Sashe 12
Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
In ka fita cikin gidan,za ka samu bene ne zagaye da shi kamar ƙwabo, sai filin tsakiyar,in ka fita ƙofar shigowa kuwa za ka samu ragowar rariyar gidan, waje kenan inda ke da lambu in ka dawo ta gaban gidan kuma doguwar baranda ce kamar ta asibiti, amma wannan yanayinta kamar ƙaton fayif ɗin ruwa.
Tun da zagaye take da shukokin fulawoyi,in kana ciki kamar kana cikin inuwa, ita za ta ɗauke ka har ka shiga gidan Faysal, wacce kamar nan naɗe take da wayoyi, sai dai akwai ƙofa biyu in ka zo tsakiyar ta.
Ɗaya ƙofar za ta fitar da kai filayen wasa na gidan, wanda gaba ɗayan zagayen gidan ciyawar nan ce ƙwantacciya mai kama da kafet ɗin ƙasa, filayen wasa ne kala-kala, akwai na ƙwallon ƙafa, ƙwallon raga, ƙwallon ƙwando, ƙwallon hannu,ƴar ƙwallon rami da sauran wasanni kala-kala.
Daga can nesa da wajen kuma wani dutse ne wanda ƙasanshi duk ƙananan duwatsu ne, ga ruwa mai ƙyau yana gudanya a ƙasansa, wanda za mu iya cewa wajen shaƙatawa, wajen ya yi mini daɗi da sanyi-sanyi. Ƙaton dutsen kuwa malale yake, tamkar an shinfiɗa a kai wanda sai ka taka kamar ƙananan duwatsu uku, sannan ka haye shi.
Ba zan iya cewa ga inda wannan ruwan ke nufa ba, saboda gabanshi duk daji ne,wato dogayen itatuwa ne, masu kama da iccen turare,ko ko iccen fulwaya za mu ce, shi kuwa ruwan kana hango ƙasanshi garai-garai, wanda ƙananan duwatsu ne ke aiki.
Muna isa wajen kuwa, na tattaka na haye saman dutsen nan,a nan take sai na ji ai ni na samu wajen zama in dinga hutawa, duk da an keɓe wajen hutawa a cikin wajen filin wasan. Ɗaya hanyar kuwa, ɓangaren lambu ne,babu abin da babu,a cikin wajen, wanda sai da muka zagaya shi sosai, sannan muka fita, shi ma a cikin shi akwai duwatsu, sannan an tanadi wata rumfar gargajiya a ciki, wacce ta sha shimfiɗu a inda daga nesa da ita akwai wani ɗan ƙaramin gida mai ƙyan gaske, sai dai sun ce gidan hutawar Yarima ne.
Saman dutsen nan mai ruwa shi ne ƙarshen zagayen gidana, tunda ni ba abin da zai kai ni gidan Yarima. A nan na umarce su da su ɗan kawo mini darduma,zan zauna a saman dutsen,dama ni ba gwanar ɗan ƙwali ba, sannan ga ni da son ƙananan kaya (English wears) duk da dama ƴan Jos haka muke,mun fi baiwa ƙananan kaya muhimmanci a kan kayan gargajiya.
Doguwar riga ce kuwa jikina, wacce take ɓalalliya daga ƙasa, ba ta wuce ƙwaurina ba, sai dai ƙaramin hannu gare ta, iya cinyar hannuna, na sa suka ɗebo mini ƴan ƙananan duwatsu don kawai in dinga jefawa a cikin ruwan.
Na samu tsayin awa ɗaya a wajen nan,ni da Mansura da Muslima, sai ga jakadiya cikin hanzari ta zube a can ƙasa, sannan ta nemi iznin hayowa, na bata,a inda ni kuma na kishingiɗa a ɗan tuntun da suka kawo mini.
*ƘASAITA BOOK 1*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 10
"Allah ya taimaki Gimbiya,Yarima ya ce a ce miki yau ƙarfe huɗu na yamma ki same shi gidanshi,za ku gaishe da Sarki, da mahaifiyar shi,dama haka al'adar take, domin su ga ya ku ka ƙwana."
Na yi shiru, sannan na nisa na fara magana.
"Ki ce masa ina da Æ´ar hidima a gidana, amma shi in ya shirya yazo ta gidana mu tafi in kuma ba damuwa ma iya haÉ—ewa a can, ina da Æ´ar rakiya." Sai na ga tana rausayar da kai.
"Shikenan jakadiya."
"To,to,to, Gimbiya ai ba gardama, abin da ki ka ce shine."
Ta miƙe ta gangara ta tafi,ni kuma na cigaba da harkokina, wanda suke yi mini daɗi, ga ba rana ko kaɗan a ganina sai ma iska da ke ratsa jikina, irin ta sanyin damuna.
Ƙarfe biyar na yamma na farka daga baccin da ya ƙwashe ni a kan abin sallah ta wanda na tashi da mamakin jikina ba hijabin da na saka na yi sallah, sannan an ɗora mini kaina a saman filo.
Cikin ɗan hanzari da faɗuwar gaba na miƙe, saboda tunawa da na yi cewa mun yi da Yarima za mu gidansu. Banɗaki na shige na watsa ruwa da saurina, ina fitowa ɗaure da tawul na leƙo ta barandar sama, ta cikin falo, na kira Mansura,wai dama in tambaye ta cewa Yarima ya aiko,ko ya zo? Ai sai kawai muka yi ido huɗu da shi.
Ya yi tsaye a maimakon in kira Mansura, ganin ya cire gilashin da ke manne a fuskarshi, ya ƙara ɗago idanuwanshi a kaina, ya tuna mini cewa jikina ba riga, na yi saurin shigewa cikin ɗakina, tare da ƙwallawa Mansura kira.
Ta shigo da sauri, "Ya daÉ—e da zuwa?" Tambayar da nayi mata kenan.
"Eh, ya daÉ—e."
"Tun yaushe ya zo?"
"Tun ƙarfe huɗu, na zo gaya miki sai na same ki kina bacci, shi ne na gaya masa,ni dai na ga ya hayo saman da kanshi, sai ya sauko ya zauna a nan,mun kawo masa kayan marmari da lemu, amma bai ko kalle su ba."
Na yi tsaki, "maimakon ki ce masa ya tafi zan zo daga baya?"
Na ga ta zaro idanuwa da sauri.
"Allah ya huci zuciya,ai ba a mayarwa da Yarima magana, yanzun ka ƙwana a yari." Nan take sai na tuno yarin nan,nima na taɓa zuwanta, ta tsawon awa goma.
"Ke ki ka cire mini hijabin jikina ki ka sa mini fulo a kaina?"
"A'a"
Haushi ya kama ni, "wa ya ce ki ka barshi ya shigar mini É—aki?"
Ta yi saurin sunkuyar dakai, ba ta ce komai ba, "fita ki bani waje ki turo mini masu kula da kayana!"
"Ai sun ajiye Gimbiya, Allah ya huci zuciya,ga su nan sun fito da su." Ta nuna saman kujera da É—an yatsa, sannan ta yi waje.
Boyal ne mai ruwan makuba (Coffee Color) wanda ya amsa sunansa, wanda ya sha aikin surfani a wuyansa da hannayensa, amma hannun bai wuce cinyar hannuwana ba, sai rigar kuwa da kaɗan ta wuce ƙuguna, amma buɗaɗɗiya ce, wacce ake kira da Stella Style.
Zanin kuwa ya sha ado, wanda zai É—aukewa jama'a hankali,ni kaina mai kayan sai da na ji sun birge ni, na zauna a jikin madubin da ke kusa da gadona, na gyare fuskata.
Takalmi da jaka ruwan ƙasa ne nasa a ƙafata, wacce jakar iya silin hannu kawai ake rataya ta, da gani ka san desginer ce,wata siririyar diamond na saka a wuyana,inda zobunan hannuwana da ɗan kunnan duk kalar sarƙarce, zobe ƙwaya biyu kacal ne a hannun nawa.
Ɗan ƙwalin Boyal ɗin ne aka naɗo shi, tamkar naɗin gwaggwaro, amma a matsayin ɗaurin ɗankwalin yake. Turaren (Network) na zuba a jikina, ban tsaya wani make-up ba a fuskata,saboda gaishe da sirikan dole zan je, sai dai na san dole ta sha farar hoda da Wetlips mai sheƙi,farcena kuwa sun sha fenti ruwan ƙasa suma.
Taku ɗaiɗai nake yi na sauko daga ƙafar bene inda takalmin ƙafata ke fitar da sauti cikin nutsuwa, saboda malalen kafet da ya baje gidan, shi ya hana su ƙara mai fitar da sauti da ƙarfi.
Babu kowa a falon sai Faysal shi kaÉ—ai da jarida a hannunsa,jin takuna yasa ya ajiye jaridar, amma ba tare da ya kalli inda nake ba, har sai da na iso daidai da shi, sannan na ga ya É—aga kai ta gefe É—aya ya kalleni,mayar da kan da ya yi ya sunkuyar ya yi daidai da fitar maganarshi a hankali.
"Something is missing."
Na ƙara kallon jikina sosai, ban ga abin da na manta ba.
"What?" Na faÉ—a cikin jan aji.
"Mayafi,ko kin manta yanzu ke matar aure ce?"
Na tsaya na ƙare masa kallo, amma shi ko motsi bai yi ba,a hankali na nufi inda na san zan ga su Mansura, sannan na yafito ta, ta iso da gudun saurinta, sannan na umarce ta da ta ɗauko mini mayafi wanda yake iri ɗaya da takalman da jakata, cikin rawar jiki ta ce to.
Ko kallon inda yake ban yi ba, na wuce zuwa waje abina,bai ce ƙala ba, shi ma na ga ya taso ya biyo bayana. Wani abun al'ajabin kuma shi ne dakarun tsaron shi suna nan tsaye ƙam suna jiran shi, a zuciyata na ce lallai wannan mutumin da mulkin masifa yake.
Limousine motar nan mai ƙofa uku, wacce ta bugeni a titin Ahmad Bello Waya, ita aka buɗe mini na shiga cikin takaicinta, ta gefe ɗaya na ga ya shigo shi ma,a inda bai fi sakan biyu da zama ba, na ga labulaye baƙaƙe sun sauka da kansu, kenan an rufe mu,ko direban ma bana gani.
Kujerar gefenmu ba kowa, sai tsakiyarta naga ƙaramar talabijin na aiki,sanyi na ji ya sauka a lokaci ɗaya, tare da wata fitila mai kalar duhuwa ita ma a zuciyata na ce lallai dole a dinga kaɗe ƴaƴan talakawa ba a sani ba.
Yanda ya shige ƙwanar kujerar da yake,ni ma haka na ƙwanta linkif a cikinta,tsawon mintuna goma sannan na ga ya cire gilashin fuskarsa da ƙyar, sai ga wani ɗan tebir ya ɓullo daga ƙasa da ƙwalaban lemu amma ba irinsu fanta ba,da kofunansu, wasu ƙwalaben ne abin kallo, don ma ina ƴar gidan masu da shi, da sai in ce giyoyi ne ba lemo ba.
Ya ɗora gilashinsa a sama, sannan yasa hannu ya janyo gaban tebirin, sai na ga ashe ɗan firji ne ya zaro robar Ice Cream da Chukulat, ya ajiye a gabana, sannan ya ɗaga ƙwalba ya tsiyaya lemo a kofi, ya ajiye a gabana, sai na ga shi ma ya tsiyaya.
Sai da ya kurɓa sau biyu, sannan ya ajiye ni kuwa sai bin shi nake da kallo ta wutsiyar idanuwana.
"Na aiko da gaisuwata ɗazu, amma ban ji gamsasshiyar amsa ba, wanda ke ce mace a ƙarƙashina ki ke,ke ya cancanci ki aika mini da ita,ko kizo ki gaishe ni." Ya yi shiru ya ƙara ɗaukar kofin ya kurɓa lemun.
"Ki sha mana,sarkin shan zaƙi."
Na ɗago na kalleshi a zuciyata na ce wa ya gaya masa ina son waɗannan kayayyakin, ban amsa masa ba sai naga ya ɗan sunkuyo kaɗan ya ɗauki Ice Cream ɗin ya buɗa ya miƙo mini.
"Karɓi."