← Book details Karuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 24

Sashe 6

Karuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dagudu baby tazo ta rungume yazid.. Yarinyace mai kimanin shekaru sha biyar kyakykyawa da i'ta.."oyoyo yayana.. time din dakazo ina toilet ya yazid, ina aunty aunty zahra?. "
Lakace mata hanci yayi ...wato ke bazaki girmaba ko baby ?, gankifa katuwa kinkusa kaini...gashi sai lukuta kike zama."
Turo baki tayi tana d'an buga k'afa don batason yace mata lukuta.
"Nikam yaa yazid banaso wllh."
"To dai yanzu jiki dauko kayanki kizo mutafi gidana...."
Ai dagudu tatafi daukowa kayanta tana ihun murna.
Girgizakak momi kawai tayi...
Harbakin mota momi tarakasu , baby tana daga mata hannu harsuka fita daga get din.

*👄BieBie Luv👄*
[3/11, 12:39 PM] 👄BIEBIE Lurv👄: *💝KARUWA CE💝.....23/24*

_Writing by_
*👄BieBie Iuv👄*

_Editing by_
*💅Sadnaf💅*

💝💝💝💝💝💝💝💝

*S*aida yabiya restaurant yasai masu abun breakfast sannan suka wuce gida.
Ko parking yazid bai gama ba baby tafito da gudu tai cikin gidan tana kwalama zahra kira...girgiza kai kwai yazid ya girgiza yana mamakin shirme irin na baby gashi i'ta bawani karamar yarinya irin yan 10years dinnan ba amma shirmen ta yayi yawa..back sit yabud'e yad'ebo ledodin abinci ya shiga ciki.
Kai tsaye yatura kafar dakin ya shiga fuska adan sake, daidai tafito daga wanka tana d'aure da towel . kallo daya yay mata yad'auke kansa tareda ajiye ledodi biyu yana kokarin fita.
"Yaa yazid ina kwana." Tagaida shi muryanta a matukar sanyaye. Juyowa yay yakalleta sai yaga tadan fada kadan amna hasketa yakaru tai mishi kyau sosea . dauke idon sa daga kanta yayi ya amsa bayabo ba fallasa yana tambayar jiki..."dasauki." Tafad'a a takaice tana karasawa gaban mirror shima fita yayi yatafi dakin sa don yin shirin fita office.

"Aunty baki ganni bane?."
Juyowa zahra tayi tana kallon inda ake maganar sai yanzu taga baby don duk da bata lura da i'ta ba.
Ta bararraje saman gado sai washe baki take.
"Laaa baby yaushe kikazo." Zahra tafada tana karasowa bakin gadon fuskarta dauke da murmushi.
"Yan zunnan yaa yazid yakawoni, gidan mu yaje wai bakida lpy inzo irinka taya ki aiki, kuma gashi aunty kin rame mai yake damunki ?ko kinada cikine ? Don yanzu ana auren mutum sai ace wai yanada ciki kamar jira ake ...ko uban wa ke musu cikin oho."
Tsananin dariya yahana zahra cewa komai sai darawa take, don rabon datayi dariya hakama harta manta.
"Kai baby wllh shirmenki nada yawan gaske...waye daga auren nasa akace miki yanada ciki?."
"Yoo gaba aunty rukayyan mu ba aurenta wata daya akace batada lpy anazuwa asibiti wai ciki...tunda agida bataiba sai lokacin....Allah dai yakyauta."
I'tade zahra mamaki kawai baby kebata, ga mutum har mutum amma shirmenta yayi yawa."to dai bara inshirya muyi break sai muje mudan rage wani aikin."
"To aunty."
Bayan sunyi breakfast suka shiga gyaran gidan , cikin dan karamin lokaci suka gama gida yay kwal sai zuba kamshi yake.

Suna zaune falo sai hira suke don baby yar magana ce ko baka i'ya surutu ba inaka zauna da baby saika koya..
cikin shirinsa nafita office yafito, yana sanye cikin black suit da bakin cover shoe yaratayo briefcase dinshi bakaramin kyau yayi imaging farin mutum da bakaken kaya..
"Laa yaa yazid dama baka fitaba ?, ai nadauka katafi ."
"Aa sai yanzu."
"To Allah ya kiyaye...yaa yazid dan Allah katafo min da ice cream da gashashshen kaza."
"To sarkin kwadayi... Kawo kudin."
"Please man yaa yazid." Ta lankwabar da kai..
"To naji."
Har yakai bakin kofa yaji muryan zahra tana mishi adawo lpy..ciki ciki ya amsa yafice abunsa.

*****
A bangaren zubaida kuwa kullu sai abinda ke karuwa a harkar *karuwancin ta* kullu a hanyar hotel ana fakewa da sunan zuwa school..
Yau suna tareda dan iskanta *Arman* a meram hotel sai zuba shaaninsu suke..duk zubaida ta gigice don arman ba bayaba gurin sarrafa mace.
Bayan sun gama har cikin gidansu suka shiga, bayan sun gaisa da mominta (don arman dan gidan aminiyar momyn zubaida ne).
"Momy nashiga school dinsu ne sai muka hadu to lokacin tagama lecture shine nakowa ta."
"A yayi kyau gaskiya , ya maman naka dasu Fauziyya?."
"Duk suna lpy Momy."
"To madalla."

Mikewa yayi daga kan kujeran yace "to Momy ni zan wuce."
"Har zaka wuce arman." "Eh wllh inadan saurine akwai inda zanje ne."
"To bari inkira maka i'ta kuyi sallama."
"Aa wllh Momy bakomai zan wuce sai anjuma."
"To kagaida gida."

Fitowarta daga wanka kenan bakomai jikinta tsirara wayarta tafara ringing, dasauri tai picking ganin sunan yazid takara a kunne tana lumshe ido.
Aziyan zuciya yasauke jin zazzak'ar muryanta da yayi...
"Nikam nayi fushi ya yazid duk yau baka nemeniba sai yanzu...tafad'a cikin shakwaba hartana dan buga kafa.
Gaba daya tafara sauyama yazid darasi , harwani mika yake daga kwancen dayake.
" am sorry my zuby ..wllh aikine yay man yawa...amma kinsan me?."
"Aa saika fada." Tafada tana d'an turo baki.
"To kikwantar da hankalinki gobe zanzo gidanku don goge lefina....."
"Dagaske ya yazid?."
"Eh man."
"To Allah yakaimu zan fadawa momy na."
"To bakomai..bari sai anjuma zamuyi waya yanzu inadan aikine ."
"To sai anjuma."
Yazid yana kashe wayar zubaida tadaka wani wawan tsalle ..."yesss yazid zaizo gidan mu daga nan kuma...hmmmm..ka kusa shigowa hannu...

****sai magrib yazid yakoma gida saka makon aiki dayayi mishi yawa.
Bakowa falon sai karar AC n dake kunne , direct yawuce dakinsa yay wanka yatafi masallaci , bai dawo ba 9. Parking a dining yayi still baiji motsin kowaba saida yagama cika cikinsa sanna yashiga dakin zahra.

Tana dukunkune cikin bargo idonta a lumshe amma ba bacci takeba . baby nazaune gabanta tazuba mata ido kamar tana kallon TV kaganta kwanin tausayi.
Karasawa bakin gadon yayi ya tsaya yana kallon su duka....
"Baby!."
Dasauri ta dago tana kallonshi , saikuma tafashe da kuka... "Wllh ya yazid aunty zahra batada lpy sosea, don amai taringa yi kaganta kwanin tausayi wllh tun abincin break bakomai cikin ta..."
Gaba d'aya takaicin baby yacika yazid
"To naji, ya i'sa. Kiyimin shiru."

Yaye bargon yayi tareda tallabo ta jikinshi..."jeki hadomin tea baby."
Dasauri tatashi tafita...ba'ad'au lokaciba tawado dak'in hanunta d'auke da karamin try da cup akai. Saida shayin yad'an huce yazid yashiga bata ..kad'an tasha tafara yunkurin amai, kyaleta yayi yabata magani yakwantar ta kana ya lullub'a mata bargo .
"Nikam yaa yazid ba ciki ne da i'taba tunda sai amai take?."
Harara yawatsa ma baby yafita bayan yarufe musu kofa.

Zagaye yafara yi acikin dakin sa yana nazarin kalmar *ciki* da ake bama zahra.
"To ko cikin gareta."
Yafada a bayyane..bakin gado yazauna yana wani tunani..dole gobe muje asibiti adubaki, inkuwa wannan maganar cikin tazama gaskiya bazaki kara second daya da aurena ba don baza'a haifamin shegeba....

*****
Washe gari takama asabar ba aiki don haka suna gama breakfast yazid yace tashirya zasu asibiti.
"Misalin karfe shad'aya ta gama shirinta yazid ya d'auke a mota suka tafi general hospital dake garin kano.

Kai tsayi suka wuce office din Dr ben wani abokin yazid, already yasan da zuwan su don haka ya shiga duba zahra kamar yanda yazid yay masa bayani tunkan su i'so.
Bayan yagama kwaje kwajensa ne yake cema yazid baciki a jikinta teapot da malaria ne ke damunta sune suke sata zazzabi da aman data keye....magunguna ya rubuta musu yazid yay masa sallama suka tafo...

Dagudu takarasa gurin motar tashiga tareda fashewa da wani irin kuka maiban tausayi..." Harni yazid zaikawo asibiti amin kwadin ciki saboda cin fuska?...zargina ma yake daciki kenan ko?...kara fashewa tai dawani kukan zuciyar ta namata kuna.
Koda yashigo motar baiko kalli inda takeba yaja suka tafi...suna cikin tafiya wayarshi tafara ringing, idon tane yakai kan wayar da sunan mace baro2 yafita anrubuta *my zubaida* daga idonta tayi tana kallonshi wanda shima ita yake kallo. Juyar da kanta tayi zuwa kallon window...shima tabe baki yayi yay picking din call... Yane baby?."
Dan farr zubaida tayi jin sunan dayakirata dashi..
"Uhmm...danacewa nayi yaushe dakazo?."
"Eh kamar 2 zanzo kidai kikwantar da hankalinki...kimain kwalliya mai kyau kinji baby?."
"To shikenan Allah yakawo ka lpy."
"Amin baby na."
Kashe wayar yayi yanadan murmushi..juyawa yana kallon zahra don ganin reaction dinta. Still kanta yana juye tana kallon window..ci gaba yayi da tukunsa yana dan murmushi a cikin ransa koyanzu yasan yab'ata mata rea.

Misalin karfe biyu yafito falo cikin wata dakakkiyar shadda blue tayi matukar amsar farar fatarshi sai zuba k'amshi yakeyi..
Suna zaune falo baby namata tsifa duk suka bishi da i'do..
"Uhmm...yaa yazid kayi kyau..unguwa zakaje?." Baby tafada tana binshi da i'do.
"Eh." Ya amsa ta a takaice. Ficewa yayi zahra batako kalli inda yakeba bara taimishi Allah ya kiyaye.

****
Biyu da rabi daidai yazid ya isa kofar gidan su zubaida wayarsa wauarsa yaciro yakirata yasanar da ita zuwanshi, baa dau lokaciba tafito sanye da pink din douwar riga tayane kan da katon mayafi fuskamta dauke da murmushi ...

*👄BieBie Luv👄*

[3/12, 7:28 AM] ??BieBie Lurv??: *??KARUWA CE??.....25/26*

_Writing by_
*??BieBie Luv??*

_Editing by_
*??Sadnaf??*

*Masoyana a kullum i'na alfaharina daku, inajin dadin adduoin ku gareni...saida ince*
*Allah kabarni tareda masoyana , i'na sonku sosea❤❤❤*

????????????????
Chapter 6 · 0% Book details