage iya 'karfin ta tasaki ehu mai 'karfi.
Toshe kunnin sa yayi tare da kallon da azafafe ya nufo ta.

Kamar zai bugeta yace "wallahi kika sake min 'kara a kunni sai naci....." sai kuma yayi shiru.

"Ina kemiki ciwo? yace yana hararan ta.
Maimakon ta bashi ansa sai ta cigaba da kukan ta.

" Tashi kibarmin office yanzun nan kafin ranki ya 'baci" yace yana matsowa kusa da ita.

Bai aune ba kawai yaji ta kama masa hannun, da mamaki da ba'kin ciki yake kallon ta.
Bai gama mamaki na yaji hannun sa a lallausan jikin ta.
A han maran ta ta d'aura hannun nasa.

Cikin kuka tace "nan ne kemin ciwo" fisge hannun sa yayi cikin masifa yace yana tofar da yamu.

"Banza 'kazamiya, amgaya miki kowa 'kazami ne irin ki? ko ance miki ni Auwal irin karnikan kine 'kazamai Wanda basu san inda yake musu ciwo ba irin ki".

"Zan miki gargad'i da babban murya ni Auwal nafi 'karfin ki, nafi 'karfin 'kazan taccen jikin ki, kuma ki fita harka ta, idan ba haka ba ki kuka da kanki".
" Banza kawai, Auwal ba jaki bane, kisani koda ni mazinaci ne irinki to bancin sauran wasu, kina mace mai aji da kima da daraja amma kinzubar dasu, koba abun abun mamaki bane arna zasuyi fiye da hakan".

Ya sake tofar da yamu idanun sa ya rufe yayi ta surfa mata ba'ka'ken maganganu.

Koda ya gama bai damu da kukan da take da juye-juyen da take ba.

Yabar office d'in tare da sanar da mai gadin wurin idan ta tafi ya rufe masa office d'in ya'kara gaba.

Tafiya yake yana ganin dishi-dishi domin abinda yafaru yana ganin sa a idanuwan sa kamar yanzu ake.

Kuma ya tabbatar da zarginsa 'yar iskance ita......

Tofah fan's kunji fan

Kubiyoni domin jin yadda zata kaya, amma hakan bazai samu ba sai naga comments.

Comment & share pls

'Yar Aliyu ce✍🏻
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*LITTAFAN MARUBUCIYAN:-*
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*

*Dedicated to my family*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

🅿1⃣7⃣to1⃣8⃣

"Dole na cire ki a raina, kota halin 'ka'ka kuwa, zuciya baki min adalci ba, taya zaki sa naso wacce bata dace dani ba? yes bata dace dani ba, bata cancan ceni ba. Ni mai tsaftane ita 'ka zama, ya Allah fitar da ita a zuciya ta". yace yana mai rintse ido, lokacin yana kwancen a bed d'in sa, babu abinda yake tunani sai ita, tunani halin da ya baro ta kawai yake.

***Ta d'au tsawon lokaci a wanann yana yin, tana cikin damuwa mai tsananin, abu uku ke damun ta. Na farko 'kama da Auwal ya kira ta hakan yayi mata zafi sosai, ta gane cewa yana zargin ta da aika ta fasi'kanci, abinda bai sani ba, zina abune da take matu'kar 'kama, hakan da ya matu'kar tsaya mata a rai.

Na biyu ciwon maran dake damun ta, ba'kin ciki yasa ya rage mata kaso hamsin na ciwon.

Na uku tsananin 'kaunar sa da bata san tanayi ba sai yau, gashi Auwal yayi mata nisa, kalman sa kawai yasa ta gane tsananin kiyayyar da yake mata.

" Ina son ka, wallahi ina son ka, ina tsananin 'kaunar ka, 'kaunar ka shine ajalina zan rayu da son ka duk da nasan baza ka ta'ba sona ba".

Tace tana mai fashe wa da kuka mai tsanani, a daddafe ta bar office d'in nasa, idan nun ta nata zubar 'kwallah.

A haka taje gida bata damu da kallon da mutane kema taba sam.

Tana shiga ta tadda uwar ta a tsakar gida, ganin yana yin da 'yar tata ta shigo yasa ta isa gare ta da sauri ta taro ta.

Tare da tambaya ta abinda ke damun ta, shiru tayi mata tana mai cije le'be.
Chapter 7 · 0% Book details