← Book details Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 17

Sashe 17

Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Na wayi gari da safe, ranar cikon kwanaki taƙwas, wanda ya zamo daran jiya muna tare da Yarima har ƙarfe ɗaya na dare,wai dole sai na tayashi hira,a irin zaman da muke yi ne a falo talabijin na ta aikin yin hidimominta, wanda hasken da ke fitowa ta jikinta shi ne kawai hasken falon saman da muke zaune.

Cikin mintuna biyar hankalinmu ya koma ga wani fim da suke yi wanda yaro da yarinyar fim ɗin suke zaune suna hirarsu, kamar dai mu sai naga yaron ya miƙe ya iso inda take zaune ya tsugunna daga nan ya yi mata wata magana wacce ta ƙunshi aure.

"Za ki aure ni, Please." Sai na ga yarinyar ta ɗaga kanta tare da riƙe hannunsa ta tashi tsaye da sauri. Abin ka ga marasa kunya sai suka kama tsotsan bakin juna, ta wutsiyar ido na ga Yarima ya ƙura mini ido.

Ɗan minti ɗayan nan da na yi ina kallon Yarima ta wutsiyar ido, sai kawai na ji takun kiɗan talabijin ɗin ya canja kallon farko ban ƙara maimaitawa ba, na miƙe jikina na rawa ko sallama babu na sauko da saurina, sai gidana. Ina isa gadona na faɗa sai kuka. Anwar na dinga kira da ƙarfi, saboda shi ne mutumin da yake ƙwance a zuciyata.

Ko da wasa ban yi zaton Yarima zai biyo bayana ba, asali ma ban ji ya shigo ɗakina ba, sai dai jin an zauna gefen gadona na ji anyi, na ɗago da sauri,dama fitilar gefen gadona ƙwaya ɗaya ita ke kunne,ido muka haɗa da shi.

"Wa ye Anwar Yasmin? Ina ƙoƙarin in ga na mallaki zuciyarki da gangar jikinki gaba ki ɗaya, ashe duk ban sani ba da wanda zuciyarki ke ƙauna, na yi da na sani a yanzun da nine na fara sakar miki jikina, saboda samun ƙwanciyar hankalin junanmu."

Ya miƙe tsaye yasa hannuwansa a aljihun wandonshi, wanda dama T.shirt ce a jikinsa, tsayuwar da ya yi zata kai ta mintuna taƙwas, sannan ya juya ya tafi. Tabbas ban ji daɗi ba, ban kuma so a ce yajini ina ambaton sunan masoyina ba.

_To masu karatu sai mun hadu a littafi na biyu, wanda tare suka fito._

_Taku har kullum: Maryam Kabir Mashi_
Chapter 17 · 0% Book details