← Book details Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 17

Sashe 10

Kasaita Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ƙyar mata suka ɓanbare ni daga jikinsa. Ganin yanda nake yi ne yasa Daddy ya ce su tafi, zai kai ni da kanshi daga baya. Hakan yasa sai dai aka lulluɓa wata abokiyar wasata aka fita da ita a matsayin amarya.

Ni kuwa har goma da rabi na dare,Daddy nata lallashina da ƙyar na amince, shi ma sai da ya yi mini alƙawarin gobe tun da safe zai je gidan,in ya ga ban haƙura ba zai dawo da ni, kai ni kaina na san dai wayo kawai ya yi mini.

Duk da na san dai shi kanshi dole ta sa zai rabu da ni,kari da ganin hankalin Dad ya yi mugun tashi har yana zubar da hawaye ganin yanda nake kuka, har da neman shiÉ—ewa.

Da lallashi da ban magana,Daddy ya kaini har gidan Faysal, shi da kanshi ya rakani har cikin ɗakin da yake nawa bayan nan ma sai da ya ɗan zauna ya ƙara yi mini ƴan maganganun da za su ƙwantar mini da hankali, wanda sai da jama'a suka ɗan ba mu fili, saboda yawa, amma duk da haka da zai tafi sai da na ji hankalina ya yi mugun tashi.

Abu ɗaya ya hana in bi shi, ƴan'uwa da ƙawayena da sauran waɗanda suka isa a kaina, kamar ƙannan Dad da na Mamee,da suka riƙe ni suna lallashi, dole dai ta sa na haƙura. A wannan rana sai da aka bar mini mutane daga gidanmu suka ƙwana, har da ƙawayena,ganin Aunty Salwa ta ƙwana,shi ma ya ƙara taimaka mini.

Sabuwar hidima ce ta ɓalle da gari ya waye,taro a cikin ariyar (area) gidan Sarki tamkar yau aka fara bikin, tun daga get kuwa har izuwa cikin gidana, wani sabon biki ma ni zan ce ake yi. Yamma na yi kuwa, sai hawan Daba ya tashi ranar Litinin kenan.

A al'adarsu,wai amarya da ango ke fitowa saman gidan Sarki, Sarki da tawagarsa a gefe É—aya, ango da amarya a gefe É—aya a sama. To sai a dinga kawo gaisuwa, dole ta sa na shirya, saboda Aunty na nan, ban da sauran dangin iyayena,Æ´an Syria,kuwa suna can wajen Mamee suna taya ta zama.

Sai da muka kai gaisuwa wajen Sarki, sannan muka wuce ni da Yarima muka zauna, baya ga ƴan bi baya da muka samu, tun daga fitowata, kafin ma in iso inda Yarima ke jira na,a nan zaune har sai da aka yi kiran Magriba, tsakani da Allah na ga girmamawa da ƙauna a wajen jama'a. Wannan tasa ma na saki jikina.

Ranar Talata kuma amarya da ango ke zuwa gidan Sarki na cikin gari, amma iyakacinmu fadarshi aka gabatar da mu ga manya-manyan hakiman Sarki.

Daga nan kuma sai zuwa gaishe da iyayensa, shi Sarkin wanda dangin amarya ne ke raka ta, kuɗi,ƙyaututtuka kuwa,wai na sha su,ni kaina na sake da irin ƙaunar da ake nunawa Faysal, na san kuwa iyayenshi suka fara nuna masa ita.

Ranar Laraba,a ranar ango ke yin tashi walimar da abokanansa, saboda gabatar da amaryarsa a gare su, ita ma ta san su, sannan da ƴan ƙawayenta ko su goma ne,a wani babban wajen taro na manya. Iyakaci na da Faysal wajen hidimar auranmu, da mun iso gida, kowa hanyarshi yake nufa,dama kuma ba mota ɗaya muke shiga ba,ni da motocina, shi ma da nasa.

Ranar Alhamis ita ce ranar da na ga kowa na tafiya, wasu da safe, wasu kuwa sai yamma, amma ni ƴan'uwana, sai da dare suka tafi, cikinsu kuwa har da Aunty da Fatima amarya, zan ma iya cewa su ne na ƙarshen tafiya, wajen taƙwas da rabi na dare, saboda sai da suka gyara gidan duk inda aka ɓata,turaran wuta da sauran kimtsa amarya da ake yi kafin ango ya shigo ɗaki, shi da abokanansa, wanda ake kiranshi siyan baki, sai da suka sa na sake wani wankan na sake kaya, sannan suka umarce ni da in sauka ƙasa,in zauna ga wata kujera ta nan ita ɗaya, idan sun tafi.

HuÉ—uba, ba wacce ban sha ba a wajen Aunty,daga nan muka yi sallama suka tafi, da sunan ba zata dawo da wuri ba, saboda gidan sarauta ba a yi masa zirga-zirga,ganin na narke zan yi mata kuka ta ce wai jibi za ta dawo,ni dai na san tsarani kawai ta yi.

Na sauko daga sama a daidai lokacin da agogon bango ya buga ƙarfe tara na dare, na shigo falo na yi tsaye a inda nake tunanin an bar ni ni kaɗai kamar mayya, na tuna irin jama'a da suka taru a gidan nan,yau gashi rana ɗaya kamar an ƙwashe su.

Na samu ƙwanar kujerar kishingiɗa na ƙwanta gefe, ita kaɗai ta sha shimfiɗun sarauta,ƙasan ta ma zagayayyan kafet ne (Circle) mai taushin gaske, da gani ka san ita ce kujerar zama idan mulki ya taso. A hankali na dinga bin ɗakin shaƙatawar da kallo, ba inda idona ya kai, sai ga ƙaton hoton Faysal wanda zan iya cewa ya fi ƙarfin taga, sai dai ƙofar mutan da.

**** **** ****

Ban ce ƙala ba, har ta gama, ina kallonta suka jera layi ita da ragowar ƴan matanta suka yi waje sai guda biyun nan su ne suka yi saurin dawowa gefena suka zauna a ƙasa, na yi murmushi na juyar da kaina gefe, sai na ji hawaye sun gangaro mini,saboda tunanin tausayawa yara ƙanana da aka jera mini su,ni ina aure su suna bauta, Allah ya kiyaye.

Na ɗan motsa na tashi zaune, amma na ɗan kishingiɗa, cikin sauri duk suka miƙe tsaye ɗaya ta ɗauki ƙafata ta gyara mata mazauni, na kalle su, ba laifi duk suna da ƙyawunsu.

"Ku zauna na gode."

Suka yi saurin zama, na kalle su.

"Ya sunayenku?"

Ɗayar ƴar wacce ta fi ƙyan ta ce mini, "Mansura." Ɗayar kuma Musulum.

"A wane gari ku ke?"

"Nan gidan Sarki."

"Na sani,iyayenku nake cewa."

"Can cikin gidan Sarki, babban gidan kenan."

Nayi shiru, ina tunanin me suke nufi da haka, ban kammala tunani ba, sai na ji sallama, na juyo a hankali na kalli masu shigowa. Jakadiya Dela ce da wasu mata biyar ɗauke da wasu abubuwa a rufe suna biye da bayanta, tana zuwa kusa da ni, ta ƙara zubewa a ƙasa,su kuwa suka matso gaban kujerar suka ajiye kayan, suka ja da baya, suka zube ƙasa, sannan suka ce.

"Gaisuwa muke, gaisuwa muke."

Na É—ago masu hannu.

"Gimbiya ta amsa." Na ji jakadiya ta ce.

"Gimbiya ayi mana afuwa,muna damun ki da zirga-zirga."

"Ba komai."

"Abin da ki ka ce ba ƙarya." Inji ɗaya daga cikin matan da suka shigo tare da jakadiya. Ta miƙe tsaye ta iso gaban abubuwan da suka shigo da su, sannan ta tsugunna.

"Allah ya ja da ran Gimbiya wannan saƙo ne daga Yarima, ya ce in kawo gaisuwa a gare ki."

Na miƙe zaune, inda su Mansura suka miƙe da sauri za su kama ni, na yi saurin ɗaga masu hannu, ina zama sosai, sai na ga jakadiya ta fara buɗe kayan ɗaya bayan ɗaya.

Faranti ne ɗan dogo, mai ruwan zuma (golden color) kayan marmari ne a ciki,lemon zai kai goma,ayaba nono ɗaya, sai tuffa (apple) da dabino a tsakiya, amma fa na alfarma, dole ne ma su ba ka sha'awa, saboda ƙyawunsu, daga saman dabinon wani ɗan faranti ne shi ma mai zagayewa.

A warwaraye ne cikinshi, tsakiyarsu da sauran kaya rakwacam, na sunkuyo na ɗauki ɗan farantin na ɗaga awarwarayen (ƴan hannu) sai na ga su shida ne, da sarƙa ƙatuwar gaske, zobuna huɗu da ɗan kunnayensu na zinare ne ƴan Dubai ɗin asalin (Daham).

Na miƙawa Mansura ta yi saurin karɓa ta ɗora a kai, sannan aka buɗe ɗayan,Faranti ne shi ma kamar tsayin na farko, sai dai shi kalar ruwan silba (Silver colour) kayan sawa ne a ciki, amma da gani na bacci ne, da faranti ƙaramin sama.

"Mansura miƙo mini." Na faɗa.

Awarwaraye ne ƙwaya huɗu da sarƙa da ɗan kunne, da zobuna biyu kacal, amma Diamond,sun bala'in burge ni, ta dinga ɗagawa,sama rigunan bacci ne a ƙwalinsu guda bakwai, kala-kala, sai tawul ƙasa da silifas, amma masu ƙyan gaske, dukkansu a ƙwalaye suke irin ƙwalayen ƙasashen tsallake,su kansu ƙwalayen abin kallo ne.

Na miƙa mata ɗan farantin hannuna ta karɓa, sannan aka buɗe ɗayan duk fa kalar faranti kalar ɗan yankin da ke rufe da shi, leshi na gani na faɗa, da takalmansa,jakarshi,mayafinshi,a samansu aƙwatina ne masu ƙyau guda huɗu sai ɗan ƙarami a sama.

Aka miƙo mini ɗan akwatin na buɗa, ɗan zobe ne, mai ƙyau na Diamond da ɗan ƙaramin zanen abin sarauta a jikinsa, ya yi mini ƙyau sosai, na ajiye shi gefe, aka dinga miƙo mini ƴan aƙwatinan duk turarurruka ne a cikinsu desginer na miƙa musu, sannan aka buɗe na cikon na huɗun,kaji ne gasassu har guda huɗu masu rai da lafiya,ko a ido ka gansu sai ka yaba.

Sai ƙamshi ke tashi sai sheƙi suke yi, da wuƙaƙe biyu ƙanana a gefe ɗaya,ɗayan gefen kuma cokula masu yatsu ne (Knife and fork) nayi murmushi na koma sosai na jingina.

"Gimbiya Allah ya ja da rai, waÉ—annan kayan siyen baki ne inji Yarima." Sannan ta buÉ—a na biyar É—in bandiran kuÉ—i ne Æ´an É—ari biyar biyar sun kai guda goma.

"Allah ya ja da ran Gimbiya idan har baki ya siyo wannan leshin Gimbiya zata saka, sai mu tafi tare can gidan shi Yarima ɗin, tare da dukkan farantan nan, saboda ko za'a buƙata a can."

Na miƙe tsaye, a daidai lokacin da jakadiya ta gama tata maganar cikin ƘASAITA na haye matattakalar bene zuwa ɗaki inda na ce su Musulum su zo.

Na basu umarnin da su ɗauki kayan da ke saman gadona su ma lulluɓe da fararan yanki, ina isowa falo, sai da naga na daidaita wajen zamana, sannan na ce da jakadiya.

"Ga waɗannan ki kai masa,ki faɗa masa baki ya siyu, amma Gimbiya hutawa take yi sai nan ƙila da sati biyu."

Na umarci Mansura da ta ɗauko mini faranti a kicin,ta miƙe da sauri. Faranti ɗaya kayan sawa ne, riga da wando da babbar riga, waɗanda aka ɗinko su daga ƙasar Sinigal,aƙwalinsu, sai dogayen riguna guda huɗu, sai gajerun wanduna huɗu, duk a ƙwalayensu da silifas, da turarurruka huɗu da tuwal ɗaya a samansu ne ke da zobe ƙwaya ɗaya na azurfa.
Chapter 10 · 0% Book details