Sashe 8
Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan mintuna hamsin ne Yaya ya shigo, ya yin da ya nuna mini sai dai in ta addu'a kawai, saboda aurena ba fashi, yanda yake gaya mini ma har sun tsayar da ranar ɗaurin aure, da sarki Jafar,nan da wata biyu shi ma domin mu samu shaƙuwa da juna.
Iya bayanin da Yaya ya yi mini kenan, ya fita shi ma jikinsa a sanyaye, ban taɓa shiga tashin hankali ba tun da nayi wayo sai a cikin ƙwanakin nan tara, ban taɓa tunanin za'a samu abin da zai girgiza min zuciya ba, amma yanzu ga shi na samu wanda Yake neman kawar mini da tunanina.
Yau ƙwana goma sha bakwai da zuwan sarki Jafar kenan ya rage saura ƙwanaki arba'in da uku yinin bikina, sai yau ne aka ce ai ga Faysal wanda zai zama angona, duk da sanyin da ake yi, amma sai da na ji tamkar an watsa mini ruwan zafi.
Mamee ta shigo ta umarce ni da in shirya in isa falon Daddy na yi baƙo, lallashi, nasihohi,Mamee ta dinga yi mini na kada in nuna masa halayyar sakarcina. Ni kuwa ba ta san gani nake ma ba ta ƙaunata.
Dogon siket da riga ne,ƙirar ƙasar Japan nasa a jikina, dogayen hannu gare su har idon hannuwana,buɗaɗɗan wuya gare su tamkar irin ɗinkunan da ake ya yi yanzu a Najeriyarmu, sai dai tare yake da ɗan ziririn mayafinsu wanda za mu iya cewa iya wuya kawai ya tsaya.
Mamee ta lulluɓa mini shi, ta sako leɓe ɗaya a gaban ƙirjina,ɗayan kuwa ya nufi bayana, gashin kaina kuwa yana can baya aka tattara shi, sai ƴan ƙwayoyi da ta ɗan gyara mini su ta sako su gefen fuskata, wanda ya bi ƙirjina ya ƙwanta.
Na sha turare da gyaran fuska, abin ka da kalar ruwan ƙasa mai cizawa ne,siket ɗin sai ya yi mini ƙyau,rigar kuwa baƙa ce mai ƙyalƙali a gabanta, ɗan mayafin kuwa kalar siket ɗin ne,baƙaƙen takalma na saka a ƙafata, waɗanda suka yi daidai da rigar, na ɗauki baƙar wayar hannu na riƙe a hannuna.
Kafin in yi sallama in shiga, sai da na leƙa ta kafar labule,jiri ne yasa na koma baya da ƙarfina, na sulale ƙasa na zauna, wanda na samu da ƙyar na isa ga bango na jingina,gumi ne ke ta tsatstsafowa daga jikina,a take na ji yunƙurin amai a lokacin da cikina ya juya.
Cikin zafin nama na yi gudu zuwa ɗakin Dad ɗina,na shige banɗakinsa,amai kam tamkar in zazzago kayan dake cikina, na samu da ƙyar na ƙwaye shantalin matsatstsan siket ɗin jikina na gabatar da fitsari mai yawan gaske, daidai lokacin da aman ya ɗan tsagaita mini.
A saman tudun da ake tsugunnin lalurar bahaya anan na zauna, tsayin mintuna goma, sannan na samu da ƙyar na ɗauraye jikina na miƙe, isa na yi ga madubin da ke manne a jikin (Wardrobe) ɗin Dad na kalli jikina yanda na faɗa a lokaci ƙanƙani, sannan na zauna saman wata ƴar kujera mai ɗan tebir a gefenta na kunna ƴar ƙaramar fankar da take a samanta, wacce zan iya cewa daidai fuskata kawai da wuyana take baiwa iska.
Shi ma domin in samu gumin da ke fitowa a jikina ya tsaya, É—an wanda ya fito kuma ya tsotse. A take kuma dabara ta faÉ—o mini na in dinga karanta "Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un!"
Cikin ƙanƙanin lokaci na ji na samu nutsuwa, na isa ga gefen gadon Dad,na ɗauki farar butar da Mamee ke ajiyewa, domin gyarawa Dad fuska, na ƙara gyara tawa fuskar na fice, sai falon Daddy,inda baƙo ke jirana wanda ganin shi ya tayar mini da hankali,wai shi Yarima Faisal.
Na yi sallama na shiga,a lokacin da wasu mutum biyu ke zaune a ƙasa a kowanne gefensa, biyu kuma na tsaye saman kan shi gefe-gefe, biyu na bakin ƙofa a tsaye, sun saka ƙofar a tsakiya ɗaya ne ke tsaye tsakiyar kanshi ta baya yana firfita shi da wannan ƙaton maficin nasu.
Da ƙyar ya ɗago ido ɗaya ta gilashi ya kalleni, maimakon in ga ya nuna razana da mamaki,sai dai na ga ya ɗan yatsina fuska, ya ƙara gyara ƙwanciya a kusurwar kujera ya kishingiɗa, sannan na ga ya ɗan ɗaga hannu kaɗan.
Sai na ji sun É—auki magana gaba É—ayansu na tsaye duk sun yi saurin zubewa suna cewa.
"Takawarki lafiya,ƴar manya, Gimbiya taka a hankali ƴar ƘASAITA,matar ƘASAITA,Yarima na gaishe ki,yana yi miki sannu da isowa."
Ɗaya daga cikinsu ya yi saurin isa kujerar da zan zauna yasa wani abu mai kyau kamar abin sallah ya shinfiɗa mini, ɗaya kuwa ya yi saurin isowa bayana da ƙaton maficin nasu ya fara yi mini fifitar tun Ina tsaye.
A take nima na fara nuna irin tamu isar ta mata, na zauna tsakiyar kujera na mayar da ƙafa ɗaya a kan ɗaya na ɗora, ina ɗan juya jikina a hankali. Yarima Faisal mutumin da muke takun saƙar ƙiyayya da shi,mutumin da ya kaɗe ni da mota, kamar ya banke akuya, shi ne yau ya zo wajena a matsayin mijin da zan aura mu yi zaman aure mai tsayi, na gani.
An ɗauki mintuna goma, gaba ɗayan falon shiru yake, sai masu gadin ke cewa ana gaishe ni, can sai ɗaya daga cikin waɗanda ke ƙasa zaune ya fara magana.
"Allah ya taimaki Sayyada, Gimbiya, É—an Sarkin Sarakuna,Yarima na gaishe ki, kuma mun zo nan ne domin amsa gayyatar da ki ka yi mana ta alheri, wannan da ki ke gani dai shi ne Sadukul ummati."
"Eh,Yarima kenan wanda yake jiran gado,yau ko gobe ko anjima ma."
"Haka yake, gaskiyarka ne, Sarkin dogarawan zamani."
"To shi ne muka zo a kan...."
Na É—ago masa hannu, ya yi saurin cewa,"Dole ne in bi umarni,shiru ma hankali ne, godiya nake."
*ƘASAITA BOOK 1*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 7
Sai da na yi yatsina nima na ɗaga baki da ƙyar na yi masu magana.
"Ku fita gaba É—ayanku ina son yin magana da shugabanku."
"Godiya muke, Allah ya daÉ—a girma, umarninki ne abin bi."
Suka sunkuya gaba É—ayansu gabanshi.
"Mun barka lafiya."
"Eh, Gimbiya ce ta bayar da umarni."
Ya ɗaga kai yana ɗan jingina shi,wato ya amsa kenan,wai! ƘASAITA. Ya amsa,eh, ya ce ya amsa godiya muke. Suka bi layi suka fice ƙofar waje.
"Yau fa ake yin ta!" Na faɗa a zuciyata, saboda na ga yanda za'a yi a yi magana tsakanin ni da shi. Mun ɗauki minti goma sha biyu kenan, ba wanda ya yi cikakken motsi a cikinmu, na ga ina ɓatawa kaina rai da lokaci, sai na miƙe na isa ga ɗan ma'ajin takardun Dad na ɗauko biro da takarda.
"Me ya kawo ka ne?"
Shi kawai na rubuta na miƙe na isa na miƙa masa, sai da ya ɗauki mintuna biyu, sannan ya miƙo hannu ya karɓa.
"Cewa aka yi in zo in gani in kinyi mini." Na karanta,a lokacin da ya taso shi ma ya miƙo mini.
"Ka koma ka gayawa wanda ya turo ka na ganka, cewa ba ka yi mini ba,ni Yasmin a ƙara gaba." Na miƙa masa.
Sai a lokacin ya É—ago kai ya kalleni, sai na ga ya yi murmushi, irin na isa ya mayar da kan shi.
"Dole ma in yi miki, tunda mu ba ma saɓa maganar iyayenmu,ki sani, ba ki tsarin cikin matan da zan iya aure, darajar Sarki kawai za ki ci." Ya miƙo mini.
"Ka tuna,ni ce wacce zan zame maka masifa, idan kuma ka kuskura ka tsallake É—aya daga cikin dokokin da zan dinga gindaya maka, zan bayyanar da boyayyen sirrinka a gaban Sarki!"
"Na gama da ke, tun da zan zamo mijinki."
"Ba ni da lokacinka, ina kuma gargaɗinka." Na miƙa masa, na koma cikin gida.
Ina laɓe ta labule na ga ya rubuta wani abu ya ajiye, sannan ya yi gyaran murya, sai ga su sun shigo a guje, ina kallo ya yi wa ɗaya daga ciki magana, amma ko shi wanda ake wa maganar sai da ya sunkuyo kusa da shi sosai, sannan ya ji abin da ake cewa, to balle ni da ke laɓe a bayan labule.
Cikin rawar jiki na ga ya sa hannu a aljihu ya fito da wasu dogayen takardu da biro ya miƙa masa da sauri ya sunkuya bayanshi, sai na ga ya ɗora a kai yana rubutu, ya ajiye.
Sorry,kin ji." Na É—aga kaina.
"Thank you."
"Je ki ciki kiyi hidimar ki zan zo miki da labari mai daÉ—i, nima dama ba san auran nake ba,ke tashi ma mu tafi tare,in ajiye ki gidan Salwa da dare na aiko a É—auke ki kin ji?" Na ce to.
Na miƙe na shiga gida na ɗauko ɗan guntun mayafi na rufe kaina da shi, wanda riga da siket ne na atamfar Super Holland ce a jikina wacce ake kira da suna A daidaita Sahu, inji mutanen Kano,mu kuwa muke ce mata Open Neck.
Da kuka na shiga gidan Aunty Salwa.
Aunty Salwa ta Zauna ta dinga lallashina ina gaya mata abin da ke damuna, da ƙyar na ƙwashe labari na gaya mata, tun farkon haɗuwata da shi da irin fansar da ya ɗauka a kaina,Ni kuma da ramuwar da nayi na ba ta takardar zancen da muka yi da shi yau da ƙarfe uku.
Ta yi shiru na tsaya kusan mintuna taƙwas, sannan na ga ta juyo da hankalinta gare ni.
"Haba Yasmin,kada ki bayar da kanki fa, kada ki zubar da ajinki,ki tuna ke ce macen da ya kamata a ce kin tsunduma kanki gidan sarauta, saboda ƙyawun da Allah ya yi miki.
Ki kalleni ki gani,ƙyawuna fa ya sani auran ɗan manyan mutane,ki sani dama fa ajinmu ya wuce na ƙananan yara, balle ƴaƴan talakawa."
"Gaskiya Aunty ni dai ina son Anwar,ko da kuwa zai dinga yin dako yana ba ni abinci ni shi nake so, balle fa da aikinsa."
"To yanzu Yasmin ya ki ke so ayi miki? Mu haÉ—a kai mu kunyata mahaifinmu,ko kuwa? What do you want?"
Ta matso ta ƙara dafa ni.
*Haba ƙanwata me yasa ba zaki haƙura ki bi umurnin iyayenmu ba, alhalin su suna yi mana abin da duk muke so,in na tambaye ki zaki iya ba ni amsa tsakaninki da Allah?"
Na É—aga mata kai, saboda kuka ya hana ni magana.
"Ba shi da ƙyau ne?"