← Book details Kauyen Yar Kadde Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 26

Sashe 10

Kauyen Yar Kadde Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Horn driver yayi, mai gadi ne ya fito har wurin motan yazo tare da kallon mai taxi d'in yana cewa don sam bai lura da Auwal ba.

"Wa kake nema ne malam?" Kafin ya bada ansa Auwal ya fito daga cikin motan.

Hararan sa yayi tare cewa "zaka bud'e ko sai ka rasa aikin ka?" da gudu ya nufi get d'in yana cewa "yi ha'kuri alhaji bansan kai bane".

Koma wa motar Auwal yayi driver ya tada motar suka shiga, mai gadi na cewa " barka da dawo wa " hannun kawai ya d'aga masa.

A compound d'in gidan Auwal yace wa mai taxi ya tsaya, yana tsayawa ya fita a motar .

Mai aikatan gidan dake kai kawo suna ganin sa suka nufo wurin da gudu sauri-sauri.

Sannu da zuwa suka masa ya ansa yana shige wa ciki, yana shiga 'kayataccen parlourn gidan babba dashi wanda aka 'kawatashi da ababen more rayuwa.

"Mamina where are you?, am back, your handsome is back" yace yana kalle-kallen parlour don ganin ta ina mamin tasa zata fito.

Da murmushi farin ciki uwar ke sakowa daga steps .

Da gudu ya 'karisa gare ta, yana isa gare ta ya rungume ta.

Cikin farin ciki tace "oyoyo my happiness, godiya ga ubangijin tali kai da ya dawo min da farin ciki na lafia, welcome back autan mami, jarumin jarumai".

" Fitilar gidan Kabir Mu'azam, farin wata shakallo, sannu da zuwa shalelen Rahama da mami".

Wani irin farin ciki da natsuwa yakeji jinsa a jikin mamin sa.

Cikin shagwa'ba yace "mamina I miss you so much" kamar zaiyi kuka.

Bubbuga bayan sa tayi tare da cewa "nima haka son, muje kayi wanka sai kaci abincin ka huta".

Tana ri'ke dashi sukayi d'akin sa, had'a masa ruwan wankan tayi tare da kama sa, sai da takai sa bayin sanan tace " maza kayi wanka ka fito my handsome " ta fita.

Sai da ta fitar masa da kaya sanan ta sauka, zaune ta tarar da Baraka cikin girmama wa tace "HAJIYA wanda ya kawo autan ki yana jira a sallame sa".

" Ayyah yana ina?" "yana compound, okay kun bashi abinci kuwa?".

" Eh" "okay ina zuwa" tace tare da wuce wa d'aki.

Kud'i ta d'ebo masu yawa bata damu da ta duba ko nawa bane ta fito.

Har inda yake taje ta basa tare da masa godiyan kawo mata yaro cikin 'koshin lafia.

Godiya shima yayi sosai yana mamakin karamcin da aka masa, yana mamakin irin kud'in da aka basa .

Cikin farin ciki yabar gidan bayan ya fitar musu da kayan Auwal d'in.

°°°°Cikin jin dad'i yayi wankan sa, gurje jikin sa yayi sosai da sosai, kai kace zai sake fata.

Yana fito wa ya wani fad'a bed d'in sa yana cewa "Allah sa mami karta yadda na koma wanan 'kauyen mai cike da 'kazamai".

Tsaki ya saki domin Joy ce ta fad'o masa a rai.

Tashi yayi tare da shafa mayuka maau tsada sai 'kamshi suke.

Kayan da mami ta fitar masa ya saka tare da feshe jikin sa da turaruka.

Fito wa yayi sak Auwal d'in mami ba na 'kauye ba.

Tunda ya sako mami ta kafe sa da ido har ya 'kariso gaban ta.

Hawaye taji nason zubo mata amma ta matse, ta'ba wuyan sa tayi lokacin ya zauna kusa da ita.

" Auta ciwo kayi ne wai?" turo baki yayi tare da cewa "mami ba sai da na gaya miki ba?, ai wanan 'kauyen babu abinda bazai sa mutum ba. Don Allah mami na kada ki bari na koma idan ba haka ba sai kinyi kuka idan kika ga yadda yaron ki zai koma".

" Kayi ciwon kenan?, a'a kawai 'kauyen ne babu dad'i ga...ga........" sai ya kasa fad'a.

"Ga me son?" kasa magana yayi.

Cikin damuwa tace "son gaya min don Allah".

" Idan na gaya zaki hansu mai dani?".

"Uhum fad'a kaji my boy" turo baki yayi domin ya tsani a kira sa da boy.

"Mami niba boy bane, don Allah kibar cemin haka dani boy ne aida ba ai yun'kurin yin min fyad'e ba".

" What!!!" mami tace tana mi'kewa................

Maman kids😍😘🥰 ina godiya sosai.

Comment & share please🙏🏻🙏🏻
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*LITTAFAN MARUBUCIYAN:-*
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*

*Dedicated to my blood sister (Fatima Aliyu wakili) Allah ubangiji ya'kara miki lafia keda baby na*

*My fan's godiya a gare ku mai tarin yawa ina matu'kar 'kaunar ku masoya, a koda yaushe ina alfahari daku, ina jin dad'in yadda kuke bibiya na godiya mara iyaka🙏🏻*

*MY SAHIBA, Allah ubangiji yabaki lafia, masoya muna baran addu'ar ku, don Allah kusa sahiba a addu'a Allah ya bata lafia😭😭😭😭😭😭*

Sister Rukyn mama ina tayaki murna nan kamla littafin ki mai suna *HUSSAIN* Allah ubangiji yaba da ladan fad'a sai munjiki a sabon wani littafin nan kusa🥰

*Besty (maman Muhammad) kwana biyu shiru😟Allah ubangiji yasa kina cikin 'koshin lafia.*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

🅿2⃣1⃣to2⃣2⃣

Ya mutsa fuska yayi tare da had'e rai yana cigaba da cewa "da gaske nake mamina, har cikin gida wata shegiyar arniya tazo min fyad'e".

" Kutumar uban can, waye uban ta shegiya da zata lalata min yaro?, amma dai bata maka komai ba ko?" shiru ya mata.

Kallon sa tayi na wani lokaci sanan tace tana mai koma wa inda ta tashi "my son tell me the truth".

Shagwa'be fuska yayi tare da cewa " yanzu mami na baki yadda da yaron ki bako?, tom shikenan ai inaga sai tamin ciki zaki yadda".

Fashe wa da dariyan babban wansu dake tsaye tun fara shirmen Auwal yayi.

Waiga wa sukayi dukan su suna kallon 'kofar parlourn.

Hararan da mami ta jefa masa ne yasa shi gintse dariyan sa.

"Na shigo?" yace yana mai danne dariyan sa, a zuciyar sa kuwa yana mai mamakin yadda mamin tasu ke zama tana sauraron shirmen autan nata.

Mai da fuskan ta tayi kan Auwal tare da cewa "oho ma, kuma mutum ya daina mana la'be ko autana?, uhmm mami na, kuma na sani sarai sai ya kai maganan gaba. kuma kin san wani abu?" yace yana mai kai bakin sa kunnin ta don kar yayan yaji, nima bai bani daman jiba.

Sai mamin da take cewa "sun ma isa ne" kawai mukaji.

Tako wa yayi ya shigo ciki, yana mai jefa ma Auwal d'in mugun kallo.

"Mami kin gansa ko?, meka masa daga dawo wan yaro?, ban san fitina fah. A saki ma yaro na mara yayi fitsari, Allah wanan karon ran kowa zai 'baci a gidan nan".

Gyad'a kai Auwal yayi kamar wani yaro, hakan ma yake jin kansa indai yana gaban mamin tasa.

" Tashi muje kaci abinci idan ka huta ma 'karisa magana".

"Ku 'karisa shirme dai" cewar yaya nasa murya 'kasa-'kasa, "mai kake cewa?".

" A'ah, ni bance komai ba mami, kama ce " tace tana 'kwafa.

Dining sukayi, jan masa kujera tayi ya zauna yayan na kallon su ta fara feeding d'in sa.

Ganin ba zai iya jure kayan takaici ba yace "mami ina wuni" "lafia" tace tana mai cigaba da bama shalelen ta abinci.

Shiru ya zauna kafin ya mi'ke tare da cewa "sai anjima mami" ya fara tafiya.

Cikin d'aga murya tace "dawo" dawo war yayi "shin baka ga auta ya dawo bane?".

" Na gansa, shine ko gasheshi da hanya bakai ba?" zaro ido yayi tare da cewa "kai mami shine gaba dani koni? tayaya bai gaidani ba ni na gaida sa?".

" Amma ai kasan daga uwa duniya ya fito ko?, sai kabari ya huta idan bai gaida kaba sai kace amma ba yanzu ba, maza masa sannu da hanya".

Kamar zai kuka saboda ba'kin ciki yace "wallahi abinda kike baki kyau tawa sam mami".

" To ubana nuna min abinda zanyi" "idan bai nuna miki ba ni gani nazo zan nuna miki" cewar dady dake shigo wa parlourn.

Shiru tayi kawai bata iya cewa komai ba.

Kar'ban jakar hannun sa yayan yayi sukayi sama suka bar su nan.

"Mamina mai yasa Dady bai sona?" Auwal yace yana mai jin zafin yadda Dadyn ya nuna halin ko in kula a kansa.

"Mami yau fah na dawo amma duba babu ko farin ciki a tattare da Dady, anya kuwa mami? anya shi ya haifeni?" yace hawaye na fita daga idanun sa.

"Shishhh autana, dai na zancen nan Dadyn ka na tsananin 'kaunar ka, yafi sonka fiye da 'ya 'yan da.." sai tayi shiru.

Lallashin sa tayi, bayan ta gama lallashin sa sai suka mi'ke daga dining d'in suka nufi sama hannun sa sar'ke cikin na mami.

Dai-dai 'kofar part d'in Dadyn tace "muje ka masa sannu da zuwa ko yaron kirki?".

" Hmm" kawai yace sukai knocking suka shiga.

Zaune suka taddashi yana ma Yusif bayanin wani abu.

Zama mami tayi a kusa dashi, Auwal ya dur'kusa kusa da 'kafar ta tare da cema Dady "ina wuni Dady" cikin sanyin murya.

Da fara'a a fuskan Dady ya ansa masa, tare da cewa "maraba da autan mami shalelen RAHAMA".

" Yaushe a gari?" turo baki yayi tare da cewa "d'azu".

" Madallah, ya hanya? Alhamdulillah".

"Masha Allah" Dadyn yace yana mai cigaba da abinda suke.

Suna zaune suka gama ya sallami Yusif d'in.

Bayan fitar Yusif d'in ne take cewa "sannu da zuwa alhaji, yauwa madam, ya gidan?".

" Lafiya qalau, ya aikin?". "Sai godiya ubangiji" cewan dadyn. "idan kin sallami yaron naki sai ki sallameni nima" yace yana nufar bedroom.

Shafo gashin kan Auwal tayi dake she'ki kamar na larabawa.

"Son jeka huta ko ina zuwa na baka labari" murmushi yayi tare da mi'kewa yace "to mamina, barci ma zanyi idan nai sallan la'asar".

" A'a my son ba kyau barcin yamma ban yadda ba kuma kar ayi".

"Kaji?" "tom first love bazan ba" ya fita daga d'akin.

'Dakin sa ya nufa, bayan yayi alwallah yayi sallah sai ya d'an kishin gid'a yana kallon t.v, barcin yakeji "amma tunda mami ta hana ba zanyi ba" yace yana mai barin d'akin gaba d'aya.
Chapter 10 · 0% Book details