← Book details Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 17

Sashe 14

Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarfe goma na safiyar juma'a na shirya tsab na fita,a inda na samu motocin da na bayar da umarnin a shirya mini su tun jiya. Motoci ne guda huɗu, ɗaya ta maza ce ƴan rakiyata, ragowar kuwa ƴan matana ne, ba wani waje za mu ba,illa gidan yari zan kai masu ziyara in ga ko ana yi masu yanda na umarta.

Bayan na shiga mota ne, na hango Yarima saman barandar É—akinsa yana kallona, tare da al'ajabin ganin yanda na danna kaina a mota, amma abin ka da sarauta,ko ya nuna alamar ya yi mini magana, balle ya tambaye ni ina zani.

Na ji daɗi ƙwarai da gaske, yanda na ga mutanen gidan yarin nan duk sun fara ƙyan gani, duk da akwai rama a jikinsu, amma ni kaina na san ta ragu sosai, gaba ɗayansu aka tara mini su,a inda na yi masu ƴan nasihohi, sannan na ƙwantar masu da hankali da maganganu masu daɗi.

Da ganin yanda suke nunawa ka san sun ji daɗi sosai,nan take na yi masu alƙawarin kawo masu ƙwararrun likitoci, domin a duba marasa lafiyarsu, da su kansu masu lafiyar, domin tabbatar da tasu lafiyar. Na ƙara jadadda masu cewa abinci mai ƙyau kuwa yanzun ma aka fara ba su.

Sannan na ce masu za'a dinga fitar da su wajen wasanni, amma sai sun yi mini alƙawarin ba za su dinga guduwa ba,in kuma na same su da cika alƙawari,nima na yi masu alƙawarin wani abu, amma ba zan faɗeshi ba, sai idan lokacin ya yi. Bayan gama jawabina, na umarce su da su ja layi za'a raba masu wasu kayan da na zo dasu.

Tun bayan goma na safe nake cikin gidan yarin nan, amma ban fito ba sai ƙarfe uku na yamma. Ina isa gida kuwa sai wanka, ban fi minti sha biyar da fitowa ba sai ga jakadiya ta russuna ta yi gaisuwa, sannan ta ce Yarima na son ganina,na bata amsa da cewa in ya shirya gani, ina nan a gida zaune.

Ƙwana uku tsakani, amma ba Yarima ba dalilinsa, wannan ba ƙaramin tayar mini da hankali ya yi ba,shin wai haka za mu yi zaman auran? Tambayar da nake wa kaina kenan daga ƙwance cikin gadona, wanda tun da na yi sallar Asubahi nake cikinsa, har ƙarfe ɗaya na rana.

Kuka kawai nake yi daga ƙwancan nan, Mansura suka shigo na sanar masu cewa ba na jin daɗi, ƙarfe biyu saura ƙwata na rana sai ga Yarima ya shigo har ɗakina, ina ƙudundune cikin bargo, amma ba ƙudundunar rashin lafiya ba, duk baƙin ciki ne yasa na kasa tashi in yi komai.

Tsaye ya yi a bakin gadona, sai da ya É—an É—auki minti É—aya, sannan ya cire gilashin fuskarsa,ni kuwa ina kallon shi da idanuwana masu fitar da hawaye.

"Ni ban san ba ki da lafiya ba, sai yanzun, sannu da jikin naki." Ya É—an yi shiru.

"Da zaki daure ki É—an saka kayanki saboda zan turo miki likita yanzu."

"Ka barshi ma, na sha magani, zan samu sauƙi."

Ya janyo kujerar tebirin rubutu a gaban gado, ya zauna, ya kalleni ina kukana, amma bai iya yi mini magana ba.

Wannan zama kuwa ya É—auke shi har wajen awa É—aya, sai dai ya ce mini sannu sau É—aya kawai.

Bayan nan ya miƙe ya zo ya ɗan dafa goshina, wanda jijiyoyin kuka suka tashi a saman shi, ina kallo yasa ɗan ƙaramin hankici ya goge mini hawayena,amma fa ba tare da ya yi mini magana ba.

"Zan dawo anjima." Ita kawai ya faÉ—a ya juya ya tafi abinsa.

Haushi da takaici suka saukar mini a lokaci É—aya, tare da tunano masoyina Anwar na san da shi ne, da naga ruÉ—ewa a yau, amma shi ko a tsokar naman jikinsa ma.

Sallamar da aka yi ta kai uku, sannan na amsa na bayar da umarnin a shigo,a inda nake ƙwancen nan. Na ga Aunty Salwa ta shigo, ban san lokacin da na miƙe da ihu ba na duro daga gado na taryeta,sai dariya take yi ita kuwa, bayan mun zauna ne take yi mini ya jiki.

A inda ni kuma na tabbatar mata lafiya ta ƙalau,baƙin ciki ne ya yi mini yawa a zuciyata,amma yanzun tunda ta iso na warke, na ƙara gyara zama, na kalle ta sosai tare da riƙe hannuwanta, kafin bakina ya motsa har hawayen da ke cikin ƙwayar idanuwana sun gangaro a kumatuna.

"Aunty gaskiya ni ba zan iya wannan zaman ba,ki gayawa Dad, ya zo ya raba ni da wannan rayuwar ƙiri-ƙiri mutum ya ce baya sona,ni ma bana son shi, amma an tursasa mu, sai mun yi zaman dole."

Na ƙwashe labarin duk irin zaman da na yi na tsawon ƙwanaki ashirin da uku a gidan nan amma ba ruwansa da harkata.

"A'a ba ruwanki da harkarsa dai,ai shi ba laifi,yana daurewa yana kula ki,ke ce mai matsalar,ni ba ma ruwana da wannan, tsaya in dawo ga haƙƙinsa. Shin kin san ba abin da yake ci ko sha?" Na girgiza kai.

"Kin san a inda yake ƙwana,ma'ana a nan tsabtar muhallin shi?" Na kuma girgiza kaina.

"Kin taɓa shiga ɓangaren sa ki gaishe shi ya nuna miki baya so?"

"A'a, amma Aunty ai duk yana da masu yi masa."

"Ba ruwana da masu yi masa,ai ke dai haƙƙin ki zaki sauke."

"Ni wallahi Anti..."

"Ke wallahi da me? Haba Yasmin ya ki ke so iyayenmu suyi da ransu,so ki ke su kashe kansu a kanmu?"

"Aunty ki yi haƙuri abin ba na faɗa ba ne."

"In baƙya son faɗa, to ki tashi ki yi wanka ki shirya jikinki,muje ki raka ni wajen Yariman mu gaisa."

"Kai Aunty in je gidansa,ai Kamar na ma zubar da ajina ne, na dai aika a kirawo shi."

"Sannu mai makaranta, saboda ai yanda ki ka ɗauki kan ki ma naga alama ya wuce aji, sai dai makaranta kawai. Wallahi idan ba ki ɗauki kanki da sauƙi ba, zaki sha wahalar rayuwar duniya,su waɗannan mutanen babu abin da Allah bai basu ba, sannan ina ki ka taɓa jin auran gidan sarauta na rabuwa? Da wahalar gaske. Sai dai su auro wata su ƙara,kina kallo ya auro wata ya yi zamanshi lafiya da ita."

"Ni dai Aunty da zai sallame ni,ni ya auro huɗu ma a lokaci ɗaya, har ya haɗo da ƙwarƙwara ma."

Nan take na ga ta daddanna wayar da ke hannunta.

"Zan gayawa Daddy halin da ki ke ciki,in ya so shi sai ya san matakin É—auka."

Na yi saurin fizge wayar daga hannunta, na kashe.

"Aunty ke daga wasa."

"To tashi ki shirya." Dole ta sa na tashi gudun kada ran iyayena ya ɓaci a kaina.

Riga da zani ne na wani yadi three in one mai ƙyan gaske, ruwan madara ne da dishi-dishin ruwan ƙasa mai duhu a jikinsa,zanan ya sha ado, kamar dai yanda ake yayi ( Wrapper Skirt ) yanzu,takalman da na sa a ƙafata kuwa masu kamar silifas ne (Flat) ruwan madara ne, sai mayafi kawai da na yafa a kaina, ban wani tsaya neman ɗankwalinsu ba, na feshe jikina da turare, amma ba wata ƙwalliya a fuskata, saboda sanyi ma da ake da ko mai ba zan shafa ba.

Farar hoda kawai na gogawa fuskata, sai kuwa man leɓe da na sakawa laɓɓana. Jere muke da Aunty a inda na cewa su Mansura su jira in dawo. Muna isa ƙofar gidansa, mutane ne sun kai goma a zazzaune, suka yi saurin miƙewa suka kawo gaisuwa, muka amsa sannan muka wace ciki.

Mutane ne su huɗu zaune a ƙasa suna ta hirarsu,falo ne shi ma ƙaton gaske, wanda ba zan iya cewa ga abin da ya ƙunsa ba, saboda farkon shigowa ta kenan, mutanen nan suka kawo mana gaisuwa, waɗanda zan iya kiran su dogarawa. Bayan mun zauna da minti ɗaya sai nake ce musu su yi mana magana da Yarima.

*ƘASAITA BOOK 1*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 12

A take É—aya daga cikinsu ya ce ai ba a hawa idan har yana sama, sai dai ni ina iya hawa. Na nuna a barshi in ya sauko ma dawo. Amma Aunty ta ce sai na hau saman nan, kamar wacce zata hadu da abin tsoro, haka nake tattaka matattakalar benen, saboda na fahimci yanayin zubinsu É—aya da gidana.

Duk inda na duba baya nan, har sai da na kai ga ɗakinsa. A hankali na murɗa hannun ƙofar gudun kada ya ji ƙara, na tura ta cikin sanɗa, sannan na yi sallama, amma shiru ba wanda ya amsa mini,sai da na kai tsakiyar ɗakin manufata in isa barandar gidan inda na fahimci ya fi zama.

Kamar an ce in kalli gefen ɗakin, sai na ganshi ƙwance a ƙasa, ya yi rigingine yana bacci ba riga a jikinsa, sai dogon wando, na matso na tsugunna a hankali a gabanshi inda na ƙurawa halittar Allah idanuwa.

Ƙyau kam gashi nan a ƙwance, a take sai na ji dama Anwar ne na samu a ƙwance nan, amma matsala ɗaya ita ce hannuwanshi waje ɗaya ya yi filo da su, da gani kuma ka san abu ne wanda zai iya wahalar da shi.

Wai sai na tsinci kaina da son gyara masa, na miƙe zuwa gado na ɗauko filo, na iso na zauna dirshen, na zare hannuwansa a hankali, abin ka da gefe nake zaune, sai kawai na ga ya yi juyin da ya iso saman cinyata, ya sa hannuwa duk biyun ya zagaye ni.

Kenan ya koma rub da ciki,a zuciyata na ce Allah ya ƙara mini,cikin ƴar dabara na samu na zame jikina nasa masa fili,wai sai na ji ina son taɓa gashin kan shi inji kowanne iri ne, a hannuna na ji wani irin laushi,dama na san hakan za ta iya faruwa, saboda baƙin gashin ya yi yawa, sai dai ba shi da yawa.

Na miƙe a hankali na juya na tafi,a inda na samu Aunty na sanar da ita bacci yake yi,baccin kuma ya yi nisa, haka muka koma sashena muka ci gaba da hirarmu.
Chapter 14 · 0% Book details