← Book details Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 17

Sashe 6

Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ko baƙar magana ka gaya mini sai na kai wa Sarki wannan ambulan ɗin da ba zaka san ko meye a ciki ba, sai nan da ɗan wani lokaci."

Ya buɗe murfin motar ya fita ba tare da ya ce mini ƙala ba,ya juya ya tafi abin sa, nima na ja motata sai gida.

Duk da na yi masa haka, amma ban ga alamar razana ba a jikinsa, wannan ta sani kaina na ce lallai wannan ya cancanci ya hau gadon mulki, saboda ba a san matsoracin Sarki, ga shi kuma da iya ƘASAITA, na yi dariya ni kaɗai, nayi murmushi kuma sannan na haye gadona na ƙwanta.

Bayan ƙwana biyu ne na taka da kaina har get ɗin gidan sarautar nan, wajen sojojin nan muka gaisa amma a cikin ɓatacciyar fuskar nan, sannan na kawo ƙatuwar ambulan (envelope), na miƙa masu na ce.

"Saƙon Yarima ne daga ƙasar Sudan."

Suka ɗan dudduba ni da motata, sannan suka ce sai na zazzage kayan ciki, na ce masu ba zai yiwu ba, amma su buga masa waya su sanar da shi cewa yana da baƙuwa ta kawo masa saƙo amma kun ce sai na buɗe....

*ƘASAITA BOOK 1*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 5

Nan take suka buga masa, sai ya ce a karɓi saƙon kawai a kawo masa, ya san da shi,ni kuwa na juya na yi tafiyata gidan Auntyna.

Ɓangaren wajen Yarima kuwa,kaset ne aka kai masa da hoto ƙwaya ɗaya. Ya sanya kaset ɗin,lallai ya san na isa, hoton ƙwance yake ba riga a jikinsa da bargo lulluɓe daga ƙafafunsa zuwa ƙugunshi, sannan ƙirjinsa yarinya ce ƙwance a daidai lokacin da yake rungume da ita, ya kai bakin shi ya sumbaci goshinta nan aka ɗauki hoton.

Kaset kuwa daga inda ya ɗauki yarinyar ne har zuwa hotel ɗin da shiga ɗakin hotel ɗin duk dai yarinyar ɗaya ce, da takarda wacce na gaya masa, idan har ya ƙara sawa aka kama ni ko ya yi ƙoƙarin sawa a yi mini wani abu zan kai wa Sarki kaset ɗin da hotunan da kaina, na yi sallama.

Tabbas ni kaina na san na gama da Yarima, saboda yanzu ba shi da wata hanyar yi mini wulaƙanci,sai dai ni inyi yanda nake so a garin nan, da ya nemi takura mini da na tona masa asiri da ƙundin kaset ɗin da na ɗauka a matsayin ɓata masa suna. In kuwa haka ta faru, sarauta kuwa shi da ita har abada.

**** ****

Yamma ce yanzu wacce ta nuna ƙarfe biyar har da wasu mintuna goma, yanayin sanyin daminar garin sun haɗa sun mayar da garin tamkar dare ya yi, sanyi kuwa mai shiga cikin tsokar jiki.

Motocin da na gani a harabar gidanmu a lokacin da na shigo da motata, shi yasa na ɗaga hannuna na kalli agogon da ke maƙale a tsintsiyar hannuna, tabbas waɗannan koma su waye baƙin Daddy ne, da gani ka san manya ne na gaskiya, saboda ganin manya-manyan (Jeep) da na yi har wajen biyar,ban da ƙananan (Pegeout 406) ga zungureriyar motar nan irin ta Yarima Limousine Cadillae.

Don dai kalarsu ce ba ɗaya ba, kuma wannan mai murfin ƙofa huɗu ce, kenan babbar ta Yarima ce,na samu na raɓa tawa motar daga gefe ɗaya, sannan da Katung ya iso nake tambayarsa su waye? Nan ya nuna mini bai san ko su waye ba, amma manyan mutane ne (Big Men).

Mamee na falo ita ma da wasu mata har biyar, ina isowa na sunkuya har ƙasa na gaishe su, sannan na isa ga Mamee, na sumbaci kumatunta alamar na dawo kenan har zan wuce sai na ji Mamee na cewa.

"Ai itace wannan."

Wata mata wacce take zaune ita kaɗai a doguwar kujera wacce da ƙyar take motsi, ita ta yi ƴar dariya ta ce mini in zo.

Ina zuwa na zauna ƙasa kusa da ita, sai na ga ta shafi gashin kaina wanda yake a buɗe ta ce.

"She is beautiful, she deserves to be the Prince's wife,amma daga yau ki dinga kula da rufe gashin kan ki, saboda yanzun kin zama babba."

Ta faɗa da harshen Hausa, sannan ta ce in tafi. Ina tashi na kalli Mamee kallo mai alamar tambaya, amma sai na ga ta kawar da kanta, na taɓe bakina na haye sama, zuwa ɗakina.

Bayan kamar mintuna goma sha biyar, sai ga Mamee ta shigo ɗakin da nake ta miƙo mini wasu riga da zani na ɗanyan ƙwatin less (Cotton less) mai launin kore wanda ya chiza wato ruwan kayan sojoji (Amry colour) da takalma ruwansa, amma mai haske (light green) da file ɗanƙwalin saƙi, da abin sagalawa a wuya, duk ruwan takalman. Da wani irin English Gold wai duk in saka a jikina.

Tambayar Mamee nake, amma ta ƙi ba ni amsa, sai dai faman shirya ni take yi hatta shimi da siket ɗin duk kalar kayan ne,ni kaina na san nayi ƙyau, balle raba gashina biyu da Mamee ta yi ta sakko mini su a gaban ƙirjina, wanda ya sauko mini har kusan rabin cikina.

Fuskata kuwa ta sha gyara,ni kaina ban san Mamee ta iya ƙwalliyar kece raini ba, sai yau, tun da ita Mamee ba ta ƙwalliya,iyakacinta ta murza hoda kawai da ɗan ƙwalli a idanuwanta. Ta umarce ni da in biyo ta,na bi bayanta a hankali wanda take ce mini taku ɗaiɗai zan dinga yi.

Dama ni sarkin iya ƘASAITA, shi na dinga yi. Mun isa falo na ga matan da ke zaune duk sun ruɗe, na yi zaton iya nan kawai za mu tsaya, amma sai na ga an nufi sashen (Sitting room) ɗin Dad,ɗakin shaƙatawarshi da ni.

Muna kai wa ƙofar ɗakin na ga Mamee ta ƙara fesa mini wani Desginer ɗin turare, sannan ta ce.

"In kin shiga da kin kai tsakiyar falon ki durƙusa ki gaishe su, amma da harshen Turanci, ban da sakarci, ban da shagwaɓar da ki ka saba yi wa My dear,kina ji na?"

Na ce, "To Mamee,wai su waye,me suka zo yi?"

"Baki da amsa yanzun sai sun tafi."

Na É—an kaÉ—a kai na shiga.

"Tafiyar nutsuwa." Haka na ji Mamee ta ce.

Yawan mutanen falon Dad su suka sa na fara rikicewa wajen tafiya, amma tunanin kada in kunyata iyayena,shi yasa na yi saurin sanyawa jikina nutsuwa a take, hankalina kam ya tashi, sai dai ban yarda na nuna ba, saboda ganin dattijon mutum da na yi a hakimce a saman kujerar kishingiÉ—ewa, har da sa masa darduma mai laushin gaske a saman kujerar.

Ban da mutane biyu da ke tsaye a kan shi, suna sama da ƙasa da wani ƙaton abu mai gashi, faɗin shi kamar ƙaton faifan bakacan masara, sai dai bazar gashin jikinsa da kalar ja da yalo da ke jikinsa da mariƙin da suka fito da shi, zai nuna maka mafici ne.

Amma na fi ganin shi a cikin talabijin, shi ma sai in an nuno wani sarki. A zuciyata na ce dan kinibibi duk A.C É—in da ke falon Dadyna, amma sai an yi masa fifita.

Yanda Mamee ta ce inyi haka na yi,bacin duk dama hankalinsu ya dawo kaina tun da na shigo. Dad É—ina ne ya iso ya kama ni ya tashe ni tsaye, sannan ya fara magana.

"Your Highness this is My daughter Yasmin."

Ya tafi da ni har gaban wannan mutumin,ya tsugunnar da ni.

"ÆŠiyata É—ago da kanki."

Na É—ago.

"Very fine lady,na tabbatar É—ana zai yaba da ita."

"Haka ne, haka ne, ai ba ja."waÉ—annan mutane na tsaye bayansa suka faÉ—a.

Sannan ya kama hannuna muka miƙe tare da shi, shi wannan mutumin ya juyar da ni na kalli ragowar mutanen da ke baje a ƙasa, sai dai wasu uku da ke zaune a kujera daban-daban.

"Wannan ita ce matar da na zaɓawa ɗana Faisal, ina fatan ta yi?"

"Ta yi, tayi."

"Waziri ta yi?"

Ta yi,ta yi."

Sai na ji wazirin ya ƙwala kira, amma ban ji yanda ya kira sunan ba, sai na ga wasu mata su huɗu sun shigo ɗauke da farantai lulluɓe da kaya a ciki, da wani farin gyale sun ajiye gabana.

"Ƙyauta daga waziri." Inji wani ya faɗa.

Aka dinga shigowa da kaya kala-kala,ni dai ina daga tsaye, daga a ce ƙyauta daga wa ne, sai daga wane, bayan kamar minti ashirin aka sallame ni na tafi. Raina a ɓace na shiga falon Mamee baƙin da na gani da waɗannan mata, shi yasa na ɗan saki fuskata, sannan na sunkuya na yi masu sallama na haye sama.

Komai cillar da shi nayi daga tsaye, takalma,tuntun saman kaina,sarƙar,awarwaron, na faɗa a gado.

"Me ye wannan?" Na tambayi kaina.

"Me su Dad ke nufi da ni,ƙyautar da ni suka yi ko kuwa siyarwa? Yanzun manufarsu in rabu da Anwar Proposed ɗina? Mutumin da nake ƙauna.

Mamee fa ta san yanda nake son shi, shine zata je ta yadda a haɗa ni da wanda ban taɓa gani ba, hawaye suka gangaro mini,shi kenan rayuwata ta raunana, tun da za'a aura mini wanda ba na so, yanzun ba za'a barni in zaɓa ba kamar yanda Aunty Salwa ta zaɓa?.

Kenan an nuna mini a gidan nan an fi son Aunty Salwa da ni, yanzu duk ƙaunar da na ga ana nuna mini,ashe duk ƙarya ne, ashe iyaye ma na yaudarar ƴaƴansu,anya kuwa ma su suka haife ni? Ban yarda ba,ƙila dai ruƙona suke yi, shi yasa za su haɗa ni da ɗan gidan sarauta ko sarautar wane gari ce ma? Oho. Ko dai cikin dangin Mamee ne waɗanda ba su Musulunta ba, na ga suma ƙyansu ya yi yawa irin nata. Tashin motocin da na ji, shi yasa na rarrafa daga gadona na ɗaga labule ina leƙensu.

Suna wucewa na sauko ina dire-dire na kuka, na shige banÉ—aki,dama na sani da ban tafi da wayata ba, duk ita ta janyo mini, da bata nan ai da ba za'a kira ni in zo ba. A banÉ—aki nake wannan tunanin da kuka mai fitar da sauti, to an fa tuno da Allah duk da dama muna kiyayewa mu a gidan nan.

Nan take na yi alwala na fito,ai sai sallah, kafin a kira sallar magriba na yi nafila ta kai goma, ina ji Mamee ta leƙo ɗakina ta koma,ganin ina sallah.
Chapter 6 · 0% Book details