← Book details Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 17

Sashe 7

Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarfe taƙwas saura minti huɗu,Mamee ta shigo ta ce in je inji Dad.

Na É—ago kaina, na kalle ta kawai, na mayar.

"Ba ki ji ni bane?"

"Na ji Mamee yanzun zan je."

Tana fita,nima na bi bayanta. Bayan kamar minti biyar.

Yana kishingiɗe a inda ya saba hutawa, duk bayan sallar isha'i, Mamee na daga ƙafarshi zaune tana yi masa matsar yatsun ƙafa.

"Yauwa,autar Daddy zo nan."

Na isa na zauna ƙasa ɗan nesa da shi.

Ya É—aure fuska, irin alamar in babba zai yi maka maganar da yake ganin so yake yaro ya É—auke ta da muhimmanci na gaskiya, sannan ya kira sunana.

"Yasmin." Sai na ga Mamee ta tashi ta fita, sannan ya ci gaba.

"Yasmin,kin san kowanne uba yana son ya ga ƴaƴanshi sun fi na kowa ɗaukaka,ƙyau, asali, tarbiyya, miji nagari, idan mata ne,in maza ne mata nagari. To balle ku ƴaƴana da ku ke a zuciyata tun ranar da na haife ku har izuwa yau. Ku kanku kun san ba wanda nake so a duniya in har suka wuce iyayena sai kuwa ku da mahaifiyarku, kamar yanda nake ƙaunar Manzon Allah (S.A.W) haka na koya muku sonshi da ƙaunarsa,a matsayinku na ƴaƴana, na horar da ku tarbiyyar bautawa Allah da bin sunnar Manzon Allah (S.A.W).

Kamar yanda ku ka san ba wanda zai ba ka ladan bautar Allah,sai shi Allah, haka ba ɗan da ya isa ya biya iyayenshi ladan tarbiyya da haihuwarshi da suka yi sai shi Allah, amma ana son a yi masu biyayya, ga duk abin da aka ga suna so da wanda suka umarta idan dai har an tabbatar bai saɓawa shari'ar Muslunci ba, da abin da Manzon Allah (S.A.W), ya zo mana da shi.

Ko da kuwa sun zama suna masu tsanar abin da suka umarce su, da ƙiyayya mai tsanani to yin biyayya ga abin da suka faɗa ɗin nan, shi zai sa su sadu da rahamar Ubangiji, wata rana kuma su ƙaunaci abin,su yi wa iyayen godiya ta musamman da addu'a idan sun riga sun rasu.

Yasmin,kin san dai duk cikin ku ukun nan,ba wacce nake ƙauna da so, sai ke. Ke ce ƴar da take ƙwance a cikin zuciyata a koda yaushe,ke ce ƴar da nake ganin nan gaba za ki ƙaunace ni, ki kula da rayuwata.

Ki tuna na haife ki, nayi miki tarbiyya tagari, na baki ilmi, na wadata ki da abinci mai ƙyau, na kawo gida mai ƙyau na gina na saka ku,ya na same su, wacce wahala na yi? Oho,ni dai ku ji daɗi,yau rana ta zo ta ki nuna mini ɗaya daga cikin son da ki ke yi mini,ki nuna mini iri-irin biyayyar da zaki iya yi mini ko da bayan raina ne.

Ki sani Addini ya yarjewa iyaye su zaɓawa ƴaƴansu mazaje na gari, idan har ƴan mata ne, ko samari, amma in sun zama aure ne na biyu, bazawara,ko bazawari, shari'ah ta ce a bashi dama ya zaɓa, ba wai don ba zai iya zaɓa da farko ba, a'a saboda Allah kaɗai ya san hikimar da yake nufi a nan.

Yasmin yau na zauna a ƙasanki ina roƙonki wata alfarma ƙwaya ɗaya, amma girmanta ya fi ƙarfin Najeriya gaba ɗayanta, nauyinta kuwa ya fi ƙarfin teku, amma a gare ki in kin yi,abu ne mai sauƙi da rashin nauyi.......

*ƘASAITA BOOK 1*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 6

Kada kiyi tunanin na yi miki haka ne don in cutawa rayuwarki,a'a na yi ne domin ina ganin na isa a gare ki, kuma na san ke yarinya ce mai biyayya, mai ƙaunata, na yi ne domin in sakaki jin daɗi da annashuwa a nan gaba, ranar da hankali ya huda miki jiki.

Ke kin san dai yanzu nafi ƙarfin a kalleni ace zan je ƙwaɗayin wani abin duniya,ko zan kai ƴaƴana domin ƙwaɗayin wani samu na duniya ke kanki kin san nafi ƙarfin haka, sannan kin san na mallaki abin da zan iya ciyar da ku har ƙarshen rayuwarmu,ko na riga ku mutuwa, zan yi alfahari da cewa na bar muku abin da za ku tafiyar da rayuwarku har ku bini inda na tafi.

Yasmin na san kina son Anwar,na san zakiyi farin ciki yau a ce shi zan aura miki a matsayin miji a gareki, amma ki sani yawancin abin da ka fi so,in har ba ka same shi ba, to ba alheri ba ne a gareka, ta yiwu alherin na ga wanda ba ka son nan.

Yasmin ni mahaifinki nake son baki haƙuri a kan hana ki auran wanda ki ke so Anwar,Ina neman alfarma a gareki da ki yi mini biyayya zan haɗa ki aure da ɗan Sarki Jafar,ki yi haƙuri na san da takurawa. Yasmin ki taimaka ki fitar da ni kunya, sannan ki sani,ni ba irin iyayen da suke kai tallan ƴaƴansu ba ne ba, na fi ƙarfin haka nan.

Ko kuwa kuna da yawa a gabana, balle ku biyu ne, da kansu suka zo har gidan nan neman wannan alfarmar, ban sani ba, sai yau, ban taɓa jin labari ba, sai dai ganin su nayi sun zo, ban san abin da ke tafe da su ba, sai da suka faɗa,ban san wanda ya ba su labarin ina da ɗiya ba, sai da suka faɗa cewa wajen taron bikin gidan Alhaji Kabir suka ganki.

Shi ne Sarkin yasa aka dinga cigiyar ke Æ´ar gidan waye, ba su samu ba sai wannan satin, shi ne Sarkin ya zo da kansa wai gudun kada in ga da wasa ake yi. Ban san ko waye ba a cikin Æ´aÆ´ansa ba, sai dai ya ce zai turo shi cikin satin nan ya zo ku gaisa,ku daidaita kafin nan da lokacin bikin. Wannan da ki ke gani shine Sarkin nan garin na musulmi."

Gabana ya faÉ—i shi kenan gidan cin mutane ma za'a kai ni, saboda waÉ—annan mutane na gidan yarin in ba cin su ake ba,ai ya isa a sake su su koma gidajensu, da gani ma sai an shanye jininsu, sannan a cinye tsokar a yanda na ga sun bushe a tsaye.

Nan take na yi dana sanin kin gayawa Daddy abin da Yarima ya yi mini wata uku da suka wuce, da na sani wata É—aya da wani abu da ya wuce da ban É—auki fansa da kaina ba, da na faÉ—a an É—aukar mini,na san da yanzu Dad ba zai yarda ya aurawa wani É—an gidan ba ni ba.

Shi yasa aka ce ta yaro ƙyau take, amma ba ta ƙarko, ga shi dai ni yanzu ba damar in faɗa Daddy ya ga kamar zan tozarta shi ne a idon duniya.

"Yasmin na ji kin yi shiru."

"Dad ai na san ba zaka zaɓa mini abin da ka san zai cutar da ni ba, saboda haka na amince da zaɓinka matsawar in ka amince da in naga abin cutarwa zan zo in sanar da kai, kuma zakayi saurin ɗaukar matakin gaggawa a gareni,ka ba ni gudummawar ka ta uba."

"Na yi miki wannan alƙawari, sannan ni ma kin tunasar da ni zan faɗa masu da wuri tun kafin akai ki, na gode Allah ya yi miki albarka, ya baki ke ma ƴaƴan da za su yi biyayya a gareki,ki yi haƙuri na san na takura miki."

Na ce, "Ba komai." Na miƙe na koma cikin gida.

**** **** ****

Shi kenan,Rayuwata ta raunana, tun daga ranar da Daddy ya gaya mini maganar aurena, har zuwa yau,ƙwanaki tara kenan, ba ni da wata walwala,in ma naɗan yi ta, to gabansu iyayena ne,gudun kada su yi wani tunani na daban.

Amma ni a ɗakina,ko motsin kirki ma bana son yi saboda tsananin tunani da kuma rabuwa da masoyina Anwar,wanda muka rabu muna kuka ga junanmu. Ƙwanaki huɗu da suka wuce, amma har yanzu ɗin nan sai da ya bugo mini waya, kullum kuwa riƙe nake da kan wayata ina kallon hotanshi wanda shi ne (Screen Saver) ɗin wayata,hoton fuskar wayata.

Na kasa fita ko ina yawon da na saba, balle in isa gidan Aunty in gaya mata halin da nake ciki,ko gidan Fatima amarya da na yi niyyar buga musu waya kuwa, sai in ga matsalar tafi ƙarfin faɗa a waya.

Ƙarfe huɗu da rabi ina zaune a kan abin sallah ta, sai na ji ƙwanƙwasawar ƙofa, da ƙyar na ce a shigo. Yaya Habib, na yi tsalle na ruga na rungume shi, ina yi masa oyoyo, madadin mu koma ƙasa, sai na janyo shi cikin ɗakina na mayar da makulli na kulle ƙofata.

"Yaya zauna tambayoyi zan yi maka,dama ina neman ka, saboda ina cikin tashin hankali, amma kada ka gayawa su Mamee, ba na nunawa a gabansu."

"To ina jin ki."

Nayi saurin tsugunnawa a gabanshi, shi kuwa yana saman gado zaune.

"Yaya su Mamee kuwa su suka haifeni ko riƙona suke yi?"

"Kina da hankali kuwa, da tambayar taki kenan ta mahaukata?"

"Yaya don Allah ka da ka juya mini baya, kai dai ka amsa mini,zan gaya maka dalili."

"Eh,su suka haife ki."

"Kana da wayo sosai a lokacin da Mamee ta haife ni ina jaririya,kana ganin tana ba ni nono a gabanka?"

"Wai ke yau ko kin yi gamo da aljanu ne?"

"Wallahi Yaya da hankalina,kai dai ka amsa mini don Allah."

"Zan iya tuna lokacin da take shayar da ke, har ma nake cewa ki sam mini nono in sha, ana yi mini dariya, har in je in kai ƙararsu ga Daddinmu."

"Kuma ka ga suna so na?"

Ya miƙe tsaye, "bana son sakarcin banza, zan yi miki duka yanzun nan."

"Don Allah Yaya ka yi haƙuri."

Sai nasa kuka.

"Wai Yaya wai É—an Sarki Jafar za'a aura mini,ban san ko waye ba a cikin Æ´aÆ´an nasa, shi ma Dad wai ya amsa shi zan aura,ni kuma bana son shi, koma waye a cikin su, duk azzalumai ne fa."

Na saka kuka na miƙe na cakume shi.ina ji ya saukar da ajiyar zuciya, ya ɗago kaina.

"Haba Yasmin ƴar ƙanwata,ki yi tunanin irin son da Dad yake nuna miki yanzun haka in za ki buɗe zuciyar Dad shima baya so, Amma,zan je in tabbatar da me yake faruwa."

"Kada ka gaya masa cewa na ce bana so."

"Ba zan faɗa ba,kin ji ƙanwata."

Ya goge mini hawayen fuskata,sannan ya juya ya fita.
Chapter 7 · 0% Book details