Sashe 25
Kauyen Yar Kadde Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga nan sai Abdul yace bayan baba ya sallame su" idan kun gama ina jiran ku saboda kada muyi dare" daga haka yayi musu sallama suka ya fita.
Yana fita yasa mai gadi shigo musu da kayan abinci ya kira Aisha ya'kara musu da kud'i, albarka suka sa masa sosai sa'anan suka mai godiya.
Basu suka bar gida ba sai da sukayi sallan la'asar sannan suka d'auki hanya.
********
Saura sati biyu bikin Husna aiki yama Zarah yawa ga shirye-shiryen biki ga aikin office, haka take ta fama, komai za'a sai Husna ta nemo ta. Tsare-tsaren biki itace kan gaba.
Anfara gudanar da biki tun biki ya rage saura sati d'aya, yau wannan bidi'an gobe wancan.
Kuma har yau Zarah bata ga ango yazo ba, daga 'kawayen amarya sai abokan ango aketa gudanar da abubuwa.
Da kyau dinner da za'ayi ana gobe biki bayan walima, sai Husna ta shiga damuwa na rashin halattan ango duk wurin shagulgulan biki, ta kuma gaji da tambayan da 'kawaye suke mata na rashin ganin angon, tun tana 'karya yanzu haka 'karyan ya 'kare kuma a rasa mai zata ce dasu.
Zaune take jugum a cikin d'akin Zarah ta buga uban ta gumi, har Zarah ta shigo bata san ta shigo ba.
Zuwa kusa da ita Zarahn tayi ta zauna tare da dafa ta.
Waigo wa tayi jin an ta'ba ta, ganin Zarah ne yasa ta rungume ta tare da fashewa da kuka.
Bubbuga mata baya Zarah tayi tare da cewa" lafia Husna? mai ya faru? mai akai miki?"
Cikin kuka tace" Zarah Auwal bai sona, da da yadda zanyi dana cireshi a cikin raina na huta. Zarah ina tsananin 'kaunar sa".
"Ni kad'ai nake haukata tunda aka fara shirin bikin nan, dai-dai da sau d'aya ya'ki halattan biki ko guda d'aya da aka gudanar. Gashi a halin yanzu 'karyana ya 'kare".
" Ya zanyi Zarah? ki gayamin, gashi anjima za'ai dinner ban san yadda zanyi yai attending ba".
Tace tana mai fashewa da matsanancin kuka.
Itama yanzu Zarah ta fara jin haushin abinda angon nan yake, mai yake ta'kama dashi?
Mai yasa baison Husna? Husna yarinya ce kyakkyawa, fara doguwa ga hanci ga zarara zaran yatsu, idanu.
Jiki ma masha Allah komai akwai, babu abinda tarasa na wanda d'ana miji yake so.
Uwa uba ilimi boko da na islama.
Ya fara bani haushi inason sanin abinda yake ta'kama dashi.
'Dago Husna daga jikin ta tayi tare da cewa tana mai kallon cikin idan uwan ta had'e da share mata hawaye.
"Husna tashi muje mu same shi" zaro ido tayi tare da cewa cikin tsoro" gaskiya bazan iya zuwa ba inajin tsoro gaskiya ".
Tsaki Zarah tayi tare da cewa" tsoro ya kasheki ya kuma kaiki ya baro".
"Tashi dallah muje" tace tana mai jan hannun ta.
Girgiza kai tayi idanun ta cike da hawaye tace" bazan iya ba, ya Auwal bai da mutunci nemo wani mafitan kawai amma ba wannan ba".
"Kirasa a waya to" tace" ko nakira sa ba zai d'auka ba".
"Bani number wayar sa" tace tana mai d'ako wayar ta.
Karanta mata Husna tayi ita kuma tana rubutawa.
Dialing number tayi, yayi ta ringing ba'a d'au call d'in ba.
Sake kira na biyu tayi sai da ya kusa tsinkewa sannan aka d'aga amma ba ai magana ba.
"Hello!" Zarah tace.
Zaune yake zumbur ya mi'ke tare da cewa" my baby, my Joyyyyyyyyyyyyyyyyyy"..................
*COMMENTS*
*&*
*SHARE*
Luv you all my fan's💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*
*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*
*we are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all.........DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
*DEDICATED TO*
*HASSAN ATK*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
🅿4⃣5⃣➡4⃣6⃣
Gaban ta taji ya fad'i, ko a mafarki taji muryan nan tasan ko na waye bare idon ta biyu. Jikin tane ya fara karma, hawaye taji nason zubo mata amma ta hanasu fita. "Sweetheart kinajina kuwa?" katse wayar tayi gaban ta na fugawa fat fat, idanun ta jajazir wani ba'kin ciki taji yana ziyar tanta a wannan lokacin ga damuwa mai tsanani da ya haifar mata da zazza'bi take a nan wurin.
"Me haka ke nufi?" tace a zuciyar ta.
Tasowa Husna tayi tare da cewa cikin damuwa" ya miki rashin mutunci ko? Dama na gaya miki ai bai da mutunci" bata bata ansa ba.
Ta sake cewa" dama na gaya miki Auwal bai da mutunci, d'an wula'kanci ne na 'karshe. Bani kad'ai yake ma haka ba, duk macen da ta nuna soyayyar ta gare sa sai ta fuskanci wula'kanci fiye da tunanin ki. Ya had'a komai, idan nace komai ina nufin komai ubangiji ya basa. Da wannan ne yake wul'kanta duk wanda ya gada ma. Amma ina son abina a haka, koda ace zai rin'ka miya da naman jikina ne. mai yace miki?"
Kasace da ita komai tayi domin jin kafafunta sun kasa d'aukan ta ga wani irin zafi da takeji a cikin jikin ta.
Dai-dai nan wayar ta yayi 'kara, kallon fuskan wayar tayi, ganin mai kiran kuma ga Husna na le'ka wayar yasa tai maza ta kashe wayar gaba d'aya.
"Mai yasa kika kashe wayar? da kin d'auka muji mai zai ce" ta tsinci muryan Husna na mata magana.
Murmushi ya'ke tayi tare da cewa" kai Husna to bashi bane" tace cikin dauri da son kauda yanayin da take ciki akan fuskan ta.
Husna tace" naga kamar number sane ai".
"To banashi bane wani d'an anace ne".
Shiru tayi kamar bata yadda da abinda tace mata ba, amma kuma sai tace" wai mai yace miki bayan ya d'aga kiran? naga tunda ki kace hello! baki sake magana ba. Na kuma gano damuwa a tattare da ke lokacin da kike sararon sa".
"Mai yace miki don Allah?"
"Bai fa d'auki wayar ba, wani abu na tuno da yasani 'bacin rai, amma bai d'auki wayar ba sam".
Husna ta saki numfashi tare da cewa" yanzu to ya zamuyi ga time nata tafiya? don Allah ki samo mana mafita".
"Ashhhh" tace tana mai ri'ke kanta tayi tagaga kamar zata fad'i.
Ri'kota Husna tayi tare da cewa" lafia? "
Ri'ke kanta tayi tace" kaina ne kemin ciwo".
"Ciwo kuma?" d'aga mata kan tayi.
"Mu shiga uku, yanzu ya zanyi? kwanta bari naje na gaya ma anty Aisha, daga nan zanje na sami Amina mu 'karisa kada lokaci ya 'kure, kisha magani amma ciwo bai min adalci ba".
Tace tare da barin d'aki, tana barin d'akin ta fashe da wani irin kuka, kuna wayar tayi tare da kallon number nasa.
Kurama number ido tayi hawaye na kwaranya akan fuskan ta.
Tsayawa hawaye yayi cak sakamakon ganin kiransa da ya sake shigowa.
Idon ta na fuskan wayar har ya tsinke wani na sake shigo wa.
A haka sai da yayi kiran da yakai goma tana kallo bata d'aga ba.
Daga 'karshe ta sake kashe wayar tare da 'kan'kame wayar.
Cikin kuka tace" ka haram ta a gareni, na haramta ma kaina kai, gobe kusan warhaka ka zamo mijin Husna".
"Kaman ta dani kamar yadda ka manta dani d'in. Ka bud'e saboda rayuwa gashi har zakai aure".
" Ka cuceni Auwal ka yaudareni, baka kyauta min ba, ace duk tsawon lokacin nan dana d'auka ina jiran ka, ashe zaman banza nake. Na hana kaina sauraron kowa da ganin kowa ina zaman jiran ka, ashe kai kana can kana rayuwa cikin kwanciyan hankali. Allah sai ya saka minin kaje, keje ban son ka, ban son ka. Kaje kuyi auren ku manta dani" tare da 'kara 'karfin kukan ta.
Jin alaman motsi yasa ta rufe idon ta kamar me barci, jikin ta yayi mugun zafi.
Aisha ne ta shigo, zama tayi kusa da ita tare da d'aura hannun ta a goshin ta.
Da sauri ta d'auke hannun tare da cewa cikin tsananin damuwa" innalillahi Zarah tashi muje asibiti a duba ki, ji jikin ki yadda yayi zafi, yanzu haka tun safe kike ciwon nan saboda shegen miskilancin ki kin gaggara fad'a. To wallahi ki sake hali don tsiyane wannan da cutan kai".
Shiru tayi kamar ba da ita take ba, har ta idah sababin ta tana jita. ta sake cewa" nasan kina jina ki tashi muje" tace tare da 'ko'karin d'ago ta.
Cikin sha'kewan murya tace" ki barni babu inda zani".
"Mai yasa? Zarah kuka kikayi? mai meke damun ki?"
Bud'e idanuwan ta tayi wad'an da suka canza kalla, sukai jajazir kamar an watsa barkonu. tare da cewa tana mai kallon fuskan Aisha cikin rawan murya had'e da in ina tace" Auwal...... Doctor...... Auwal d'ina shine....shine mijin....shine zai au......ri.......Hus.........na" tare da runtse idanun ta hawayen ba'kin ciki na zuba mata. Zuciyar ta na mata zafi.
"Ban gane me kike cewa ba, ban gane zancen ki ba, wani irin zancen kike? taya hakan ya faru? ke bazai ta'ba yuwuwa ba".
" Nace miki doctor d'ina shine zai auri Husna " tace cikin d'aga murya.
"Zarah kin san mekike fad'i kuwa? taya hakan ya kasance? huh? tayaya? wai ma tsaya, waya gaya miki haka ko don sunan su yazo d'aya?"
Cige le'ben ta tayi tare da runtse ido sosai don ta mugun jin zafi a cikin zuciyar ta.
"Kifar ka Zarah idan mafarki kike, and ki daina tunanin mutumin da ya manta dake, kinemi wani kibar min zancen sa. Don ya tafi ba zai ta'ba dawo wa ba, Auwal ya barki ba zai dawo ba, da zai dawo da tuntuni ya dawo. Ke yama manta dake, yanzu haka kila yana da 'ya'ya, don ba zai ta'ba zama har tsawon shekaru nan baiyi aure ba. Ke da ya dawo gareki".
Shiru sukayi na tswon wani lokaci.
Magan ganun Aisha sun mata zafi sosai, sun 'kara rura mata zafi a zuciyar ta.
Rawan sanyi ta farayi shine ya katse shiru nasu, mi'kewa Aisha tayi tare da cewa" subhanallahi, bari na kira hubby yazo shi yasaki ki zuwa asibitin".
Bata ce komai ba har Aisha ta fita.
Hawaye ke zubo mata akan fuska tana mai dafe da zuciyar ta da take jin kamar zai bar jikin ta.
Dawo wa Aisha tayi tare da Abdul, kiran sunan ta yayi shiru bata ansa ba.
Sai ya sake kiranta tare da had'a fuska" tashi maza yanzu mu wuce asibiti ".