← Book details Kauyen Yar Kadde Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 26

Sashe 26

Kauyen Yar Kadde Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Idanun ta jazur ta kallesa tare da bud'e baki daninyan magana, amma ya hanta ta hanyan sanya hannun a le'ben sa tare da girgiza mata kai.

'Ko'karin mikewa take Aisha ta taimaka mata ta mi'ke.

Ganin ta mi'ke sai ya nufi hanyan fita d'akin tare da cewa" maza ku fito muje sauri don inason daga can zan wuce gidan Ammi na tana nema na".

'Dan kwalin dogon rigan jikin ta kawai ta yafa mata suka fito.

Wurin motan suka nufa Aisha ta bud'e mata 'kofan seat d'in baya tare da taimaka mata ta shiga tare da rufewa.

Aisha na shiga ya tada motan tare da danna horn mai gadi ya bud'e suka bar gidan.

Suna tafiya Aisha taga ya wuce asibitin da Zarah ke aiki, sai ta bud'e baki tana mai kallon sa tace" Hubby yaka wuce asibitin su? ina can zamu?"

"Zan kai ta ainihin wurin mai asibitin nema ya duba ta a d'ayan asibitin shi, don ina son a duba ta yadda ya kama ta, don naga jikin nata sosai ne, idan bashi ya duba taba hankali na ba zai ta'ba kwanciyan ba".

Murmushi tayi tare da cewa" lallai kanaji da 'kanwan nan taka".

"Ba dole ba, ita kenan min Ammi ta'ki min 'kani ko 'kanwa, daga ita sai Muhusin".

Murmushi kawai Aisha tayi, niko ina tafama a bayan mota .

Su kad'ai ked'an fira jefi-jefi tare da min sannu akai akai, cikin tsantsan kulawa.

Wani babban asibiti had'ad'd'e dashi, da gani na masu dashi ne, tun daga wajen asibiti zaka sheda hakan.

Tun da muka zo bakin get d'in shiga gabana ke fad'i ga zazza'bina da ya'kara gaba.

Domin tunani kawai nake ga uban ba'kin cikin da nakeji.

Wanda ji nake kamar na had'e rai na na mutu na huta.

Parking yayi Aisha ce ta fara fita sanan y Abdul.

Zuwa tayi ta taimaka mini na fito ya rufe motan muka nufi cikin asibitin.

Direct office d'in mai asibitin muka nufa.

Y Abdul na gaba muna bayan sa, gaba na na cigaba da fad'uwa.

Sanin ko waye ya Abdul a wurin mai asibitin yasa babu wanda yayi magana san da muka dumfari office d'in.

Knocking yayi har sau biyu ba'a asa ba, da akai na uku cikin masifa da fitina ya nufo 'kofan tare da cewa" Labiba wuce na sallame ki daga aiki, bana gargad'e kiba" tare da bud'e wa.

Ganin y Abdul ne sai yayi murmushin ya'ke tare sosa kai yace" welcome babban yaya".

Tare da basa hanya don shiga, da mamaki yaya Abdul ya bisa da kallo tare da shiga.

Aisha ko ganin wanda ke gaban ta ta saki baki, tare da mutstsike ido.

Tunanin tako mafarki take.

Ganin Zarah zata fad'i yasa tai maza ta ri'keta da 'karfi, wanda zuwa wannan lokacin bata wani sanin meke faruwa.

Bin bayan y Abdul tayi hannun ta ri'ke da Zarah.

Doctor Auwal zaune yana mai fuskan ta y Abdul yake cewa" yaya da kanka? ai da kakirani nazo, meke............" kasa 'karisawa yayi sakamakon wanda ya gani a gaban sa.

Y Abdul ne yace" bani neba ai, 'kanwata ne bata da lafia".

Kauda tunanin rashin yuwuwan tunanin sa, yasa ya kauda tunanin sa, yafi tunanin gizo ma suke masa.

Tashi yayi daga kan kujeran shi tare da cewa ba tare da ya sake kallon suba" kwantar da ita a kan gadon can".

Kwantar da ita Aisha tayi tanayi tana satan kallon sa, had'i da mamakin irin wannan kama.

Matsawa tayi ta basa wuri, matsowa yayi.

Kuramata ido yayi na tsawon wani lokaci, hannun sa na rawa ya fara duba ta.

A hankali yake komai har ya gama, rubutu yayi tare da cewa yana mai kallon y Abdul ta gefen ido, don baiso su had'a ido ya gane halin da yake ciki.

Yace" zamu bata gado jikin ta yayi tsananin sosai".

"Meke damun ta?" cewan y Abdul.

"Damuwa ne mai tsananin yake damun ta, 'karin dad'i kuma zuciyar ta na gab da bugawa".

Salati sukayi .

Abdul ya waigo yana mai kallon Aisha.

Itako sanin abinda ya haifar mata da haka yasa ta sake kallon doctor.

Had'a ido sukayi tayi saurin kauda fuskan ta gaban ta na fad'uwa.

Idon tane ya sauka akan teburin doctor d'in, ganin sunan dake aje yasa ta firgita tare da mu'kewa tsaye.

" Lafia my Esha?" cewar Abdul.

Murmushi ya'ke tayi tare da zama don kada ta bada kanta tace" ba komai hubby".

Girgiza kai yayi doctor ya sake cewa" meye sunan ta?" zuciyar sa cike da tsoro.

"Fatima Mukutar" cewar Abdul.

Shiru yayi na wani lokaci yana tunani, idanun sa sun 'kara rinewa fiye da dah.

Daga baya ya rubuta sunan hannun sa na rawa.

Bayan ya gama rubuta abinda ya kama ta yakira wayar nurse suka zo suka tafi da ita d'akin da za'a kwantar da ita.

Bari su y Abdul a office d'in yayi tare da bin bayan su.

Abubuwan da yakamata ayi anyi aka mata harda alluran barci tukuna ya fito.

Kasa koma wa office d'in yayi domin jikin sa da zuciyar sa suna sanar masa da cewa Joy d'in shine, amma inda zai 'karyata hakan shine wannan Fatima take.

Motar sa ya shiga tare da kwanciya sai faman tunani yake shi kansa yana bu'katan a duba sa, don zuciyar sa zafi take. Ga wani matsanancin ciwon kai.

Rintse ido yayi hawaye na zubo masa, tare da cewa" mami baki min adalci ba, kin hanani tafiya, mami zan mutu, zan mutu indai tai aure mami kashe kaina zanyi".

"Bazan iya rayuwa babu itaba, zuciya ta zafi take. Mami da kanki zaki sanadin mutuwan yaron ki, baki barni da abinda nakeji nake dako ba na tsahon shekaru, kinje kin 'ka'kaba min wani aure".

"Gashi takirani ta kashe, nabi baya ta'ki d'auka. Ina ta sami number na Allah kad'ai ya sani sai ita, bansan meyasa ta'ki d'aga kirana ba, Allah sa ba fushi take dani ba".

"Mamina meyasa kika daina sona?" yace tare da fashewa da matsanancin kuka kamar wani 'karamin yaro.

Kiran wayar sa da akai yasa ya tuna yabar mutane a office d'in sa.

Duba fuskan wayar yayi Bros Abdul ya gani.

Share hawayen fuskan sa yayi tare da d'aukan goran ruwa ya bud'e 'kafar motan tare da wanke fuskan sa.

'Daukan wayar yayi dai-dai ya sake kira, don haka ya d'aga tare da cewa" srry yaya gani nan zuwa" tare da tsinke kiran.

Fita yayi tare da dai-dai ta natsuwan sa.

Da sallama ya shiga office d'in, ido suka bisa dashi, kauda kai yayi tare da cewa" yaya an gama komai Allah bata lafia ".

" Ameen".

"Meke damun ka? kaima kamar baka da lafia, kana bu'katan a duba lafian ka".

Murmushi yayi tare da cewa" kai yaya lafia na qlu fah. Mai ka gani?"

"Ba komai".

" Kai na sha'afa ango ne kai nan ba da jimawa ba, kai ya fara zafi ko?"

Murmushi ya'ke kawai yayi ba tare da yace dashi komai ba.

"Soja yace min ma wai yarinyan gidan alhaji Ibarahim ma'kocina zaka aura".

Zaro ido Aisha tayi har bata San lokacin da bakin ta yace" Husna? " ba.

Kallon ta Abdul yayi murmushi kwance a fuskan sa yace" eh, ai yayi sa'an mata don yarinyan ba dai hankali ba".

"Ummm yaya yarinyan na barci bari naje na duba wasu kuma".

" Tom nima wuce wa zanyi Aisha ne zata zauna da ita".

"Yauwa ina kai service d'in kama? wai my Esha tace kayi mata kama da wani".

Don son tabbar da idan sune yasa da 'kwarin guywa yace" wani 'kauyene mai suna 'yar kadde dake nasara.........." "Shine.... Wallahi shine....hubby shine" Aisha tace tana mai taya besty ta ba'kin ciki, shikenan zancen ta ya tabbata, ashe gaskiya take fad'a mata. To ya akayi ta sani? tayi zancen a zuciyar ta.

Nuna ta shima yayi fuskan sa d'auke da farin cikin da ya dad'e baiyi ba yace" Aisha.... Aisha..... ina Joy?"

Sai kuma yayi shiru gaban sa na fad'uwa, hararan sa tayi tare da cewa" ka manta da ita kamar yadda ka manta d'in".

Tare da kamo hannun mijin ta.

Abdul bai tashi ba sai faman kallon su da yake.

Ganin ba zai taso ba yasa ta saki hannun sa tare da barin office d'in da gudu tana kuka.

Auwal ya dawo gaban Abdul tare dur'kusawa hannun sa akan cinyan sa. Fuskan yayi jazur yace" y Abdul don Allah ina kasan Aisha? "

"Itace matata ai".

" Yaya nasan kasan 'kawarta don Allah tana ina a halin yanzu?"

Tausayin sane ya rufe sa don haka yace" itace muka kawo".

"Yaya Fatima fah kace sunan wancan?"

"Eh ta musulunta n...." tashi yayi baiko sake kallon Abdul ba ya fita office d'in.

Sauri-sauri gudu-gudu yake tafiya fuskan sa d'auke da fara'a.

Sai faman kallon sa ake tare da mamakin sa, don kullum fuskan sa a d'inke yake.

Shiga d'akin yayi tare da rufe 'kofar ya tsaya daga bakin 'kofar yana sauke numfashi tare da 'kare mata kallo....

To fah ga Zarah ga doctor d'in ta, mai zai faru? ansan ku na wurin 'yar Aliyu.

*COMMENTS*
*&*
*SHARE*
Chapter 26 · 0% Book details