← Book details Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 17

Sashe 13

Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na girgiza kaina alamar a'a, saboda mamaki da al'ajabi ya hana ni motsi, ashe ya iya magana mai sanyin gaske ko don bai cika yin magana ba.

"Yasmin!"

Na juyo sosai na kalle shi domin mamakin yanda aka yi yasan sunana, ya ɗan yi murmushin ƘASAITA, ya ƙara miƙo mini,na sa hannu zan karɓa, sai na ga yasa ɗayan hannunsa ya riƙe hannuna, ya kama ƴan yatsuna, sannan na ji ya yi magana.

"Daga yau don Allah kada ki ƙara shafa irin wannan fentin, ina son kisa a yanke miki faratan gaba ɗayansu,ni ba na so, Allah ma baya so."

Na zame hannuna, "Dole ne ki bi umurnina, saboda ina mijinki, ba ki da wata hanyar rabuwa da ni, tunda kin zo hannuna."

Na yatsina fuska. "Ka manta da ina da abin da zan iya tona maka asiri da shi?"

Ya yi murmushi, "Ai yanzun kan ki zaki tonawa asiri, tunda duniya za ta kira ni da mijin Yasmin ne ɗan iska mai bin mata. Amma duk da haka ina roƙon ki ƙonasu,bana so mu ɓata ran mahaifanmu."

Na yi murmushi na juyar da kaina gefe É—aya.

"Zan ƙona su, amma sai ka bi dokokina."

"Bama za ki same su ba,ki yi shiru kawai."

Bai yi wata magana ba, na ga ya koma ƙwana ya ƙara gyara ƙwanciyarsa.

Ni dai ƴar bi ce kawai, saboda ban san ko'ina ba a gidan, har muka iso wani falo. Wata ƙyakƙyawar mata ce kishingiɗe a saman wani tudu kamar na katifa, wanda ya sha shinfiɗun dardumai wanda kalolinsu ba sa ƙirguwa. Sai da muka isa kusa da matar, sannan na ga na ma taɓa ganin ta. Ƙasa na ga Yarima ya zauna cikin ladabi, nima sai na yi yanda ya yi.

Cikin ɗan lokaci ƙanƙani, na ga matan da ke zagaye da ita suna kawo mana gaisuwa,suna ficewa waje.

"Barka da yamma Mama."

"Barka ka dai yarona."

Nima sai na faÉ—i yadda ya ce, "Barka da yamma Mama."

"Ɗiyata barka da yau, ya baƙunta, ina fata baya ɓata miki rai?"

"A'a Mama, lafiya ƙalau."

Sai na ga ya tashi ya haye shinfiɗar ya zauna, ya fara wata magana irin ta shagwaɓa, mamaki ya kama ni,nan take na ce lallai iyaye, iyaye ne ashe da wanda Faysal ke wa magana lafiya ƙalau ba taƙama.

"Mama ni har yanzun Sarki ya hana ni zuwa Malesiya,Mama don Allah ki sa baki ya bar ni in tafi gobe."

"Ba fa zai yiwu ba,in dai ka tashi zuwa Honey Moon ne to na san ba zai hana ka ba."

"Mama don Allah." Ya ƙara matsawa kusa da ita har da riƙe mata hannu.

"Kana da naci Yarima a kan abin da ka san ba zai taɓa yiwuwa ba. Yanzun ka tashi ka je ku gaisa da Sarki naji an ce ya shigo, kuma na san saboda kai kawai ya shigo. Baby Yasmin ku je ku gaishe da Babanku, ga shi can ya shigo gida,ki ƙyale wannan shagwaɓaɓɓan mijin naki,kin gan shi nan kullum bai girma ji yake kamar a mayar da shi ciki ma."

"Mama, kada ta raina ni,ni bana yi mata wasa."

"A'a,lallai ni tashi ka wuce ka ba ni waje,marar kunya."

"Mama." Ya faÉ—a a daidai lokacin da shi kuma ya sauko muka tafi.

Tabbas sarauta sai ɗanta, Sarki kam yana mugun ƙaunar Faysal, saboda yanda ya nuna lokacin da muka shiga. Mun shiga Faysal ya sunkuya har ƙasa ya gaishe da Sarki,a inda ni ma na yi yanda na ga ya yi, sannan muka zauna gabansa.

"Faysal na ji aikenka har karo biyu, amma na bayar da amsa ɗaya, ita ce a'a, yanzun ma a gabanka na ce a'a, ba wai don in ɓata maka rai ba, a'a saboda yanzun ba da bane ba, yanzun kana da nauyin iyali a kanka, ya kamata a ce ka tsaya ka kula da su na tsawon lokaci kafin ka yi wata tafiya.

Faysal ban haɗa ku aure da sunan in zalunce ku ba,mu iyayenku mun haɗa ku aure ne, saboda muna ganin ku ƴaƴa ne nagari masu tarbiyya, hakan yasa ni nayi tunanin wacce ta dace da kai ta ɓangaren ko'ina rayuwar duniya nan, har izuwa lahira, na ga ba wacce ta dace sai wannan yarinya.

Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Ɓacin ranta zai iya shafar tsakaninmu da kai,ko da kuwa labari na samu,ka riƙe ta tsakaninka da Allah, shi so da ka ke gani, a hankali yake shiga cikin zuciya, har ya ratsa gangar jiki,in kuka yi haƙuri da juna, wata rana sai kun yi murna. Saboda mu ma duk haka aka yi mana,ga shi yanzun ya zame mana alheri."

Daga nan ya ci gaba da yi mana nasihohi, sannan ya sallame mu.

Muna fitowa daga ƙaton falon Sarki,Yarima ya yi gaba ya bar ni a baya,a zuciyata na ce ni dama cewa ka yi in tafi gidanmu,ni ya fiye mini alheri, tunda nima saboda mahaifina kawai nake zaune a gidanka.

Ina isa falon mahaifiyarsa na ga ban gansu ba, sai na nufi wata ƙofa nima in nemi inda suka shiga sai na jiyo muryar Yarima.

*ƘASAITA BOOK 1*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 11

"Mama wallahi yarinyar nan ba ta sona ƙwata-ƙwata, nima har yanzu ban ji ta ƙwanta mini ba sosai. Mama taƙama gareta ga jiji da kai."

"Kai ka fara yi mata,ka manta labarin da ka ba ni a baya cewa yi fa tana burge ka,tun ranar da ka fara ganinta."

"To Mama ai burgewa ba so bane ba."

"To yanzun me ka ke so inyi maka?"

"Mama ki yi mata faÉ—a, ita ma ta rage jiji da kai."

"Kai ka yi mata."

"Wallahi Mama tun da ki ka ce kada in yi mata wallahi ba na yi mata."

"Haba Faysal na san ka fa."

"Mama ko yanzun fa da zamu zo nan ni na je har É—akinta, sai da ma na jira ta tashi daga bacci. Mama ai kuwa na yi."

"Shin wai waya gaya maka rana ɗaya so ke shiga,a hankali in kuna tare zaka ji kana sonta, amma na gaya maka dole kai ne za ka yi ƙasa ka dinga lallashinta,ƙiyayyar mace ba ta da tsanani."

"Mama ni wallahi da an bar ni nayi tafiyata kawai."

"Bana son haukan nan naka fa,kullum ana koya maka hankali, amma ka ƙi ka koya." Jin kamar ta yi ɗan shiru yasa na yi saurin yin baya na samu ƙasa na zauna.

"Haba Yasmin!"

"Na ji an faÉ—a, na yi saurin É—aga kaina. Mama ce, "Nan fa ya zama gidanku,ki saki jikinki."

"Na yi murmushi, ta zo ta zauna kujerar kusa da ni, sannan ta kama hannuna ta sa mini awarwaraye da zobe.

"Na gode Yasmin,ki je kuyi ta haƙuri kin ji ko, balle ma na san za ki samu kulawa sai na kawo muku ziyara."

Nayi godiya, sannan muka yi sallama. Ai tunda muka shiga mota ban kalli inda ma yake zaune ba, saboda baƙin ciki,wai ni Yasmin ce yau ake tambulan da ni ga ɗa namijin da ba na ƙauna,wai har ba shi baki ake yi da lallashi a kaina dole ne in zo in tayi masa abin da zai ji haushi, har ya haƙura da ni,a raba auran don dole.

Safiya na yi na sa aka kira mini jakadiya,na tambaye ta wa ke tsaran gidan yari? Ta amsa mini da Sarkin tsaron gida, na ce ta sa a kira mini shi, shi da mai kula da basu abinci, wanda ta ce mini sunanshi Ma'aji.

Suna zuwa na umarce su da su shiga dafa abinci mai ƙyau kamar wanda suka san ana ci su dinga ba ƴan gidan yarin, kuma sau huɗu a rana. Da wadataccen ruwan sha, sabulun wanka,wanki,kayan sakawa, na tabbatar zan yi masu ƙyautar da ba su taɓa kawowa zuciyarsu ba, sannan tabbas zan iya kai masu ziyarar bazata,a duk lokacin da na so. A take na ce masu idan Yarima ya tambaya suna iya ce masa ni na saka su, na ɗaga filon ɗin da yake kusa da ni, na ɗauko bandir ɗin ƴan ɗari biyar guda huɗu na basu na ce su raba.

Na kawo guda shida na basu na ce a siyi duk abinda aka san babu. Nan Ma'aji ya tabbatar mini aƙwai komai, ya ba ni labarin irin kayan abincin da ke gidan nan,ya tabbatar mini za su iya ciyar da mutanen Jos da ƙauyukansu har na tsawon shekaru goma, mai ƙyau mai daɗi.

Bayan sati biyu ta cika ne,a daren ranar sai ga jakadiya da mace É—aya tana biye da bayanta,a inda ta tsugunna ta gaishe ni. Ni kuwa ina kishingiÉ—e saman kafet ina hutawa su Mansura na gefena, ana ta ba ni labarurrukan ban dariya da nishaÉ—antarwa.

Na ba ta iznin ta faÉ—i abin da ya kawo ta, shi ne ta ce Yarima ne ya turo ta tunasar mini na lokacin da na É—iba ya cika, ta ajiye mini farantin hannun matar nan É—aya,tana buÉ—ewa sai na ga manya-manyan kaji ne har guda uku, na É—an yi shiru na tsayin mintuna biyu, sannan na nisa.

"Ki koma ki sanar da shi cewa ni ma na san lokaci ya cika, amma ko a wancan lokacin na baya, cewa na yi ƙila, saboda haka ki mayar masa da waɗannan kaya ki ce na ji saƙon shi, amma idan ya samu dama ina son ganin shi yanzun, anjima, gobe,ko duk lokacin da ya samu damar zuwa,ki gaishe shi."

Ta ɗan ɗauki lokaci, sannan ta miƙe, shi ma kamar ba za ta tafi ba, na juyo na kalle ta.

"Shi kenan." Ta tafi tana kiran,"To, to,ai ba gardama."

Mun samu sama da awa uku muna hira ni da ƴan matan gidana,ganin sha ɗaya na dare ta yi yasa na sallame su,ni ma na nufi ɗakina, domin kayar da kafaɗata saman gado. Al'adata ce yin Sallar nafila kafin in ƙwanta bacci, sannan in kawo wutirina, wanda nake ƙin yi dama sai dare ya yi. Sam ban wani tsaya tunanin zuwan wani Yarima ba na haye gadona.
Chapter 13 · 0% Book details