← Book details Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 17

Sashe 2

Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shigowa ta fara faɗa, "wallahi My Dear,kai ke ƙara shagwaɓa yarinyar nan, shi yasa kullum take ganin ta kamar ƙaramar yarinya, ta ƙi tsayawa ma ta ƙwantar da hankalinta ta fito da miji a yi mata aure ma mu huta, ina dalilin sakarci irin wannan? Wallahi na kusan gajiya zan haɗa kanki in auna da ke Syria in huta,ko bakina ma ya gajarce."

"Dad kaga Mamee ko bata so na, yanzu da Aunty ce dakaga sun shige É—aki sun koro ni waje, amma ni kullum ta dinga yi mini faÉ—a."

"Ki yi aure ki gani in na ƙara yi miki haka."

"Dad..."

"Ke sorry ƙyale ta,ban ma san wanda ya kira ta ba, fita My Dear kada in taso miki nan."

"Allah ya huci zuciyarka duk dai son da ake mata,ni dai wajena ba shi da amfani, tunda an ƙi yi mata aure shekara ashirin da uku. Ni kuwa tawa ɗiyar tun da sha taƙwas nayi mata auranta."

"Fita na ce ko!" Ya faÉ—a har da É—an tashi daga kishingiÉ—ar da ya yi.

"Na yi shiru sorry."

"Nayi nima, dawo nan to ki zauna." Ya nuna kusa da shi kaÉ—an ta taso ta zauna, sannan ya ce, "Okey, talk my daughter."

*Dad,dama da na fita ne wani ya bankeni da mota."

"What?" Ya faÉ—a har da tashi zaune.

"Wa ye shi?"

"Nima ban san shi ba na faÉ—i kuma wai sai yasa wasu za su dake ni."

"How is that senseless man?" Ya tashi zaune sosai.

"Okey, tell me."

"Dad,kuma ya ja motarshi ya yi tafiyarsa,wai don raini ma har da jifa na da kuÉ—i. Dad ko magana fa ba ya yi, da kai da hannu yake ba su duka (Instruction)."

"To waye ubanshi a garin nan?"

"Oho,ni dai na ji mutanen da suka zagaye ni bayan ya tafi suna cewa wai ko ɗan waye ma, oho,fa don haushi ban tsaya tambayarsu ba. Dad da ƙyar fa yake motsi,ƙwance yake a bayan mota."

"Zaki iya gane shi in kin ganshi yanzu?"

"Eh Dad."

"To duk lokacin da ki ka ganshi ki É—auko mini lambar motarsa da sunanshi kawai ma sun isa, zan haÉ—a shi da hukuma tunda haka sukeyi wa mutane sakarci a gari."

"Haba My Dear, ya za ka biyewa zancen yara ka je kaji kunya."

"A'a zan sa a koya masa hankali, ba wai don ya taɓa ƴata ba, illa saboda nan gaba, tunda da gani haka suke yi wa mutane,don suna taƙama da iyayensu na da kuɗi."

"Wallahi Daddy da gaske ne,ka ga ma kayana yanda suka koma,ƙafata ma sai ciwo take yi."

"To anji Allah ya bada sauƙi, tashi ki je ki sha (Panadol) fanadol.)"

"Dad ka ga Mamee ko?"

"Ke ƙyaleta,je ki abin ki ke dai ki yi mini aikin da na saka ki kinji ko?"

Na ce, "To." Na tashi na tafi.

Ina isa falo na samu Katung a tsaye. Katung mutum ne mai ban dariya, ga iya bin hanyoyin da zai saka ka cikin farin ciki,ko da ranka a ɓace yake. Ai kuwa nan ya dinga bin hanyoyin shi da ya saba, har sai da ya saka ni dariya a dole. A nan ne har ya samu damar tambayata, na ƙwashe duk abin da ya faru na gaya masa.

A nan ya ce in har na gane ko waye, to shima fa zai bayar da gudummawarsa, ya ɗan ba ni ƙwarin gwiwa, sannan ya miƙo mini kayana,har da makullin motata, waɗanda na manta da su ƙwata-ƙwata, sannan na haye ɗakina, na jefa kayana saman gado na wuce banɗaki kawai, saboda in shiga ɗan ruwan ɗumi ko naji ɗan daɗin jikina.

**** **** ****

Plateau State,wacce jama'a suka fi kira da suna Jos. Jos gari ne wanda Allah ya yi masa ni'imar sanyi da duwatsu kala-kala, ga wajen ƙwanciyar ruwa yana dashi. In kayi la'akari da Jos,za kaga yanayinta ya fi kama da ƴan ƙasashen tsallake (Abroad), ire-iren wannan ne ya sa garin kullum tamkar ana damina.

In kuwa lokacin sanyi ya zo,....

*ƘASAITA BOOK 1*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 2

In kuwa lokacin sanyi ya zo, sai ka ga har ƙananan dusar ƙanƙara ke zuba wasu lokutan (Snow), amma saboda sabo wannan duk baya hana mutanen garin yawonsu da hidimomin su. Wannan kuma yasa yawancin Turawa da sauran ƴan ƙasashen duniya ke zama a Jos. Asali ma ƴan garuruwa da ƴan ƙasashe daban-daban sun fi yawa a garin.

Sai dai mutanen garin Jos, yawancinsu sun fi baiwa (English wears) mahimmanci, ƙananan kayan turawa. Wannan dalili ne ma yasa ko a tarihin Jos, shi ne garin da aka fara kawo kayan gwanjo daga ƙasashen duniya, shi yasa har yau kuwa ita ce kasuwar duniyar Gwanjo ga wuraren da shagunan siyar da sababbin kayan turawa (Boutiques) sun yi yawa.

Jos gari ne wanda ya saba da jama'a kala-kala, wasu in ka samu tarihinsu sun daɗe sosai a garin, wasu ma ba su san asalin inda garin iyayensu da kakanninsu yake ba. Wannan dalilin ma ya haddasa samun harshen yare da dama a garin, wanda a iya ɗan ƙiyastawa za a iya samun harshen yare ya kai kusan ɗari biyu a garin, wannan yasa suka ɗauki Hausa Central Language ɗinsu. Sai dai sun ɗan fi amincewa da Turanci,ko da kuwa irin turancin da aka fi sanin ƴan Legas ko kuma mutanen Ibo,wato (Broken English).

Yanzu haka sana'o'in masu kuɗin ba su wuce shigo da motoci, da kayan sawar turawa da Gwanjo, amma za a ga masu kuɗinsu na yawo da ƴar ƙaramar sanda mai lankwasashen masa. Ni kam garin na burge ni, saboda wuraren shaƙatawarsa, amma fa sunayen Hausawansu duk irin sunayenmu ne. Wannan kuma bai hana su yin karatun zamani ba, wato makarantun boko, ga shi akwai Islamiyoyi a garin, kamar yanda aƙwai wajen bautar yawancin wasu yare Choci.

Mahaifina kuwa ɗan asalin ƙasar Najeriya ne,a jahar Adamawa, wacce take kusa da jahar Taraba. Suna wani ƙauye wai shi Gembo. Iyayenshi duk ƴan asalin can ne, amma duk Allah ya yi musu rasuwa, tun yana ɗan yaro,a hannun Yayan Babansa ya girma. Mahaifinmu bai yi karatun boko ba, a lokacin da yana garin Gembo.

Saboda a lokacin ba a waye sosai da karatun ba. Asali ma abin da ya hanashi karatun mariƙinshi talaka ne sosai, sai dai sun yi karatun allo, wanda har sun yi sauka. An taɓa yi masa aure a ƙauyen Gembo wanda dalilin auran ne suka yanke shawara shi da abokanshi su fita neman kuɗi.

A lokacin yana shekara sha takwas kaɗai. Sun fara tsayawa Kano tsawon shekara ɗaya,a inda ya fara sana'ar siyar da rake a ƴar kura (baro), shi ma ta haya ce ɗaya daga cikin abokansa,ko in ce abokin wasanshi, saboda ɗan mace da ɗan namiji suke, shi ne ya kama sana'ar Gwanjo a kasuwar Ƙofar Wambai.

Tun yana tsaro ana biyanshi, har ya fara ɗan sarar nasa yana yawo da su a hannu, ganin yana samu yasa ya janyo hankalin mahaifina da ya daina sana'ar rake ya koma ta Gwanjo, da ƙyar ya amince.

Ganin sun ɗan bunƙasa kaɗan yasa suka yanke hukuncin zuwa Jos su dinga sarowa. Zuwansu uku,ana huɗu ya yi shawara da yayan Babanshi ya amince suka koma Jos da zama, shi da kanshi bai san ya bar matarsa da ciki ba,sai dai haihuwa aka aiko masa.

Saboda ya ce mana sukan yi wata baƙwai,taƙwas ba su je gida ba. A ranar da ya isa gida, a daren matarshi mai suna Huraira ta rasu, lokacin ƙwananta uku da haihuwa,ana gobe sunan yarinyar da ta samu, ita ma ta ce ga garinku nan.

Shi ne tun da ya baro Gembo bayan an gama makoki da sati uku, daga shekara sai shekara yake komawa garin, domin gaishe da wan Babanshi Alhaji Tsalha. Har yau kuwa yana nan da rai, sai dai ya tsufa.

Ikon Allah yasa suka shiga makarantar yaƙi da jahilci,su wai don saboda su iya maganar ciniki da yaran garin,a haka kuwa suka yi fice wajen iya komai, aka sa su, suka zama zakaru a ajin.

Wannan yasa aka tura su Sakandire ta garin da suka gama, aka dinga bin su da aiki. A lokacin neman masu karatun ake ba kamar yanzu ba. Cikin ikon Allah Daddy na har digiri ya yi inda ya haÉ—u da mahaifiyata kenan ita ma tana digiri É—in ta a kan Education, shekararta ta farko.

Shi kuwa yana shekarar ƙarshe ta kammala digiri ɗinsa,a lokacin yana ɗan shekara talatin da biyar kenan. A shekara sha ɗaya ya je Jos, ya yi shekara ɗaya ashirin kenan, suka yi yaƙi da jahilci shekara biyu, Sakandire shekara shida, shekara biyu sharar fagen shiga jami'a, Diploma kenan, sai haɗa digiri shekara uku, sai kuma kammalawa da bautar ƙasa ya ɗauke shi shekara biyu.

Tunda Allah ya haɗa Momeena da Dad ɗina, Mahaifinta ya nema masa aiki a ma'aikatar (NNPC) ta Jos, ya kama masu wajen zama. Mameena gidan Dad ta kammala karatunta na digiri, da tana aiki a ma'aikatar Ilimi (Ministry of Education), amma daga baya Dad ya hana, saboda maza da suka dame ta. A hankali har Allah yasa komai nasa ya bunƙasa, amma har yanzu sana'ar shigo da kayan Gwanjo tana nan Dad na yin ta,irin tasu ta manya-manyan ƴan kasuwa.

Saboda yanzun haka, ba ya aikin gwamnati, sai dai siyar da motoci da harkar Gwanjo da ta safarar kayayyaki ƙasashen duniya. Amininsa abokinsa ɗan uwansa, wanda suka fara harkar tare shi ne Alhaji Kabir babansu Aminiyata ƴar uwata Fatima Kabir.

Mahaiyata Mamee, wacce sunanta na gaskiya Sharifat,iyayenta Æ´an asalin Syria ne,mahaifinta ne yazo aikin wakilcin Syria a Nijeriya (Ambassador) ya zo da su Mamee suna Æ´an mata,a inda Mamee ta gama makarantar gaba da Secondary a Najeriya ta fara karatun digiri É—in ta a jami'ar Jos.

Mahaifin Mamee ya zo Najeriya tun shekara ta 1973, a lokacin mulkin Gen.Gawon, a inda ya ji daɗin zaman Najeriya, ya yanke hukuncin zama a cikinta,a lokacin da ya kammala aikinshi. Su Mamee su biyu ne a wajen iyayen su, ita da ƙaninta Saifullah.
Chapter 2 · 0% Book details