Sashe 1
Kauyen Yar Kadde Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[11/5, 9:49 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
🌳🌳🌳 🌳🌳🌳🌳
(Ta'kai taccen labari)
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫
We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO
LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*
Labarina 'kir'kirarren labari ne, haka zalika banyishi don wata ko don wani ba, idan yay yanayi da labarin ka kayi ha'kuri akasi aka samu😃.
Ya Allah yadda na fara lafia Allah ubangiji ka bani ikon gamashi lafia, Allah sa ya amfani al'uma amin.
Bismillahir Rahamanir Rahim
🅿1⃣to2⃣
'Kauyen 'yar kadde wani garine dake 'kasarmu ta Nigeria, garine dake jihar nasarawa, garine da ya had'a mutane daban daban. Ya had'a yaruka da dama, 'karamin garine wanda ya had'a mutane musulmai da arna, garine mai tattare da zaman lafia, ga tarin ni'ema. A kwaisu da noma iri iri.
A cikin garin yau na yada zango, gani tsaye a 'kofar wani d'an ma dai-dai cin gida, gida ne dai irin namu na 'kasa, kusa da gidan kad'an akwai wani 'karamin asibiti, gaba dashi akwai wani 'karamar primary school.
Shiga gidan nayi domin d'ako muku rahoto.
""Joy yau dai kinsan cewa a kwai Church ko?"" Shiru tayi kamar bada ita uwar take ba, "" Joy ina magana kina jina, baki tashi tsiyarki sai Sunday, da zarar ance yau Sunday ne shikenan sai ki kama nu'ku nu'ku, to maza ki shirya ki tadda ni can, time nata kurewa, saura kuma ki'ki zuwa"" tai 'kwafa tare da tale mata kai.
Har uwan tabar wurin bata tashi ba, tana nan zaune inda ta barta, bata tashi a wurin ba sai kusan hour1.
A kuma wannan lokacin ne na'kare mata kallo, yarinya ce 'yar karama da ita, shekarun ta bazai wuce 16 years ba, farace doguwa yanayin fuska kuwa ita ba mummuna ba haka zalika ba kyakkyawa ba, wato tsaka tsaki kenan.
Tana da diri mai kyau, yanayin ta mai cike da natsuwa, tana sanye cikin kayan barci Wanda suka zauna d'as a jikin ta.
Cikin natsuwa taje kitchen, d'iban d'umamen shinkafa jallof tayi a kwanan miya kamar Wanda za'a bawa d'an shekara biyu, koma wa tayi d'aki taci ko gama cinyewa batai ba taje ta aje tare da sake ruwan wankan a bokiti tayi bayi.
Ta'bata lokaci sosai sanan ta fito, ta shiya cikin wata 'karamar riga da dogon wando, rigan tad'ame ta sosai wanda ya fito da shape d'in ta.
Gara gashin tada yake ba'ki, mai Kyau dashi tayi Wanda ya kwanta a gadon bayan ta.
Babu wani kwalliya a fuskan ta tad'au Bible d'in ta ta rufo gidan nasu ta nufi hanyan church, shima Church d'in ba nisa yake dasu ba.
Tafiya take a hankali cikin natsuwa, komai nata masha Allah.
A haka tazo wuce wata wurin wasu samari da talura kullum safe wurin zaman su kenan koda ana sanyi damuna .
Wani daga ciki tunda ya hango ta yafara had'iye yamu, yana lashe le'be, har tazo ta wuce su duka zuka zuba mata ido kamar zasu lashe ta.
Lumshe ido yayi saurayin tare da cewa "" gayu al'kur'an yarinyan nan tayi, komai yaji wallahi ta zata yadda dani hmm da abin ba'acewa komai. Kai dana more"".
Wani cikin su ya sake cewa "" yarinyan badai kaya ba, sai shegen miskilanci da jijji dakai, ni da zata yarda wallahi da auren zanyi, kaji baza wawa shashsha madace fah kuma arniya, meye gamun buri da kada? ina laifin mu lalla'bata mu kwashi ra'ba?"" Wani wanda bakin sa ba'ki'kirin dashi yake cewa haka.
"" Ah Allah yarinyan zatai taurin kai, guma kawai na aura domin na bari ta su'buce min hmm inaga sai na kusa zaucewa. Wa zai yarda ma har ka aure ta?, ai duk tsiya indai yarinyan ta yarda ai angama"".
Haka dai suke ta zancen ta, itako bata San ma sunayi ba.
Koda ta'karisa church har an tashi, domin mutane har sun fara fita, da murna ta saki wani murmushin dake saka kuma tunta lotsawa, hakan kuma na'kara 'kawata fuskan nata.
Da mamaki nake kallon ta, tana tsaye kusa da church d'in saiga maman ta tafito ita da wata 'kawanta.
Da mamaki suke kallon ta uwan ta fusata domin gani ta ganta bata ko tsorata ba saima kafeta da ido da tayi kamar yadda tayi.
Don haka cikin zafin rai ta nufeta tana cewa "" yanzu don ubanki sai yanzu kika zoko?"" Tai mata ran'kwashi, taji zafi domin harda runtse kyawawan idanuwan ta.
"" Joy mekike so?, meke damun ki? bansan wata irin yarinyan gareni ba Sam baki maida addinin ki abakin komai ba, baki da hankali sam "".
'Kwanta tace "" madam Gloria kenan ai na fad'a miki indan baki raba yarinyan ki da watanan musulman ba sai kinyi kuka watarana"".
Haka maman tai ta mata fad'a ko damuwa batayi ba, itako 'kawar maman sai faman zugata take.
***
"" Mami Allah baza niba, indai ba Dady bazai je yasa su canza ba bazani ba, haba kamata a rasa inda za'a turani sabis sai wani gari ko nace 'KAUYEN 'YAR KADDE, ina bazai yuwu ba, i can't believe this"".
Yace cikin zafin rai, murmushi mai ciwo mamin tayi sa'an nan tace ""Auwal kasan kowe mahaifin ka, idan ya kafe to babu wanda ya isa ya tankwara sa, bai magana biyu tunda yace sai kaje to kayi ha'kuri kasan baso nakeyi ba don haka sama ranka salama kaje kawai Allah yaba sa'a"".
Numfasa yayi tare da kwanciya a kushin d'in da yake, zuwa tayi kusa dashi tare da d'aura kansa a cinyan ta tana shafa masa lallausan gashin kansa yana ta lushe ido, zuwa can barci ya kwasheshi.
Share
&
Comment
Comments d'in ku zaisa nagane yayi muku
Sai najiku
[11/5, 9:49 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

Dedicated to my son Muhammad, Allah ubangiji yaji'kan ka yayi maka rahama amin.
Bismillahir Rahamanir Rahim
🅿3⃣to4⃣
Mami na zaune har kusan hour amma bai tashi ba, tana ta faman shafa masa kai, tana ta kallon yaron nata cike da tausayin shi. Sallaman yayan sa yaron ta na biyu yasa ta d'ago kai tare da amma sa masa sallah mansa bayan sa matar sace da yarinyan su mai kimanin shekara biyar da watanni.
Itama d'auke da tata sallamar, "" mami shi kuma wannan lafia? ko shagwa'bar tasace ta motsa?"" hararan sa tayi tana mai ansa gaisuwan matar tasa.
Yarinya da suka zoda ita ta 'kariso gare su tana mai cewa "" tashi uncle, ka tashi zan sha ice cream"" tana mai girgiza shi, bud'e idanuwan sa idon cike da barci domin barci bai isheshi ba, koda yaga bebyn sace a gabansa sai ya tashi da sauri yana mai cewa "" oyoyo my beby, kece haka da safen nan?, uhum uncle, tashi muje ka kaini yawo sai mu biya shan ice cream"".
"" Angama my beby bari naje nai wanka, to uncle ina jiranka fah karka dad'e, okay "" sai lokacin yaga yayan nasa don haka sai ya 'bata fuska domin harda shi a son yake 'kauye fatar sa ta lalace, ko kula maman yarinyan baiyi ba ya huce. Itako cikin tsokana tace "" ohni waya ta'ba min maigida nane?" hararan ta yayi tare da wucewa fau.
Dariya suka kwashe dashi sai da mami ta harare su sanan suka daina.
"" Granny waya ta'ba uncle? waya ya 'bata masa rai? gasu nan kishiyan a gaban ki, UMMAH kece ko da abbah, kubar 'batawa uncle rai zai mutu idan kuna 'bata masa rai"" mai zasuyi inba dariya ba, harda kakan sai data dara.
Ganin suna mata dariya sai ta fashe da kuka harda birgima.
Ba shiri suka gintse bakin su, mami ta tashi tayi d'akin ta tare da iman.
Itama ikilima ta biyo su tana cewa "" baruwa na mami ni banma autan ki komai ba, oho dai kwaji dashi daga ke har munafikin mijin ki "".
"" Kai mami ni d'in ne munafiki? eh kai ko bakai ne kaja za'a turamin auta sauro ya kashe min shiba?"" Shiru yayi yana Sosa kai.
"" Kaban ansa mana"" tace tana mai zama akan sofa dake ciki d'akin nata.
Ya'ki bata ansa domin yasan bai dai gaskiya sai ma wayan cewa yayi da cewa "" bari na wuce office idan nataso zanzo d'aukan su, oho maka kuma ta Allah bata mutum ba insha Allah babu abinda zai samamin yaro, kuma mutum yasani nan gani nan bari ehey mutum ya fita harkan yarona, 'kwarai ma kuwa mami na"" yace yana mai shigowa d'akin.
"" Ga sojan ki can na hango sa yana parking motar sa, shima karki raga masa mamina kija masa kunni, harda shi bakin su d'aya Sam basu so suganni kusa dake sai sukama cewa wai bana abinda ya dace, kome nakeyi mara Kyau oho musu"" ya'karisa yana turo baki.
Dariya iman tayi tana cewa "" uncle kabar yin shagwa'ba kaga ka girma idan ba haka ba ko 'kawayena suka ga kana haka dariya zasu ma"" dariya suka soyi, amma sai suka matse. Domin yadda mami ta had'a fuska zataci 'kaniyan su.
Sun d'anyi shiru na wani lokaci shiko Auwal yana ma'kale kusa da mami kamar zai shige mata ciki so kawai yake babban yayan nasu ya shigo ayi masa nasa sanan yabar wurin.
Aiko sai gashi da alama tsaikon nashi yatsaya gaisawa da masu aikin gidan kamar yadda ya saba.
Aiko daga Auwal har mami suka had'a fuska kamar hadari.
Gaisuwar matarsa kawai ta ansa shiko sai faman hararan sa take.
Murmushi kawai yayi domin yasan kwana nan zancen don haka sai yace cikin ladabi "" Allah huci zuciyar mami ayi ha'kuri don Allah, mami kuma ma ai taimakon 'KAUYEN zaiyi, aikin lada zaiyi idan kikaga matsalan doctors da suke saikin zubar masu da hawaye "".