Sashe 4
Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abin ka ga garin da ya tara yarurruka kala-kala, wannan yasa kusan yare ashirin suka yi raye-rayensu da waƙoƙin su, sannan aka koma wasan ƙwaiƙwayo, inda ƴan Legas suka yi nasu a kan zamantakewar auratayya da tarbiyyar yara.
Ƴan wasa kuwa shahararru ne, irin su Pate Odochi,Sam Loco,Ramsy Noah,Geneve Nneji,Liz Benson,Mama G. Gaskiya wasan ya yi ƙyau, dole ne ma fili ya ɗauki tafi,abin ka ga mutanen da ba su da Addini duk da ita ma Jos da sauƙin Addinin, amma yanda suka shirya shi ne kamar da gaske, shi ya burge ni. A nan take na ji ina son yin auren, saboda rayuwar da suka nuna.
Kamar an ce in ɗaga kaina, sai na hango wannan sakaran mutumin wanda ya kaɗe ni ya wani ƙwanta a kujera sai fizgar kai yake yi, kowa ya kewa, Oho. A zuciyata na ce yau ka faɗa, da Dad zan haɗa ka,kasha dukan tsiya.
Bayan fitarsu ne sai fili ya ɗan ruɗe kaɗan da hayaniya,in ɗan kalla sosai sai na ga ashe shahararrun ƴan wasan Hausa ne na jahar Kano waɗanda muke gani a cikin talabijin yau ga su a fili, kamar su Iyaye Alhaji Ibrahim Mandawari, Alhaji Hamisu Iyantama,Kabiru Na Ƙwango, Shehu Hassan Kano,Usaini Sule Ƙoƙi,Kabir Mai Kaba. Tare suke da ƴan fim ɗin su maza da mata. Sai iyayen fim din su mata na biye da su kamar su Hajara Usman salihar mace,Saratu Giɗaɗo macen da kowa ke so, Jamila Haruna kin fi kama da matar Gwamna da dai sauransu.
In na tsaya lissafawa ba zamu gama ba,sun yi wasan ƙwaiƙwayonsu a kan samu da rashi sannan da mutuwa da kuma ƙaunar iyaye da ƴaƴansu, wasan kuma ya sanyayar da zukatan mutane, wanda a take kowa ka kalla ya yi la'asar, tamkar yana jiran Mala'ikun mutuwa su iso kanshi.
Bayan nan kuma ɗaya bayan ɗaya aka dinga tashi ana magana da ƙoƙon fitar da sautin magana da ƙarfi (Microphone), iyaye,abokan arziƙi, shuwagabanni,a inda har wani shugaba a nan Jos ya baiwa ƴan wasan Kano ƙyauta ta motoci guda biyu, saboda yawon wasa da suke yi.
Wannan ne ya buɗe fili aka dinga yi musu ƙyaututtuka. A ƙarshe abokin ango ya fara faɗin halayyar abokinsa, ya kuranta shi, inda ni ma na tashi na yi, duk fa da harshen Turanci,dama su ni an iya turancin hanci (Slang) shi nayi a wajen. Ni kuma na san duk wanda ya ganni a tsaye ya ji turancina kuma ba zai taɓa ɗaukar ni bahausa ba ce ba, sai dai ƴar ƙasar tsallake.
Ango ya yi godiya, amarya ma haka, daga nan sai aka dinga rarraba abinci wanda duk ka ke so, sai ma an tambaye ka wanda nan kuma masu raba abincin Hotel É—in ne ke aikinsu (Waiters).
Ƙarfe biyu da rabi na dare aka tashi ba wai watsewa ba, saboda in na tashi ne ake samun damar gaisawa da jama'a na nesa da na kusa. A lokacin ɗakin taron da wajen ya baje da jama'a ana ta gaisawa tare da yin hira da su a gidan talabijin.
Da ƙyar na samu na je na gayawa Dad cewa na ga mutumin da ya kaɗe ni, kafin in waiga in nuna masa shi ya ɓace mini,wannan yasa na yi saurin jan ɗaya daga cikin ƙawayenmu na fita wajen Hotel ɗin, domin in samu damar ɗaukar lambar motarshi.
Cikin ɗan sauri-sauri muke tafiya, a inda na ci karo da wani, wanda har sai da muka haɗu da juna sosai, turaren da ke jikinsa kuwa, irin mai sanyaya zuciya ne, ina jin ƙarar faɗuwar jakata da wani abu a ƙasanmu, duk wannan bai fi cikin sakan uku ba, maimakon in kalli ko waye sai na duƙa don ɗauko masa wayar hannunsa, wacce ta faɗi tare da jakata.
Ɗagowa ta kuwa ta yi daidai da duƙawarsa ya ɗauko mini jakata yana ɗagowa ina shirin ba shi haƙuri, saboda a zatona ya yi tsaran iyayenmu, sai kawai haushi ya kama ni a take kamar yanda na lura al'ajabi ya kama shi mutumin da nake faman nema in nunawa Dad ɗina,shi ne muka yi karo da juna.
Na rasa me zan ce masa, na yi tsaye da wayarsa a hannuna, shi ma da jakata, ganin shi ba shi da niyyar yi mini magana, saboda tsananin girman kai, yasa nima na ƙi tanka masa, sai dai na fizge jakata da ke hannunsa ta ƙarfin tsiya, sannan na jefe shi da wayar da ke hannuna, ta faɗi ƙasa ta tarwatse.
Wannan ta yi daidai da tahowar wasu gungun shuwagabanni, za su wuce gamu mun tsare hanya,ƙawata Uwani ita ta janye ni cikin sauri sannan na ga ta sunkuya ƙasa tana tsince masa tarwatsatstsiyar wayarsa, wanda ta bi shi da sauri don ta bashi, saboda gungun mutanen sun yi gaba da shi.
Wai sai da na É—auki mintuna biyar a tsaye sannan na yi saurin tunowa da lambarshi fa zan É—auka ta mota. Na fita cikin zafin nama ina ta waige-waige, amma ko kalar mai rigar sa ban hango ba.
Na gaji da waigena har na juya zan koma ciki, sai na ji Uwani na ƙwala mini kira na yi saurin waigawa domin in gano inda take, saboda na ma san na gane mutumin nan, amma sai na ganta ita kaɗai, na yi saurin taryar ta, ina tambayarta.
"Ina yake, ina yake?"
Wai tambaya take wa? Na ce mata wanda ki ka kaiwa waya. Sannan ta nuna mini motar da yake ciki wacce ta kusan fita daga hotel É—in, ba kuma za a iya hangen lambar jikin motar ba, balle a É—auka.
Haushi ya kama ni na dinga yi mata faɗan masifa a taron nan,a haka har aka tashi wannan taro, ina cikin ɓacin ran rashin ɗaukar lambar motar nan.
Bayan mun je gida na sanar da Dad abin da ya faru,nan ya ce inyi ƙoƙarin ɗaukar masa lambar in na yi haka, to shi kenan in sa ido, na amsa masa tare da ƙudirin sai na ɗauke ta in Allah ya yarda, amma har muka gama biki ban ƙara ganin ko mai kama da shi ba. Wannan kuwa ba ƙaramin takura ni ya yi ba.
**** **** ****
Bayan ƙwanaki arba'in da huɗu da gama bikin Fatima da mijinta Ibrahim, wacce take da mahaifinta da Dad abokan wasa suke. Ni kuwa bayan bikin ban ƙara zuwa inda take ba, sai yau ranar Asabar saboda in samu Ibrahim a gida shi yasa na bari sai Asabar.
Cikin isa nake jan motata zuwa unguwar Ring Road,domin kai wa Fatima ziyara, daidai wajen bada hannu ne wajen unguwar Ahmad Bello way,na tsaya bai fi mintuna biyu da tsayawa ta ba ina jiran a ba ƴan layinmu hannu, sai kawai na ga ƙato ya buɗe murfin motata a gaba ya shigo, ina ƙoƙarin yi masa magana na ji buɗewar baya,waigawar da zan yi sai naga ƙarti uku zaune a cikinta, sun nuna mini bindiga, wanda na gaba ya ce mini.
"Kiyi shiru,ki ja mota kawai muke so!"
Ban tsaya gardama da su ba na mayar da hankalina ga tuƙina inda aka ba mu hannu.
"Titin hannun ki na dama za ki bi."
Haka ɗayan ya ce mini. Ni dai na san ba zan ɓata ba a garin nan sai dai in kashe ni za su yi, saboda haka ban razana ba.
Duk inda suka ce in nufa,nan nake bi da motata, har zuwa wani mahaukacin gida, wanda yake É—auke da yawan fitilu, duk da safe ne ba kunna su aka yi ba, amma ganin su a tsaye shi ya nuna mini yawansu.
Titin get ɗin gidan muka miƙe, tamkar za mu wani garin, bayan mun shiga get ɗin gidan waɗanda yake ɗauke da sojoji sun kai goma sha biyar,ni kuwa ganin sojojin ma ya ƙara mini ƙwarin giwar in sakin jikina ma, sai da muka dinga wuce gidaje zan ce ko gine-gine, sun kai baƙwai sannan suka ce in tsaya a ƙofar wani gida mai bene,wanda saman shi yake zagaye da barandar sama.
Da gani zagaye yake kamar ƙwano kenan circle ta can sama na hango ƙyallin wani mutum ta labule ya ɗan ɗago masu hannu, daga nan sai suka ce in yi gaba na ja mota muka nausa cikin wani daji, duk fa a cikin harabar wannan gine-gine. Bayan tafiya ta kai ta kilomita uku, sannan na ga mun iso wani gida mai dogon gini kamar ginin Choci.
Nan aka umarce ni da in tsaya in fito daga motar, ba wanda ya taɓa ni cikin su, suka nuna mini hanya har cikin gidan nan. Mun wuce wurare da dama, sannan na dinga ganin ragar ƙarfe da mutane a ciki, wannan ya nuna mini gidan yari ne aka kawo ni,abin da ban gane ba,shin ziyara aka kawo ni inyi ko kuwa ganin wani,ni dai na san ban yi laifin komai ba......
*ƘASAITA BOOK 1*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 4
Abin tausayi na gidan (Yarin) gidan maza, saboda duk sun bi sun rame, sun ƙare,ga su nan da ƙyar suke magana, masu ɗan ƙarfi ne ke miƙewa su zo su kama ƙarfen suna yi mana magana wadda bana ganewa.
Matattakalar bene muka haye ni da su, wanda nan naga mata birjik a É—aure a zuciyata na ce laifin me suka yi waÉ—annan bayin Allah, har da masu tsohon ciki da masu Æ´aÆ´a, ga su nan a kukkulle,ni dai Æ´ar kallo ce har aka kai wani É—aki na ga an buÉ—e shi wai in shiga,ban musu gardama ba muka shiga tare da su.
Gado ne ƙarami irin na ƴan makaranta amma wanda bashi da sama, sai ɗaya a kusa da shi da wata ƙwance tana bacci. Ba su yi mini magana ba ɗaya daga ciki ya buɗe wata ƙofa,nan na ga ashe banɗaki ne, ɗaya ya buɗe famfo a kusa da ni, na ga ruwa ya zo, duk dai ban yi magana ba.
Sai da na ga duk sun fita suna shirin kulle ni a ciki, sannan na yi masu magana da harshen Turanci.
"Baku gaya mini komai ba har za ku tafi."
ÆŠaya daga cikinsu ne ya ce, "ki zauna za a neme ki."
Ya juya ya tafi ban ce masu komai ba,nima na É—an kalli gidan nan na zauna.