← Book details Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 17

Sashe 5

Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsayin awa É—aya, sai na ga matar nan ta tashi, tana ganina ta taso a hankali ta iso wajena ta zauna.

"Yaushe aka kawo ki?"

Naji ta faÉ—a da Hausa. Na kalleta sosai.

"Ko baƙya jin Hausa?"

"Ina ji,É—azun aka kawo ni."

"Me ki kayi?"

"Ba komai"

"To Allah ya taimake mu"

"Musulma ce ke?"

"Eh."

Daga nan muka dinga hira da ita.

Ina nan har ƙarfe tara na dare, sannan naga waɗannan mutanen sun buɗe in da muke sun shigo, ɗaya daga ciki ne ya ce in taso, na yi wa wacce muke tare sallama mai suna Mabaruka. Tana kuka na bar ta tausayinta ya kama ni. A motata muka kuma shiga na ja har gaban gidan da muka tsaya da rana.

Muna tsayawa na ɗaga kaina sama sai na hango mutum zaune a barandar saman bene ya miƙe tsaye sosai ya juyo tare da dafa majinginin barandar, cewa suka yi in fito, na fito na kalleshi sosai, cikin sakan uku na gane mutumin da ya kaɗe ni watanni huɗu da suka wuce.

Me zan ce masa ni kuma yanzu bai yi magana ba, nima ban yi masa ba. Na girgiza kaina na juya na koma motata har na tashe ta ɗaya daga cikin ƙartin nan masu sanye da fararan T.shirt, ya sunkuyo ta gilashin da nake tuƙi ya ce.

"An baki last warning saboda haka yana gargaɗinki da kada ki ƙara shiga layin gonar shi, balle har ganganci ya kai ki kice za ki ratsa tsakiyar ta, ina fatan kin fahimta?"

Na ɗaga masa kai kawai, na ja motata har na yi nisa na tsaya na leƙo da kaina na ɗaga masa babban ɗan yatsana ma'anata a nan za mu haɗu wata rana.

A mota ne na yi tunanin ba zan gayawa Dad kome ya faru da ni ba, amma ni da kaina zan É—auki mataki wanda ko a hanya ya hango ni sai ya ce a sake wata. Har na isa gida ina tunanin hanyoyin da zan bi, amma na rasa su, saboda haka na ajiye lamarin, na dangana shi da ba aikin gaggawa ba ne.

Sai da Mamee ta ɗan yi mini faɗa a kan nayi dare, goma saura kaɗan, na san banida gaskiya na dinga ba ta haƙuri,gudun kada ta gayawa Dad shi kuwa ba wasa a lamarin sa, idan har ka taɓo shi. Kun san iyaye dai.

Bayan na yi wanka na shirya jikina ne na gabatar da sallolin da ake bina, daga nan ban iya yin bacci ba, saboda tunanin hanyar ramuwar gayyar da nake son haÉ—awa Yarima.

Wannan dalili ne yasa na tunano da litattafan novel na Turanci na shahararren marubucin nan (James H. Chase). Na san a cikin litattafan sa akwai idea zan iya samun wata hikima a ciki. Daɗi, murmushi, dariya, suka saukar mini a lokaci ɗaya, wannan ya sa na kashe fitilar gefen gadona na koma na ƙwanta, tare da tabbacin yanzu bacci zai zo mini. Haka aka yi kuwa,sallar Asubahi ma Mamee ce ta tashe ni.

Da ƙyar na shawo kan Mamee ta amince na fita, shima don na ba ta tabbacin iyakata Bookshop na nufa domin neman wasu littattafai, cikin saurin da bai fi na mintuna talatin ba na dawo,lode da litattafan James, sun kai goma sha biyar.

Tun da na haye sama ɗakina ko motsi na kirki ma bana son yi, abincin rana kuwa sai da la'asar na samu na ci shi. Sai da na ɗauki ƙwanaki goma ina nazarin litattafan nan da birona da zungureran littafina a gefe,in ta kama in rubuta in kuwa tawa muguntar ta faɗo in rubuta.

Wani lokaci a falon Dad,nake shigewa saboda kada a dameni, sai na ji dawowarshi, sannan in koma É—akina, na gama karantawa saura haÉ—a ayyuka. To yaya kenan?.

Ƙarfe taƙwas saura na safiyar Litinin wacce ta yi daidai da ƙwanana biyu da gamawa, na je na samu Katung Maigadi nan na zauna na gaya masa buƙatata, a take ya ce ai wannan duk abu mai sauƙi ne, tunda da akwai shi, sannan akwai abokanansa,in zan tura da kuɗi kawai su zasu kawo mini aikin da suka shirya. Na yi murna ƙwarai da gaske, sannan na ce ya bani ƙwana ɗaya.

Saboda na jima ban fita ba, shi ne na tambayi Mamee zan je gidan Aunty,ta amince mini. Ina isa gidan na ce mata kuÉ—i nake so, na dinga narke mata kamar zan yi kuka, har sai da ta bani dubu goma, na bugawa Yaya Habib waya na ce masa kuÉ—i nake so ya ce zai turo ta account É—ina wato banki.

Sai da na haÉ—o dubu talatin, sannan na É—auki ashirin a nawa (account) É—in na haÉ—a, na zo wajen Dad kuma na dinga fadanci cewa litattafai zan siyo, ya bani, saboda ganin da yake ina yawan karanta su, ya bani talatin. To saura Mamee, na girka mata kuka tun da ita ba wasa.

Ganin duk ranar kuka kawai nake, shi ne ta tausaya mini ta dinga lallashina, har tana tambayar me nake so, shi ne na gaya mata cewa account ɗina ba komai a ciki, shi ne nake son kuɗi in siyi litattafai, shi ne Dad ya bani kaɗan ,nan ta ce nawa ne? Na ce ashirin, ta ƙirgo ta ba ni.

Bayan ƙwanaki tara, ya zo ya ce mini komai ya haɗu, amma aikin farko kenan,yau wajen ƙarfe biyar na yamma in bi ta hanyar Bank Road saboda ruwan da ake yi na san yanzu zai kai har nan da tsayin lokaci a yanda (weather forecast) ta nuna.

Cikin ruwan sama mai tsanani na bi hanyar Bank Road,hanyar da bata cika mutane sosai ba, sannan tana da haɗarin bi a lokacin ruwa, ga shi yau garin na Jos shugaban ƙasa ne ya kawo mana ziyara, saboda ganewa idanunshi tabbacin zaman lafiyar da aka samu yanzu a Jos, madadin rikicin da aka samu tsawon lokaci ana yi a baya. A cikin shekara ta ɗari biyu da uku (2003).

Wannan yasa sai motoci ɗaiɗai ke yawo a garin,na laɓe da motata a gindin wata babbar mota na ga motocin Yarima sun wuce cikin gudu sai da suka yi nisa, sannan na ji sun bugo mini waya da in tafi,nima in bi hanyar, cikin natsuwa na dinga tuƙina, balle kuma yanda ake tafka ruwan sama.

Ban fi tsayin tafiyar kilomita ɗaya ba, sai ga shi na same su motocin su sun tsaya, ga ruwa ana yi balle su samu damar ɗauko wasu,ga ba motoci masu giftawa, saboda ruwa da ake yi kamar da bakin ƙwarya.

Tun daga É—an nesa na ga mutum a tsaye da lema yana É—aga mini hannu, daidai motarshi Yariman, na tsaya na zuge gilashina,nan wannan yake mini bayanin zan bayar da motata za a mayar da Yarima gida.

"A'a ka ce masa sai dai ya fito in rage masa hanya,me ma ya samu motocin naku?"

"Kawai gani muka yi motarmu ta tsaya,mun ɗan tsaya gyarawa sai ta bayanmu ta kama hayaƙi, ba mu lura da ta Yarima tayoyin sun sace ba sai da muka ta da ita da sunan shi a isa dashi gida."

"Ka gaya masa in ya amince, amma gaskiya bana bayar da aron motata ni in tsaya nan har sai an kaishi an dawo ba,ka tuna ni macece."

"To Hajiya."

Mayar da gilashina na yi na zuge, ina kallonsu sun ɗan jima, sannan na ga sun zagayo da sauri dukkansu sun kara masa lema tare da baza babbar riga,wai gudun kada ruwa ya jiƙa shi,a haka suka kawo shi har motata, inda aka buɗe masa baya ya shiga.

Ya koma ya ƙwanta yanda yake yi, kafin wani ya zagayo ya buɗe gaba,ni har na ja motata, amma don ƘASAITA ko motsi bai yi ba, balle magana.

A Hill Station Hotel na yi fakin da motata a wajen harabar ajiye motoci, ina fita suna isowa da baƙaƙen kaya dogaye suka nuna masa bindigogi a cikin motar, mutane ne sun kai goma.

"Fito!" Haka ɗaya daga cikinsu ya ce, cikin taƙama ya fito a daidai lokacin da ni kuma na cire baƙin gilashin da ke manne a fuskata.

Tabbas ko ban faɗa ba na san mamaki ya dirar masa a lokaci ɗaya don dai namiji ne mai ji da mulki, shi yasa bai nuna razanarsa a fili ba. Duk fuskokinsu manne suke da safar fuska baƙa, wanda gilashi baƙi ne ke manne da fuskarsu.

"Alhaji doka ta É—aya" wani daga cikinsu ya faÉ—a da harshen Turanci.

"Na farko za ka bi Madam zuwa sama, ba na buƙatar ka nunawa wani cewa kana tare da mu,in kuwa ka ƙi." Ya ɗago hoto duk dogarawansa ne tsare da bindigogi.

"Zamu É—auki rayukansu a yanzu, sannan mu É—auki naka."

Sai a yanzu ya samu ya yatsina fuska ya yi magana cikin isa a hankali.

"Okey,no problem."

Na yi gaba yana biye da ni, na waiga na ce masa.

"Ka je ka biya kuÉ—in É—aki ni nayi gaba."

Bai ko kalleni ba, ya yi wajen biyan kuÉ—i ni kuwa na haye sama.

Tsayin minti sha biyar sai ga shi ya miƙo mini makullin da aka rubuta No.120, ɗaki na ɗari da ashirin, ina tafe yana biye da ni har ɗakin. Na buɗe na shiga ya biyo bayana, sannan na juyo na fito na mayar da ƙofar na kulle. Na sauko na bawa Katung makullin.

"Ku ƙarasa sauran aikinku, amma kada ku yi masa komai, kuyi komai cikin mutunci,kun san babba ne ku ƙarasa haɗa komai, ina fatan kun gane?" Suka amsa eh. Na miƙa masa dubu talatin a biya a ɗan ci abinci.

Bayan ƙwana uku na dira a hotel ɗin da ƙarfe goma na dare, wanda su Mamee ma basu san na fito ba, na sa makulli na buɗe shi yana kishingiɗe a gado yana karatun mujalla ta Turanci (Tell) da ido ɗaya ya ɗago ya kalleni.

"Za ka iya tasowa mu tafi yanzu."

Bai ce komai ba ya miƙe ya zura babbar rigarshi da ke gefe ɗaya ya biyo bayana.

A motata har wannan gidan da yasa aka kai ni, amma inda yake da alama dai gidansa ne,kafin in shiga sai da na rufe fuskata da wata baƙar fuska mai tafe da kitso, sannan na ɗaga wata ƙatuwar ambulan na ce masa.
Chapter 5 · 0% Book details