← Book details Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 17

Sashe 11

Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗaya farantin kuma alƙur'ani ne da abin ɗora shi, ɗan katakon nan da dardumar sallah mai beza mai ƙyan gaske, da carbi da littafin ibada da hukunci ƙwaya ɗaya.

Farantin da Mansura ta É—auko mini kuwa, na sa hannu na É—auki kaza É—aya, na É—ora a saman shi, cokali mai yatsu É—aya, gefe É—aya na sa tufa biyu,lemo biyu,ayaba biyu, na É—auki dabino huÉ—u na zuba, na bayar da umarnin a É—auki yanki É—aya a rufe.

*ƘASAITA BOOK 1*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 9

Sannan na É—auki kaza É—aya na baiwa Æ´an kawowa, tare da bandir É—in kuÉ—i.

"Jakadiya ku je ku raba,ke da abokan rakiyar ki, waÉ—annan kuma na gaya miki ki kai masa,ki ce Gimbiya na gaishe shi baki ya siyu, amma tana hutawa har nan da sati biyu."

"Maganar ki ita za'a bi, godiya muke."

Na koma na ƙwanta jikin kujerar da nake zaune, ina kallonsu suka bi layi suka fita kamar yanda suka shigo, bayan nan kuma na umarci su Mansura da su ƙwashe kayan su ɗan ɗibar mini kayan marmarin,su ɗauki ragowar, haka kajin na ce su ɗauki ɗaya.

Cikin girmamawa da biyayya suka aikata yanda na faɗa, tun daga lokacin kuwa sai na koma sama,a inda na umarci su Mansura da su ɗauki daki ɗaya a ƙasa su ƙwanta,ni sai da safensu.

Baƙin ciki, takaici, suka saukar mini a daidai lokacin da na tuno da Anwar,na yi tunanin da shi na aura,muna can ya shigo ɗaki a sunanshi na ango, ina can yana tarairayata da nuna mini kulawa ɗari bisa ɗari, wannan tunanin yasa na sha kayan baccina, na buɗe ƙofar da za ta fitar da kai barandar da take a gaban gidan.

Na dafa ƙarfen barandar, wanda na mayar da idanuwana na lumshe,a daidai lokacin da wani ni'imtacciyar iska ta kaɗa, iska ta dinga ɗaukar gashin kaina tana juya shi a hankali, hawaye masu sanyi suka tsiyayo mini a kumatuna, a lokacin da tunanin rayuwata ta raunana ya faɗo mini,anya kuwa zan amince in dinga irin wannan zaman jakadancin? Komai ke tsakaninka da mijinka sai wata ta sani.

Na buɗe idanuwana tare da ware hannayena tamkar ina jiran wani ya rungume ni, kamar an ce in kalli barandar sama wacce take kallon tawa barandar,sai kawai na hango mutum a tsaye, shi ma ya dafa ƙarfen barandar ya sunkuyo yana kallona.

Da ɗan nisa, shi ya hana ni in gane ko waye, kuma ga iska tana kaɗawa, natsuwa na yi sosai na ƙura masa ido, ba abin da idanuwana suka karanta mini sai angona Faysal.

Tsanarshi na ji ta ƙaru a zuciyata a take ban san lokacin da na juya na shige cikin ɗakina ba, na mayar da ƙofa na kulle, na wuce na faɗa gadona a inda na kasa tunano komai sai Dad wanda da ya san rayuwar da ya jefa ni ciki, na san da bai fara ba.

Ni ce har ƙarfe biyun dare zaune a abin sallah ta, ina roƙon Allah ya kawo mini canjin rayuwar da ta fi alheri a gareni,ni kam na san ba zan iya wannan auran ba, na yi tunanin wai yau ne daren farko (first night) ɗina,amma gani nan a zaune ko kalar ango ma ban gani ba.

Ƙarfe shida na safe na farka, hakan yasa na yi saurin saukowa daga gadona, domin gabatar da sallar Asubahi ɗin da na makara ban samu yi ba. Ƙarfe tara na safe har na gama komai na sauka ƙasa domin nemawa cikina abin da zan ci.

Wani abin mamaki da na gani, shi ne yanda har an gama gyara ko'ina na falon, sai ƙamshi ke tashi, sannan kuma gaba ɗayan gayyar ƴan matan nan sun hallara waje ɗaya ni kawai ake jiran fitowata. Tausayinsu ya kama ni,a zuciyata na ce bayin Allah, insha Allahu sai na raba ku da wannan ƙangin na bauta,a take na ji ina ƙaunarsu, sannan ya zama dole ma in ɗan saki jikina da su, saboda su ji daɗi su ma.

A take na yi murmushin dariya, "A'a Mansura har kun tashi?"

Cikin sakan ɗaya har sun gama isowa bakin matattakalar benan da nake saukowa sun zube ƙasa.

"Haba, abokaina, ya zaku dinga yi mini haka, tamkar wata wacce ku ke bautawa, na san dole ne ku ba ni girma, amma irin wanda nima zan ji daÉ—inshi ba irin wannan ba.

Sai na ga wannan ya kalli waccan, waccan ta kalli Æ´ar uwarta, na sauko na dinga dafa kafaÉ—ar na kusa da ni.

"Ku zo muje." Suka biyo bayana. Ina zama gaba ɗaya suka zube ƙasa.

"Gimbiya mun gaishe ki. Barka da ƙwana?"

Na amsa masu da lafiya ƙalau. A nan na dinga tambayarsu sunayensu, ɗaya bayan ɗaya, wani abun in yi ƙoƙarin ba su dariya, amma bayin Allah nan sai na ga sun kasa yin dariya, ga ta kuma suna son yi. Na waiga na kalli Mansura.

"Mansura, har yanzu ban fahimci waÉ—anda ke kicin ba."

"Allah ya ja da ran Gimbiya ga mu nan."

A take na ga ƴan mata masu ƙyau suma.

"Yaya abinci?"

"An gama shirya shi a wajen cin abinci, na Yarima fa?"

"Ai can ake haÉ—a masa shi ma."

"Su wa ke haÉ—a masa?"

"Yana da masu yi masa."

*Maza ko mata?"

"Maza ne."

Na taɓe baki, sannan na miƙe na bada umurnin a kai ni wajen cin abincin. Kai wata duniyar ma in ka shige ta, sai ka ga tamkar yau aka haife ka, saboda ganin sabon yanayi da sabon tsari.

Duk a cikin falon muke, amma da muka bi ta wata hanyar sai na ga tamkar mun fita ƙasashen turawa, wani ɗan rukuni ne mai kama da ɗan ƙaramin wajen shaƙatawa an saka masa wasu labulaye masu kama da rumen kitso, da ka buɗa sai ka ji sun yi kankacakau, madadin tebirin cin abinci da muka baro a falo.

Sai na samu shi kuma wajen shafe yake da kafet, mai ƙyan gaske ga wani tsakiya mai zagayewa, sannan na ga an shinfiɗa wani yanki mai ƙyan gaske,fari mai zanen jajayen fulawoyi, shi ma zagayayye ne,saman shi aka jera kayan abincin,ga tuntayen alfarma guda uku gefunansa.

Ina zama jakadiya na isowa, ta zube gabana ta kai gaisuwa.

"Allah ya ja da ran kilishin Gimbiyoyi jakadiya na yi miki barka da Asuba."

Na yi murmushi, "Gimbiya na amsawa jakadiya,kin ƙwana lafiya?" Sai na ga tana sussunne kai.

"Jakadiya ba a amsa mini."

"Lafiya lau, Kilishin Gimbiyoyi."

"Dama Yarima ne, ya aiko ni ya ce a gaya miki yana jiran gaisuwarki, sannan yana gayyatarki karya kumallon safiyar nan,zuwana na huÉ—u kenan a lokacin dai baki fito ba."

"Ki gaya masa ina amsawa, amma ki ce kin same ni har na Zauna saman in da zan karya nawa kumallon,sai dai ya jira wata safiyar sai ya ƙara aikowa."

"An gaishe ki." Ta miƙe da hanzari ta yi gaba,ni kuwa na buɗe kayan cin abincina, amma a cikin sauri ƴan matan nan masu girki suka karɓe ni. Farfesun naman kai ne da sinasir a gefe ɗaya, sai soyayyan dankali mai ƙwai a ciki, ga kunun gyaɗa a gefe ɗaya, ban da ruwan shayi da yake a gefe, da cinyoyin kaji zalla an soya su.

Bayan na gama ne na umarci su Mansura su zo su raka ni in zagaye gidan, har waje saboda sanin yanda yake duk da ƙwanana biyar kenan a gidan, amma a tare nake da jama'a ƴan biki.

Samana dai falo ne babban gaske, wanda ya sha kujerun alfarma har kala biyu, kowanne rukuni,kalar kujerun su daban, amma irin na gidan sarauta, sai ɗakuna ƙwaya biyu kacal, wani gado ne ƙwaya ɗaya a tsakiyar ɗakin zagayayye mai kama da ƙwano (Circle), ƙaton gaske,an zagaye shi da wasu labulaye farare, wanda sai dare ya yi ake danna wata na'ura wato remote sannan sai ya sauko.

Gaba ɗayansa shinfiɗe yake da zanin gadon da ya bazu ƙasan shi, wanda kafet mai laushin gaske ne ƙasan shi, shi ma a zagaye yake, sai daga can gefensa kujeru ne masu zagaye aka yi masu rukuninsu daban, har ɗan tebirin tsakiyarsu (Centre table), sai daga kusurwa tebirin rubutu ne har da kujerunsa biyu.

Daga ɗan nesa da gadon kuma kujerar kushin ce doguwa, ƙwaya ɗaya, wacce ta sha shinfiɗar dardumar sarauta da filillikan ta biyu. Gefe ɗaya kuwa wani irin kafet ne, amma ba wai irin wanda ni kaina na sani ba, tabbas wannan ya fi kafet ɗin tsakiya laushin gaske.

Bangon gidan kuwa ɗaukar ido kawai yake yi, wanda na yi imani da Allah ba tayal ba ne ba saboda yanda yake ɗaukar ido. Ɗaya ɗakin kuwa, shi ma an zuba masa wani irin gado, wanda kan shi kawai ma abin kallo ne, sai kujeru ƙwaya uku da ke gefe, sai kuwa rukunin tebir ɗin kayan Na'ura mai ƙwaƙwalwa (Computer).

Banɗakin ɗakunan kuwa shi ma wani sabon gida ne, saboda shiga ka ke yi ƙwamin wanka tamkar ka shiga ramin wanka (Swimming pool) saboda ƙasa ya shafe, kuma sam ba ka ganin mai ke ƙasan ƙwamin ne,ko kuwa irin abin da ke manne a bangon gidan ne? Oho, sai dai zaka ga yana ta gudu, tamkar ka shiga ƙorama.

Sannan an rubuta zafi da sanyi a jikin wani bango da yake tsaye shi kaɗai a can tsakiyar kusa da ramin wanka, shi kan shi ramin wankan ka tattaka matattakalar bene,amma shi sai mu ce kamar za ka gidan ƙasa, sannan ka shiga ciki.

Wasu green da blue ɗin abubuwa ne liƙe da ɗan dandamalin inda za ka ajiye hannuwanka in ka shiga, wanda aka rubuta sabulu da soso, ma'ana su za ka danna su fito da kansu,in ka gama ma su koma da kansu.

Ƙaton madubi ne wanda za mu iya cewa ya kai rabin bangon banɗakin, shi ne ke kallon ka in ka shiga, da in ka fito. Tsayawa ƙarasa bayanin ma na san abu ne mai ɗaukar lokaci.

Da ka buɗe ƙofar da ke cikin ɗakin,za ka ga gaban gidan, wanda yake kallon gaban wani gida wanda na ga Faysal tsaye jiya da daddare,da ka gangaro matattakalar benen,sai ƙaton falo, wanda zan iya cewa tsayawa fassara shi ɓata lokaci ne, sai dai aƙwai ɗakuna biyu shi ma a ƙasan da banɗakinsu.
Chapter 11 · 0% Book details