← Book details Karuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 24

Sashe 14

Karuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Momy kam duniya sabuwa don tayi sabon d'a yazid yazama nasu sai yadda suka juyashi.

***
Yazid da zubaida na zaune falo kan sofa ta kwanta jikinshi ga waya hanunta tana karatun wani novel maisuna *mahimmamci budurci*. Dariya tayi kasa kasa "ohh..su budurci manya,,..mukan ai munkawo namu.." Tafada cikin ranta.
Yazid dake faman shafa mata dogon gashinta yace "baby yaushe zamuje gaida mami."
Bata rea tayi tana hararanshi. "Watoma maminka kadai kasani banda tawa uwar ko?."
"Noo..baby bahaka bane..duk zamuje har gidan momyn ma..." Karan wayarsane ya katsar dasu.. Sunan mami ne ya bayyana kan screen din.. "Kingama ..takira."
Tsaki tai k'asa2 tamayar da hankalin ta kan wayarta.

Mami ko amsa sallamarsa batayi ba bare kuma gaisuwa.."kazo yanzu ina naimanka."..daga haka takashe wayarta.

Kallon zubaida yake wanda itama kallonshi take cikin tuhuma..."wai me tace."
Dan gefen kansa ya sosa yace.."uhm..ca tayi inje yanzu tana menana."
Tsaki taja tareda cewa"to ba'inda zakaje,,ina bukatarka a kusa."
"A'a baby dan Allah kiyi hakuri kibarni inje,,,kinga mami ne."
Sauka tayi daga jikinshi tahaura sama tana cewa bazai jeba."
Shima tashi yayi yabita bedroom din yana bata hakuri. Dakyar yashawo kanta tayarda tabarshi,,amma tace kada yawuce minti talatin!.
Jiki na rawa yafita yashiga motarsa yay gidan mami.

*??BieBie Luv??*
[3/20, 2:42 PM] ??HABIEBA LUV??: *??KARUWA CE??.....47/48*

_Writing by_
*??BieBie Luv??*

_Editing by_
*??Sadnaf??*

~ ~*NOTE*~~

*MASU KARATU I'NASO KUGANE CEWA, NI _??BieBie Luv?? (HABIBA MOHAMMED)!_ NIKE RUBUTA LABARIN KARUWA CE BAI WAI _BIEBEE ISA!_ BA KO _BIEBIE DEE!_ KOKUMA _BEE BEEN MASOYA!_ BA....NI _??BieBie Luv??!_ NIKE RUBUTAWA YAKAMATA KUGANE WANNAN!.*

??????????????????

*_Y_*ana shiga yatarda mami falo sai zagaye take yi.. Kallo daya tai masa tadauke kanta tanema guri tazauna.. Shima gefen kafarta yazauna kansa kasa ya gaidata . bata amsa gaisuwarshi ba sai tambayar data jefo masa. "Ita kuma zahra n yaushe zata dawo?,,,tunda kungama cin amarcin naku ea saika dawo da i'ta." Ba yabo ba fallasa mami tai maganar. Shafa kyeyarsa yayi yace.."mami ea da canma bani nace tatafiba, ita tace tanason tafiyar...kuma tace wata biyu zatayi.." "Kana hauka ne Yazid dazaka barta hartai wata biyu?, to banyarda ...inaso acikin satinnan kaje da kanka kadauko ta kadawo da ita gidanta!." "Kobazaka iya bane ina maka makaga kayi shiru?." Mami tadaka masa tsawa , jiki a matukar sanyaye yace "to mami ." "tashi kabani gu...soko kawai..duk ka sakwarkwace akan mace."

Ikon Allah ne kadai yakai yazid gida..kansa sai juyawa yake saboda fargabar sanarwa zubaida zaije borno dauko zahra, damatukar wuya ta amince dazuwan!.
Tana kwance falo daga ita sai pant da bra gakuma eirpice kunnanta tanajin kida. Har yazauna gefenta batasani ba harsaida yarungumota jikinshi. Kara shigewa jikinshi tayi tamakalo hanunta tana shafa kwantaccen bakin gashin kansa. "Baby meye mamin tace?." Fuskarta yarike daduka hanayensa biyu yahade dahashi .. "Baby kinsan me?." Girgiza mai kai tayi batareda tace komaiba "mami tace cikin satinnan inje Maiduguri indauko zahra..." Kwace kanta tayi tana binshi dawata uwar harara "wllh ba inda zakaje ...bazakaje ba, saidai intagaji tadawo da kanta,,amma ba inda zakaje." Cikin masifa tai maganar.
"Kinga baby... Dakata tad'aga mishi hanu " ba'abinda zan saurara don baza kajeba..saidai ita mamin taje dakanta." Daga haka tatafi bedroom dinta. Sosea yaji haushin abinda tamasa, amma bayadda ya'iya yama matukar shakkarta ..tashi yayi yabi bayan ta.

***********
Yana sanye cikin kananan kaya masu kyan gaske sunyi matukar amsar sa.. Yana zaune falon aunty idonsa nakan wayarsa dake hanunsa yana dannawa. Suma fitowa sukayi cikin shirinsu sunyi matukar kyau, twice ne da zahra duk suna sanye cikin Arabian gown kowa tayi rolling dakaramin Vail din rigar. " yaa Yusuf mugama." Kallon salima datayi maganar yayi yawatsa mata harara.. "Saikubari nima nagama abinda nakeyi , don bazanyi tajiran Ku kuki fitowaba nikuma kuzo Ku azazzaleni." "We are sorry yaa Yusuf,, let's going...plss." Murmushi yayi yakalli zahra wanda tai maganar yatashi sukabi bayanshi. Shida zahra suna gaba twice kuma a baya suka tafi *KANTIAN* yin shopping don gobe Yusuf zaikuma Spain hutunsa yakare,,,kuma kowanne zuwanshi kafin yatafi sai yad'ebi kannansa sunje shopping yasai masu duk abinda suke bukata.
Sai yamma liliss suka dawo gida dakaya nik'i2 , kowa agajiye yake. Direct Yusuf yawuce part dinshi yasakarma kansa ruwa sannan yashirya yadawo falon aunty.. Suma lokacin duk sunyi wanka sunsanza kayi sunfito suna baje kayan a aunty.

Washegari..karfe hudu suka raka Yusuf airport, basu suka tafoba sai da sukaga tashin girginsu sannan suka tafi gida.

*******
Bayan sati.
Tun ranar da mami tama yazid maganar daukowa zahra bata karajin duriyarshi ba bare tasan yaje ko bai jeba. Halin da yazid yashiga na matukar damun mami, tana balain jin tausayinsa. Addua kawai tasa malamai namasa itama nakarawa danata.

Yau takama asabar, ranar daya ciki aure yazid da zubaida wata daya da sati biyu. Yayinda tafiyar zahra borno yazama wata daya da sati uku.
Yana durkushe gabanta yazuba gwiwoyinsa kasa yana rokonta.. "Don Allah baby kiyi hakuri, kitaimaka kibarni naje...wllh mami tace inbanje cikin wannan satinba tsinemin zatayi...don Allah ki amincemin." Kamar zaiyi kuka haka yake maganar.
Kokulashi batayiba idonta na kan wayarta datake dannawa. Tafi minti biyar haka kafin tadago tana kallonshi a yamutse.
"Zanbarka kaje, amma wllh aranar dakaje aranar zaka dawo kanaji?." Dasauri ya gyada mata kai eh...wllh nayarda.."bazan kwananba."
"Gud boy, to kabari sainayi tunani sai inbaka ranar dazakaje." "Baby mami fa tace cikin satinnan." "To katashi katafi yanzu man, tunda u ab ur own right.."
"Noo...baby don Allah kiyi hakuri.. Kawai natuna maki ne."

"Tashi kadawo kazauna nan." Tai commending dinsa tana nuna mishi gefenta. Jiki na rawa yatashi yazauna gefenta yana . cigaba tai da danna wayarta tana kada kafa."

Ranar jumma'a , shine ranar da zuby tacirema yazid zuwa Maiduguri.
Dawuri yagama shirinsa yama hajiyarsa sallama yashiga motarsa yatafi..dugun har yatafi a jirgi yarasa dawowa yaudin..

Acan kuwa tunda zahra tashiga satin tafiya gyara aunty tasa anai mata naciki dana waje saikace wata amarya.
Yau zahra na kwance a daki tun safe hakanan kawai kirjinta ke faduwa , addua kawai takeyi acikin ranta har tai bacci.

Kamar a mafarki taji muryan aunty na kiranta , a hankali take bude idonta har suka gama bud'ewa duka,
Aunty tagani zaune bakin gadon na zaune. Tashi tayi zaune bakinta dauke da salati tana tambayar aunty.
"Kedai, mijin kine yagaza hakuri yabiyoki, kinganshi can falo najiran fitowarki,,,,,,kuma yace kishirya yanzu zaku tafi."
Tunda aunty tafara maganar kirjinta ya tsananta bugawa. Dakewa tayi tace" nikan aunty kice mai yatafi ai wata biyun dayace nayi bai cika ba,,sai gobene zai cika." "Ke da'alla banson shirme,,,da yau dagoben ea duk daya ne kuma tunda yazo ai ko lokaci baicika ba dole kibishi....don haka kitashi ki shirya.

Tana hawaye tatashi tashiga bathroom aunty kuma tashiga hada mata kayan ta.
Cikin minti talatin tagama shiri suka sauko falo tare da aunty.
Wani wawan yankewa gabanta yayi lokacin data hangoshi zaune shima idonsa nakan ta. Wani iri taga yazama kamar ba Yazid ba,, sabanin yazid dayaga takara kyau sosea tayi kiba abunta gawani sheki da fatanta keyi. Sauri dauke idonsa daga kanta yayi tare da mikewa.
Inda yake suka karaso zahra tagaidashi cikin sanyi ya amsa . zaunar dasu aunty tayi tana musu nasiha sosea,,shide yazid duk bayan wani lokaci saiya duba agogo gudun har lokaci yakure yashi ubansa gurin zubaida.
Harbakin mota suka rakasu su twins na dagama zahra hanu har saida suka fita daga gidan...su hajiya zahra kam harda dan hawaye.
A mota bawanda yakallin dan uwansa bare magana ta hadasu,,haka suka ringa tafiya har suka shiga kano.
Ana kiraye2 n sallar magrib yazid yay parking a parking lot din gidansa, fito mata da kayanta daga Booth yayi yabar matasu gurin yay shigewarsa. Daukar akwatin tai dakyar tana ja tashiga falon.

Zubaida na zaune falon tasa wasu gantalallun kaya takure waka tana bi.
Tana ganin yazid tataso ta rungumeshi tana shigewa jikinsa ..."oyoyo baby..I miss you wollh" shima rungumeta yayi yarike west dinta yana kissing wuyanta.
Bakinta dauke da sallama tashigo falon , ido hudu sukayi da zubaida wanda idonta ke kan kofar falon. Kallonta kawai zahra takeyi ko kiftawa babu..

*??BieBie Luv??*
[3/22, 10:19 AM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝K̥ͦḀͦR̥ͦU̥ͦWྂAྂ CྂE💝ྂ...... 49/50*

_wrítíng вч_
*👄hαвєєвαtєє👄*

_єdítíng вч_
*💅ѕαdnαf💅*

*🇳 🇴 🇹 🇪*

*ASSALAMU ALAIKUM MASOYANA, NA CANJA SUNANA DAGA 👄BIEBIE LUV👄 ZUWA _HABIEBATIE_. LURA DA YANDA SUNAN NAMU YAZO D'AYA DA WASU WRITERS: BIEBIE ISAH, BIEBIE DEE DA BEE BEEN MASOYA.. NAGA ANA TA CECE KUCE AKAI KOWACE TANA GUDUN ACE ITA TA RUBUTA NOVEL D'IN KARUWACE, INDA HAR AKA FARA WRITE UP DAN ANA YAD'AWA. TO SUNAN NOVEL BASHI YAKE NUNAWA NOVEL BANA ARZIKI BANE DARASIN DAKE K'UNSHE A CIKI SHI YAFI MAHIMMANCI KUMA ALHAMDULILLAH TUNDA NA FARA BABU WANDA YA ZAGENI SABIDA BA ABUNDA KUKE ZARGIN NA RUBUTA SHINE A CIKI BA,, KUMA BABU LAIFI MASOYANA DAKE BIYE DANI SUN SAN HAKA BABU BATSA A CIKI SAI DAI KUCE SUNAN NOVEL D'IN DAI BAI DACE BA BABU SUNAN KUMA DAYA DACE DASHI SAMA DA KARUWA CE DAN HAKA MASOYANA HANYAR LAFIYA A BITA DA SHEKARA DAGA YANZU HAR NAGAMA DA HABIEBATIE ZAN RINGA AMFANI HAKA KUMA A DUK WANI NOVEL DA ZANYI DAFATAN MASU TUNANIN BIEBIE ISA DA BEE BEEN MASOYA KE NOVEL D'IN KARUWANCI YANZU ZASU BANBANCE DAN IDAN KAI MAI BIN NOVEL D'IN MUTUM NE SOSAI YACI ACE KA GANE RUBUTUNSA HAKA MA DA TSARIN LABARINSA BA A FAKE DA HAKA BA NGD.*🙏🙏🙏🙏😎

_bansan iriyar godiyar da zan makuba mosayana masu kirana a waya damasu taramin sako..nagode sosea da kulawarku, Allah yabarmu tare..
#One ❤.

💝💝💝💝💝💝💝💝💝
Chapter 14 · 0% Book details