← Book details Kauyen Yar Kadde Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 26

Sashe 22

Kauyen Yar Kadde Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga wanna ranan shirin nan bai wuce ta. Yawan kallon shirin yasa taji tana matu'kar son musulunci don tana shi'awan itama ta iya karatun al'qur'ani.

Rana tsaka ta samu Aisha har cikin d'akin ta lokacin Abdul bashi ya tafi wurin aiki ita kuma night duty take da.

"Besty har kin tashi?" tace da ita lokacin da take shigowa.

Bata bata ansa ba illah 'karisowa da tayi ta zauna kusa da ita fuskan ta d'auke da murmushi.

Ri'ko hannun ta tayi tare da cewa" Aisha inason na musulunta" daga haka ta tsuke bakin ta.

Waro ido Aisha tayi tare da cewa cikin tsantsan farin ciki" da gaske my besty?" d'aga mata kai tayi.

Don haka Aisha ta rugume ta cikin tsantsan farin ciki, har da hawayen ta.

Babu 'bata lokaci Aisha ta kira mijin ta ta sanar masa, babu 'bata lokaci yace suje wurin limamin anguwan su.

Koda sukaje ba'a wani 'bata lokaci ba ta'kar'bi musulunci.

Aisha ta za'ban mata Suna Fatima, wani irin natsuwa da kwanciyan hankali taji yana wanzuwa a gare ta.

Ga wani irin farin ciki da takeji.

Fatima wanda suke kira da (Zarah) tana d'aukan abuabuwan addinin musulunci da ake koya mata fiye da tunanin ku.

Babu abinda tafiso a ciki rin Qur'ani, don haka ta mai da hankali sosai tana koya, saboda 'kwa'kwa da kuma son abun.

Cikin wata hud'u tayi sauka, zo kaga murna da farin ciki wurin ta da uwan uba Aisha, don haka gaga rumin walima aka shirya mata.

Sai dai abinka da boko da kuma ansaba shigan 'kananun kaya nana sai ma wanda ya 'karu sai dai na d'an d'aura 'karamin mayafi.

***************

Fatima mai farin jinine tun tuni balle ta musulunta don haka abin sai ya 'karu.

Maza da mata kowa nason ta kulasa tayi mu'amala da ita.

A haka ne tayi wata 'kawa a ma'kotan su mai suna Husna, Husna yarinyan nacin masifa. Kad'aci ke damun ta, da yake basu dad'e da tare wa ba. Kuma su biyu ne kawai 'ya'yan gidan daga ita sai wanta, da wannan dalilin yasa take shige-shigen ma'kota. Shine Allah ya had'a ta da Fatima taji ta Shiva ranata, sai ta maida gidan su faty ma kamar nasu tai ta shige mata. tun Fatima na 'kalleta har sai da yazo suka fara 'kawance domin sam bata da zuciya.

Tana zuwa gidan su Zarah sosai, amma ita dai-dai da rana d'aya bata ta'ba shiga gidan nasu ba.

••••••••••••••••••••••

"Don Allah ki rakani yau mana" cewa Husna suna zaune kan gadon Zarah bayan sun gama cin abinci.

"Kiyi ha'kuri gaskiya babu inda zani" cewar Zarah.

"Haba Zarah kullum nazo miki da bu'katata sai ki 'kimin, bansan mai yasa kike min haka ba. Wallahi ba kyau wula'kanci, har yanzu kin'ki sakin jikin ki dani. Wallahi Faty ina matu'kar 'kaunar ki har cikin raina, keko kin'ki sani a zuciyar ki ko kad'an".

"Meyasa? wallahi hakan bai dace ba".

" Allah baki ha'kuri tunda baki sona baki aminta dani ba nayi nan nagaji haka, kullum ni kenan nan nai ta bibbiyan ki kamar wata sarki to nagaji ba dole 'kawance" tace cikin fushi tare da mi'kewa idon ta cike da hawaye don tana matu'kar 'kaunar Zarah.

Amma ga dukan alamu ita bata son mu'amalan su.

Kamo hannun ta tayi tare da cewa" idan ba zamu dad'eba muje don inason naje wurin aiki 2pm dai-dai".

Dawo wa tayi tare da rungume ta tana maijin farin ciki.

"Ki muje idan ba haka ba na fasa".

" A'a muje hajiya ta mai ajin tsiya sai har dani za'a rin'kama wa?, gidan su hayati zani Maman sa ke nemana kinsan biki ya taso sauran sati uku, zani na kur'bi tsumi, kai matan nan Allah ya samata son d'an nan kamar shikenan mata".

"Bata gajiya sam wurin gyrani yanzu haka sati mai zuwa zamu India a min gyara na musamman, wanna kuma yayar sace ta d'au nauyi".

Ta'ba baki nayi tare da cewa" muje ni kada 'batan lokaci na'ki zuwa kimin kuka".

"Don idan na biye miki takan mutumin da bai San kinayi ba zamu iya kaiwa dare".

" Wallahi ni har mamaki kike bani ace wai macce kamar ke ki mutum ma mutumn da Sam bai ra'ayin ki, wallahi ko shine autan maza sai haka" ta 'karisa tare da sakin tsaki.

"'Karin kayan takaicin bai zuwa sai dai ke kije gidan su ku zanta, anya wannan auren za'a sami kwanciyan hankali kuwa?"

Murmushi mai ciwo Husna tayi tare da cewa" baza ki gane ba yarinya gayen ya had'u, yadda kika san ba mutum ba saboda kyau, ni tunda uwata ta haifeni ban ta'ba ganin kyakkyawan mutum irin saba".

"Oh really?"

"Allah kuwa idan kika gansa zaki ce na gaya miki, don gayen 'karshe ne".

Ta'ba baki tayi tare da girgiza kai ina mama kin ta, sai tace" muje fah kada na 'bata lokaci kije ki fasa rakani".

Fito wa daga cikin d'akin Joy sukayi suka mufi na Aisha kwance take tana duba wani littafin.

Sallaman su yasa ta kauda fuska daga littafin tare da zuba musu ido tana mai ansa musu sallaman.

Tashi tayi daga kwancen tana mai cewa" sai ina kuma 'yan mata?"

Husna tace" anty Aisha zata rakani wuse ne gidan 'kawar momy".

"Hummmm kice dai gidan siri kan mu" murmushi kawai tayi tare da cewa" sai mun dawo".

"Besty baki sallameni ba" cewar Aisha ganin Husna ta jata zasu bar d'akin.

Murmushin ta mai burgewa ta jefe ta dashi tare da cewa" sai mun dawo to" daga haka suka bar d'akin, ita kuma ta bisu da addu'a dawo wa lafia.

A compound d'in gidan suka tsaya Zarah tace" jeki d'ako motar ki ina jiran ki a nan".

Shagwa'be fuskan ta tayi tare da cewa" don Allah my Zarah yau mu fita a sabon motar can ta'ki".

Hararan ta tayi tare da cewa" na'ki" marairai ce mata tayi, ba don taso ba haka tasa aka fito mata da motar suka Shiga.

Tare da barin gidan, bata son hawa motar ne saboda wani saurayin ta mai nacin tsiya ya sayo mata.

Motar babu 'karya ta had'u.

Husna ke driving d'in sai faman santin motar take.

Wani tamfareren gida suka shiga, parking Husna tayi Tare da kallon Zarah tace" Zarahty ya kikaga gidan surukan nawa?" don taga tun daga get d'in gidan take kallo har suka shigo gidan.

Yatsina fuska tayi tare da cewa" gidan yayi".

"Muje to" tace tare da 'ko'karin fita daga cikin motan.

Rufe motar Suka yi tare da shiga ciki, sallama sukayi a bakin 'kofan babban falon gidan, shiru babu ansa.

Don haka suka shiga daga ciki, part d'in mami suka nufa, a nan suka tadda mamin. sallama sukayi ta ansa fuskan ta d'auke da fara'a.

Shiga sukayi har gaban ta suka gaida ta, ta ansa idon ta nakan Zarah da tunda ta gan ta taji wani irin fad'uwan gaba.

Idon ta nakan Zarah tace " Husna 'kawar kice wannan?"

"Eh mami" tana murmushi tare da kallon Zarah taga kanta a 'kasa kamar wata muna fuka.

Mami tace" sannu ko" take ce da Zarah.

Ansawa tayi sai mamin tace" tashi ku zauna a cushion mana, nasha gaya miki Husna kibar irin haka bakiji".

Tashi sukayi Husna na murmushi tace" Allah huci zuciyar mamin mu baza mu'kara ba".

"Allah sa, ya momyn naki?"

"Tana nan lafia qlau, tace a gai daki".

" Masha Allah, bari a kawo muku abinci" .

"Mami mun 'koshi" mamin tace tana hararan ta" dama nace baki 'koshi bane? kullum dama ke a 'koshe kike zuwa gidan iyayen naki".

"To yau sai kinci" tace tana 'ko'karin mi'kewa. Cikin murya mai dad'in amo da sauraro cike da natsuwa Zarah tace" mun 'koshi mami, don abinci muka gamaci muka fito".

Gaban mami ne ya sake fad'i dajin wannan muryan, tsayawa tayi cak tare da waigo wa tana kallon gefen da Zarahn take.

Had'a ido sukayi still fad'uwan gaba ne, murmushin ya'ke mami ta sakin mata tare gyara zama.

"Husna amma 'kawar nan naki ba 'yar nan bace ko?"

Murmushi Husna tayi tare da cewa" 'yar nasarawa ce, amma tana zaune a ne a garin nan".

"Oh sannu" tace da Zarah.

Ansawa tayi dai-dai nan RAHAMA ta shigo Auwal a bayan ta da sallama d'auke a bakin su.

Amma na RAHAMA ne ya fito, na Auwal kuwa sai idan ka kalli bakin sane zaka gane yayi sallama.

'Karisowa inda su mamin ke zaune tayi, shiko dodon mutane tsayawa yayi daga bakin 'kofar shigowa yana mai cewa" mami mun dawo zan tafi office sai na dawo" daga haka ya juya.

RAHAMA ko zama tayi tare da cewa" wassh mami nagaji walla............" bata samu zarafin 'karisawa ba sakamakon fuskan Zarah da tagani.

Idon ta da 'kwallan da ya taru cikin sakonni tace" mami kina ganin abinda nake ganin kuwa?"

Mami tasan me take magana akai amma tayi mata shiru.

Taso wa tayi tazo ta dur'kusa kusa da mami tare da kamo hannun ta tana mata nuni da Zarah tace" mami anty ce fah nake ganin, sai dai kuma jikin ta ya nuna na yara ne, dama idan ka mutu ka dawo yaro kake koma wa?"

Shirun mami yasa tace lokacin hawaye ya fara zuba" mami anty ce ko?... Itace ta dawo gare muko? dama ina mafarkin ta mami bata mutum ba, kullum haka take gaya min a mafarki, tana cemin zata dawo. Zata dawo ta rayu da Auwal d'in ta ".

" Mami taso, taso" tace tana janta, fizge hannun ta tayi tare da cewa cikin tsawa" RAHAMA ba ita bace, kina haukane? a ina kika ta'ba ganin mutum ya mutu ya dawo? Kuma ma idan itace sai tazama yarinya? kin manta tana da d'an da ya isa aure da yayi da wuri idan Allah ya albarkaci auren da yaran sa biyar ko hud'u".

"Idan kina mafarki ne ki farka don ba ita bace" mami ta 'karisa idon ta na zubar da hawaye .

Tun da suka fara zancen su tsoro ya shigi Zarah, don haka mi'kewa tayi ba tare da ta kalli inda Husna take ba zata fita.

RAHAMA tace" mami kalli zata gudu anty don Allah ki dawo kada ki barmu muna tsananin bu'katar ki.. Munyi kewan ki sosai. Ga habibin ki zaiyi aure kinga ga matar da zai aura nan, Husna jeki, jeki ga mahaifiyar mijin ki can".
Chapter 22 · 0% Book details