← Book details Kauyen Yar Kadde Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 26

Sashe 19

Kauyen Yar Kadde Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi tayi tare da zuwa inda yake.

Dafa kafad'an sa tayi tare da cewa" ina zakaje habibi?" Banza da ita yayi tare da zare hannu ta daga kafad'an sa ya bar wurin.

Wurin ajiye motocin gidan ya nufa, 'barayin da motocin sa suke ya nufa.

Rufe suke ruf d'aga wa yayi d'aya bayan d'aya, gani yayi duka sunyi kura.

Cike da masifa yake 'kwala ma mai wankin motocin kira.

Da gudu ya nufo sa, ma'kaitan kaf sunji kiran nan har 'kwa'kwalwan su.

Hatta su mami sai da suka fito suga dalilin uban wannan kiran.

Abinda bai ta'bayi ba fuska babu walwala yana zuwa ya dur'kusa tare da cewa" gani yalla'bai" .

Ya bashi wani irin mari tare da cewa cikin masifa "wani irin iskanci ne zaka barmin motoci da 'kira eyeh?"

Yace yana 'kara masa wani, cike da girmamawa yace" yalla'bai go kwana hud'u baya sai da na wanke".

"Sai akace maka kuma jiya ko yau karka wanke ko?"

"Maza wanke min wancan jan yanzu na baka minti biyar kuma ya fita, idan ba haka ba yau sai kabar gidan nan" yace tare da tsaki ya juya.

Kamar d'azu suna kallon sa ya wuce ta gefen su baikoyiwa wani daga cikin su magana ba.

Da mamaki RAHAMA tace idanun ta cike da ruwan hawaye "Dady don Allah muje mu bashi ha'kuri muji meye damuwar sa, idan ma zaman 'KAUYEN yake so sai mu barshi ya koma idan yaso muyi masa ginin zamani a can. Sai ya rin'ka zuwa duk sati gida yana dubamu komu murin'ka zuwa".

Tunda ta fara maganan yake hararan ta har ta idda maganan ta.

Yau da badon 'yar gaban goshi bace tai maganan nan ai da tasha mari.

" Baki da hankali ko RAHAMA? ni kike so naje na bawa d'ana ha'kuri to bai zai ta'ba yuwu wa ba, don bashine ya haifeni ba, don ko uban sa.........."

Sai kuma yayi shiru "to bari kiji babu wata 'KAUYEN da zai koma, nd kwanan nan zai fara zuwa asibitin sa, don an gama komai bikin bud'e wa za'a sai ya fara aiki kinji ko?" Daga nan yayi tsaki tare da barin wurin.

"Kema dai inajin mahaukaciya ce ke, wai da bakin ki kike cewa Auwal ya koma 'KAUYEN da zama. Hmmm to bari kiji ko zuwansa sabis saboda ya rage wasu abubuwa da basu dace ba shiyasa muka dage kai da 'kafa ya tafi".

" Don sam bamu soba ke har Dady kan sa, saboda yayi hankali ne kawai muka kai sa" cewan babban wansu.

Kuka ta fashe dashi tare kallon mami da tai shiru .

Matsawa inda take tayi ta rungume ta tare da cewa" mami yanzu ya zanyi ya zanyi my brother ya dawo kamar da?" shiru tayi domin ita kanta abin na damun ta sosai.

Suna tsaye su biyu domin sauran sun bar wurin sai gashi ya fito.

Wuce su yake sonyi mami tace cikin matsawa da d'aure fuska.

"Ina zaka?" tsayawa yayi shiru ba tare da yace komai ba.

Tsawa da bata ta'ba masa ba shine tayi masa "dakai fa nake kayi shiru".

Fukan nan a had'e yace" nasarawa zani " daga haka yayi shiru.

"'KAUYEN nan zaka ko?" Shiru yayi ba tare da ya bata ansa ba.

"Wai shin Auwal meye kakeso? Meye kake nema a 'KAUYEN nan?" Still bai bata ansa ba.

"To tunda baka da ansan tambaya ta koma ciki" wani iri juyo wa yayi cikin tashin hankali yake kallon mamin.

Zaiyi magana tace" daga yau na sake jin sunan 'KAUYEN nan a bakin ka bare kace zaka sai na.............................

Comment nd share

Luv you all my fan's💋💋💋
[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*

*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*My ❤, my kaka, my Hafsatuwa😉, my Hafnan is back.💃💃💃💃💃💃💃💃💃ina masoya ku fito, ga shahararriyan Marubuciyan nan da ta saba nishad'an tar daku, wato Marubuciyan, SHI SO 'DAYA NE, FATALWAN MIJIN NA da kuma HIBBATULLAHI. ta dawo muku da wani shahararran littafin ta mai suna KAICON SO! Masoya ku hanzar to kar kubari a baku labari Hafsat Mustafah (Hafnan) ta shirya tsaf domin nishad'an tar daku, wa'azantarwa da ilimantarwa. Da abaka labari gumma ka bayar, saboda haka masoya ku fito 'kwai da 'kwar'kwata domin wanke idanuwan Ku, karrrrrrr kubari.....................*

*you will never brave, if you don't get hurt. You will never learn, if you don't make mistakes. You will never be successful, if you don't encounter failure..................Good morning😉🙏🏻

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

🅿3⃣7⃣➡3⃣8⃣

"Wayyo Allah na, wayyo mami na. Wallahi mutuwa zanyi, mami in............" Sai kuma yayi shiru, kallon sa tayi tare da cewa "indai na isa zan gani" daga haka taja hannun RAHAMA suka wuce ciki, Kamar zaiyi kuka ya tsaya kallon hanyan da suka bi. Yana tsaye ba'kin ciki fal a cikin ransa, amma ya ya iya, haka ya gama tsayuwan sa yayi ciki, ko kallon inda suke baiyi ba san da ya shiga.

Sati na zagayo wa akai gagarumin bikin bud'e asibitin, Dady yayi 'ko'kari matu'ka ya cika uba na gari wanda kowani d'a zai alfaharin kasancewan sa uba a gare sa.

Ya zuba masa duk abinda ya kamata, had'a dasu manyan doctors, kayan aiki na zamani tun daga 'kasanr waje da dai sauran su.

Amma abin mamaki koda na waiga inda mutumin ku yake sam babu alaman farin ciki a tare dashi, fuskan nan a murtuke.

Angama taro lafia sai dai fatan Allah sa albarka.

Ya fara aikin sa cikin nasara, yana samun girmamawa ga duk ma aikatan, suna matu'kar girma mashi, aiki sosai suke a asibitin ciki tsantsan 'kwarewa.

Lokaci 'kan'kani asibitin yayi suna, sun sami lambobin yabo daga wurare daban, don gaskiya doctor Auwal 'kwararrene.

Kimanin wata hud'u da bud'e asibitin sa, amma Auwal bai ma kowa magana sai ta kama dole, walan gida ko asibiti.

Haka zalika fuska a d'aure, mata na son sa kamar zasu mutu amma babu fuska balle su san'kafa mai tayin soyayyar su.

Duk wata mace maiji da kanta da isa, burin ta Auwal ya kula ta.

Amma hakan bai samuwa sam, Auwal ya zama wani irin mutum.

Auwal ya zama fitinan nane 'karfi da yaji, abi kad'an kayi kuskure zaka sha masifa ko kuma ya kore ka, gida ko asibiti. shiyasa duk wani mai son kansa da arzi'ki yana gujewa 'bacin ran Auwal.

Ba gida ba ba asibiti ba kullum kwanan duniya ka sake kayi kuskure kad'an yanzu zai 'kore ka, haka zalika ko sakon baka 'karawa a wurin.

***********

Zaune yake a bakin bed d'in sa sai faman kiran wayar sa da ya bawa Joy yake da ya zame masa kullum kamar ibada amma bata shiga.

Kamar zaiyi kuka yace" why my happiness? Kullum sai na kira layin nan yafi abinda yafi, ko ba'a baki bane? Kai inah nasan yaron nan sosai bazai 'ki baki ba".

"To amma meye na kashe waya?".

" Oh Allah na help me" yace tare da sake gwada layin, still dai abu d'aya baturiyan nan take ta nana tawa.

Cikin fushi yayi wurgi da wayar, kwanciya yayi a gadon tare da runtse idanu.

Bai ankara ba kawai sai ga hawaye masu d'umi suna zubo mishi, bai hansu su zuba ba har sai da suka bar zuba don kan su.

Dai-dai nan yaji ana knocking, tsaki yayi tare da tashi ya nufan 'kofan, bud'e wa yayi.

Ganin wacce ke tsaye yasa ya mai da 'kofa ya rufe, abin mamaki fanz RAHAMA ce fa akai wa haka, lallai abin babbane.

Kuka ta fashe dashi, yana jin kukan har cikin ransa amma yayi biris da ita, da yaji kukan na damun sa ma sai ya tashi ya shige toilet abinsa.

Kuka tayi sosai kafin tabar wurin, daga nan ta zarce part d'in mami.

Da gudu ta nufe ta, tace cikin kuka "mami don Allah kuyiwa my brother abin da yake so, don Allah ku barsa ya tafi can d'in don samun kwanciya hankalin mu. Mami bai magana da kowa, baicin abincin gidan nan sai da matsi".

" Mami jifa, ni na raine sa da hannu na, na kula dashi kamar uwan da ta haifesa, shine abokin shawarata, abokin firata, shine kesani nishad'i. Shike sani farin ciki fiye da kowa, baya son ya ganni cikin damuwa ko d'an 'kan'kani ne, ya tsani ganin 'bacin raina. 'Kanina na sona, kullum......." Sai ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi.

Rarrashin ta mami take, tace cikin lallashi "ki fita harkan Auwal idan ba haka ba ciwon ki na gab da dawo wa".

"Mami ina fita harkan Auwal fa kika ce?" Tace cikin zaro idanu "amma mami bakiyi tunani ba sam, Mami Auwal fah d'anki ne na duniya da lahira, maraya ne kin sani sarai, mami kina tunanin share sa da kuke hakan ya dace? har yau kun'ki zama dashi kuji meye damuwar sa meye yake so?".

" Shin haka ya dace kuyi ma maraya? kunyiwa maraya adalci kuwa? mami kamar bake ba, mami kiyi tunani da kyau shin abinda kukayi dai daine? Auwal d'ane d'an gata, saboda iyayen sa ma 'yan gatan kune. Mami kiyi tunani ".

" Mami kamar bake ba, mami Auwal d'inki ne fah, yaron Anty ne fah. Anty baza ta ta'bajin dad'in ace yau ga yayan ta tabar mata d'a cikin wannan yanayi ba, kin bar mata yaro cikin damuwa".

"Mami kin manta wannan shine jinin Anty 'kwalllin 'kwal? Shine ita fah tunda bata, mami ina son da kike mata ya tafi? wai yau da bakin ki kike cewa na rabu da jinin Anty na? Bayan Anty na itace uwata.".

" Anty da Abbey mutanen kirki ne sosai ke kanki sheda ce, uwa d'aya uba d'aya kuke mami ko kin mata Abbey 'kanin mijin ki ne uwa d'aya uba d'aya? ".

" Auwal jinin mune gaba da baya, da mamaci na magana da tabbas Anty ta sanar miki bata jin dad'in yadda kika bar mata yaro kamar mara gata ba, Anty ta mutu tana murna da murmushi na tabar farin cikin ta a hannun ki, saboda tasan bazaki ta'ba wofin tar mata dashi ba".

RAHAMA ke zancen nan cikin kuka mai tsanani.
Chapter 19 · 0% Book details