Sashe 15
Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙarfe biyar na yamma na dinga haɗa Aunty da Allah a kan ta sa kayan wasa mu je muyi tennis a filin wasa. Siket da riga iya gwiwa na saka,farare ƙal, da ganinsu ka ga kayan wasa, saboda wuyan T.Shirt ɗin kore ne zagaye da ita, haka hannuwanta ma, sai bal ɗin matse gashi wanda na roba ne,koriyar safa ce amma farin kambos ne a ƙafata.
Ita kuwa Aunty Siket ɗin ta har ƙasa yake, sannan ta ɗaura ɗanƙwalin wasa sai dai ita ma farare ne na wasa, na umarci su Mansura da su je su duba mana lafiyar filin wasan, sannan su isa da ruwa da lemo kafin mu isa, wanda tuni nasa an yi gaba da kayan wasan.
Shigar da nayi ita tasa na ji ni tamkar an yi mini albishir da Aljanna, saboda samun kaina da na yi cikin farin ciki da nishaɗi,hakan yasa ma da guduna na isa filin wasan, saboda motsa jikina. Aunty kuwa ta biye mini ne kawai na san don dai ta ja ra'ayina in yi haƙuri in ci gaba da zama.
Wasa kam ya yi daɗi, amma har yanzu ba wanda ya ci wani. Ikon Allah kuwa Allah ya ba ni Sa'a na ci Aunty,ban san lokacin da na dinga ihun murna ba, har da su tsalle. Kamar an ce in kai idona ga barandar Yarima, sai na gan shi a sunkuye ya dafa ƙarfe yana kallonmu, kallon da nayi masa ya kai na minti ɗaya sannan na juyo na yi tsaki,a inda ya ɗago mini babban ɗan yatsa,alamar yabawa da cin da na yi.
Na kira Mansura na ce ta je ta kirawo min jakadiya ta amsa tare da tafiya da saurinta. Ban fasa wasan ba wai saboda ganin Yarima, sai dai jikina na bani kallona yake yi. Tsawon mintunan da ba su wuce taƙwas ba, sai ga jakadiya da saurinta tana zuwa ta zube gefena a inda ina wasana ina gaya mata saƙo. Saƙon kuwa bai wuce ta je ta cewa Yarima ga Antina ta zo in yana da dama za su gaisa.
Gudu nake kada in ce yazo Aunty ta yi mini faɗa,ni kuwa ba na fatan ƙara zuwa sashinsa,lallai zance,ko kuwa tabɗijan! Ganin Yarima a filin da muke wasa, shi kaɗai da silifas a ƙafarshi,shin ina aka ajiye girman kan da ƘASAITAR, koda yake na lura a cikin gidan shi sauƙin kai ne da shi, tunda har yana ƙwanciya ƙasa saman kafet,ko filo babu.
Cikin rawar jiki ƴan matan nan suka sunkuya suka gaishe shi. A idona cikin mintuna biyu na ga an kafa rumfar lema da kujerunta uku amma na (Cane) irin kan Nan mai lanƙwaso da tebir a tsakiya, wannan duk aikin wasu maza ne, waɗanda ban ga isowarsu ba, sai dai aikinsu kawai na gani. Mulki, na ce a zuciyata saboda ganin ga rumfar da aka tanada don hutawa, amma har sai da aka kafa masa wata.
Mamaki yasa na yi tsaye na riƙe ƙugu da hannuwana duk biyun, ganin yanda ya gaishe da Aunty har da ɗan russunawa alamar girmamawa, yasa na dinga tunanin anya kuwa Yarima Faysal ne kuwa? Tambayar da nayi wa kaina kenan a daidai lokacin da na ga sun jera da Aunty suna tafiya zuwa ƙarƙashin inuwar lemar nan.
Har sai da suka zauna, sannan Aunty ta yi mini maganar wai in zo,a lokacin ne ma hankalina ya dawo a jikina, na iso na zauna a tawa kujerar, wacce ke gefe É—aya,hakan kuwa ya yi É—aya da lokacin da wani mutum ya iso da farantin kayan sha,su lemo kenan, wanda gefensu kuma tufa ce (Apple)
Hira sosai shi da Aunty. A cikin hirar na ji tana cewa, "Wai ranar da ku ka je gida Mamee ta gaya mini,cewa kun biya ta gidana ba ku same ni ba." A zuciyata na ce, Au! Ashe har gidanmu ake zuwa ba a gaya mini ba,neman shiga.
Iska ta taso mai ƙarfin gaske, wanda zan iya kiranta da guguwa,jin yanayin wasu addu'o'i a bayyane yasa na yi mamaki, a inda ni kuma gashin kaina ya kaiwa gefen fuskarshi ziyara, yasa hannu ya cire shi a hankali,a inda ya ci gaba da magana da Aunty.
"Aunty ki yi mata faɗa, ba ta son ɗaura ɗanƙwali ƙwata-ƙwata, tunda ta zo gidan nan ni dai sau ɗaya na ganta da ɗankwali, shi ma na san don gidanmu za'a."
Ta juyo gare ni, "kin ji ki daina."
"Aunty ba fa kowa a inda nake sai yaran nan su Mansura fa."
"A yanda ki ke gani ba,ni ko jiya na ji cikin dogarawana wasu na yin fasalin ƙyan gashinki,kin ga kenan suna kallonki in kin fito."
Maganar da yake yi mini kuwa tana nuna cikin jin haushi yake yin ta, na kalli Aunty, "Sai kin shigo Aunty." Na miƙe a fusace.
"Yasmin zauna." Na ji ya faÉ—a. Na juyo na kalle shi sannan na kalli Aunty. Aunty ta daka mini harara na koma na zauna, amma sai na kawar da fuskata É—ayan gefen.
"Aunty kin ga matsalar da muke ciki kenan ni da Yasmin ba yanda za'ayi in ce tayi abu ta yi shi, alhalin ta hakan za mu samu jituwa, amma na yi iya ƙoƙarina ina ƙasƙantar da kaina ina bin abin da ta umarce ni, yanzun kin ga an kusa ƙwana ashirin da ce mata ta yanke farcinan hannunta, amma ban isa ba."
Aunty ta juyo ta kalleni, "Yasmin tashi ki shiga ciki ina zuwa."
Na tashi cikin fushi na yi gaba, har sai da na yi wanka na shirya sannan Aunty ta shigo a inda ta same ni falon sama.
"Yasmin,duk na fahimci matsalarku, ba ta wuce jiji da kai duk ya gaya mini irin yanda ku ke tafiyar da rayuwarku. Na ba shi haƙuri. Yasmin ya ce baki girmama shi,in ya aiko ki je, sai ki mayar da ɗan aiken da cewa ba ki zuwa.
Ya nuna mini kina kunyatashi a gaban barorinsa,a nan ma kuma na gaya masa kin gaya mini aiken jakadiya ne baƙya so, ya ce yayi alƙawarin ya daina, sai dai ko aike na hidimar gida, yanda yake nuna mini ke ce mai matsalar kin rigaya kin sanya tsanar shi a zuciyarki. Haba ƴar ƙanwata, yanzun daɗinmu ne a ce mu dinga ɓatawa iyayenmu rai, kiyi tunani mana, wallahi na san Dad na kuma fiki sanin halayyarsa,kin ga saboda wannan matsalar,za ku iya mugun ɓatawa.
Ba na mantawa akwai wata rana muka yi rigima ni da Abdulƙadir lokacin ina goyan Tahir kin ga bai fi shekara ɗaya da ƴan watanni ba kenan, rigima ta kai mu har gida,kin ga yanda Dad ya yi mini kuwa. Ke a takaice sai da na shekara uku Daddy baya amsa gaisuwata sosai,in ma na samu ya amsa, balle faɗan ni ce banida gaskiya. Kinga kuwa a nan ke ce ba ki da gaskiya, duk da nasan ba ƙya son shi, amma ai shi Dad gabansa kin nuna za ki zauna da mijinki lafiya."
Nasihohi da faɗa su Aunty ta dinga yi mini,a inda ni kuma ba ni da wata maganar mayar mata sai kuka. Kai a ƙarshe na ce mata.
"Aunty ba na son shi,bana son shi, shi ma fa baya sona, jiki na kawai yake wa ƙwadayin ya samu Aunty."
Cikin kukana da mayar da kaina saman kujera na ƙwanta, Aunty ta ɗago ni ta rungume a inda ta gaya mini maganganu masu ƙwantar da hankali, sai da taga na ɗan samu kaina sannan ta tashi ta shiga wanka,a inda sallar magriba ta kawo jiki.
Bayan sallar magriba ne, sai ga Uncle ya zo É—aukar ta, sai dai kawai muka gansu sun shigo tare da Yarima,mu kanmu mun yi mamaki, sai dai kuma tunanin gidan da ake tsaron shi kamar wannan gida, dole ne a san mai shiga da fita, har mota muka raka su Aunty Salwa,ni da Yarima muna tsaye dakarunsa guda biyu suka buÉ—e but É—insu Aunty suka sa musu wasu kaya, ban san ko su meye ba.
A daren ba a ƙwana ba, na ga masu aiki na ta haɗa wata waya a cikin gidana, wacce na ga an liƙa wani ƙaramin jan abu a falon ƙasa, haka a falon sama. Ni dai iyakaci na idanuwa, sai da ma suka gama, ana gwadawa a ga in ya yi,jin ƙarar shi yasa na gane Inner caller abin da ake kiran mutum idan yana nesa.
Ƙarfe sha ɗaya saura ƙwata na dare na ji ƙararrawar nan ta yi ƙara, doguwar rigar bacci ce a jikina tare da ƴar samanta, mai ƙyan gaske, har na kallu ba zani ba, saboda na rigaya na yi shirin ƙwanciya, amma tunanin abin da muka yi da Aunty yasa na ɗauki doguwar alkyabba na ɗora ta sama, sai ɗanƙwalinta na rufa a kaina.
Gaskiya aƙwai tsoro fita a wannan lokacin, don dai ma ko'ina gidan fitila ce tamkar da rana ne, ƙasan falonshi ba kowa, sannan fitilu duk a kashe suke, sai ƙwaya ɗaya, wacce ta bayar da kalar duhuwar haske na mayar da ƙofa na rufe kamar yadda na ganta.
Falonshi na sama ba kowa, sai duhu ne a tare da shi, ba wata fitila ko ɗaya, cikin jin haushi na tura ɗakinsa na shiga, tare da sallamata. Fitilar gefen gado ce kawai a kunne, amma ban ga kowa ba a cikin ɗakin,sanin zuwan da nayi da rana na same shi ƙasa ƙwance, yasa na dinga kallon ƙasan ɗakin, amma ban ga kowa ba.
Wucewa na yi barandar shi inda na san ya cika zama, shi ma baya nan, na leƙa kaina ƙasan barandar, amma ban ga kowa ba, sai ma na ji tsoro ya kama ni da baya da baya na dinga tafiya,wai ni gudun kada in juya wani abu ya kama ni,banyi aune ba sai kawai na ji nayi karo da wani abu ta bayana, kafin in yi ƙoƙarin juyowa sai na ji an rungume ni gam,an sa gefen fuska a tawa fuskar.
"Yasmin gani nan." Ya faÉ—a cikin muryar raÉ—a a hankali na bi na zame jikina,a inda na bi ta gefensa na wuce na zauna kujerar kusa da ni, wucewa ya yi saman gado ya zauna, sannan na ga hasken fitila ya gauraye É—akin.