← Book details Karuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 24

Sashe 21

Karuwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Shadaya suka isa , can nesa ya hango *Ajibt* wani friend dinshi dama already yasanar dashi zuwansa kuma gidansu zai sauka. Hugging din juna sukayi suna mai farin ciki, at d end dai mota suka shiga sukatafi. Wow nace time din da'a wangale get din gidan. gidane na bugawa a jarida don yahadu harshe. Mahaifin ajibt mai kudine sosea dan siyasa ne. Saida suka biya yazid ya gaida umman ajibt sannan suka wuce part dinshi.

"Kai man yanaga duk kafita daga yazid dinka?." Furzar da iska mai zafi yazid yayi ya koroma ajibt abinda ke damunsa. Sosea ya tausayama yazid "man harka damu insha Allah komai zai dai2 ta ,zan taimaka maka.

Wanka yazid yayi yasa kananan kaya yafito falo suka zauna da ajibt suna tattauna yanda zasujema zahra. daga bangaren Umma tasa akakawo musu lafiyayyen lunch, saida sukaci suka koshi sannan yazid yace" man yanzufa zamu je." Harara ajibt ya balla masa "saimuje din ea, kabari sai gobe man amma daga zuwa , ko hutu babu.." "Kaga nibansan wulakanci, aikasan ba hutu nazoba kawai inzaka rakani kazo muje.." Bayanda ajibt ya i'ya haka yatashi suka tafi.
"Yazid dama nan gidan ne?, ae gidan abokin Daddy ne!." Gyada kai yazid yayi "abun zaizo mana dad'an sauki kenan!." Basusha wani wahalan shiga gidanba don maigadin yashaida yazid, kuma dama yasan ajibt sometimes akan eakoashi gidan. parking sukayi suka fito akabud'e masu dayan get din suka shiga.

Sanye takeda wani doguwar pink riga 'yar kanti , ta matseta sosea tafidda mata da shep dinta ga boos dinta suncika rigar kamar zasu fito. Tayi rolling da milk din vail, tasa hell hill milk mai adon stones kamar yadda yake gaban rigarta ma stones masu kyau jere. Tana zaune cikin wani rumfa mai zagaye da flawers gaba daya attention dinta nakan wayar ta datake charting kuma da'alamu yanai mata dadi.

Tunda daga nesa yazuba mata mayun idonsa yana kallonta, gani yake kamar ba i'ta..tayi wani irin kyau na musamman sai shining take gawani kiba datayi . har i'sa gurin batasan ya i'sa ba, wayar hanunta yarike tareda had'awa da beautiful fingers dinta. Dagowa tayi tana kallonsa don duk a tunaninta Yusuf, razana tayi tamike tana binshi dawani irin kallo wanda bansan nameba..shima kallonta yake kamar lakacin yafara kallonta "ZAHRA!." Yafada cikin wani murya. Gagara cewa komai tayi sai gaban dake balain faduwa..shima dakewa kawai yake amma wani irin faduwar gaba yakeyi. Pls say something man.." Still batace komaiba kuma idonta nakansa .. ganin taki magane yamatso kusanta yana kokarin riketa, dai-dai shigowar Yusuf kenan ya hango yazid nakokarin rikota "stop malam don't ever touch her!!!." Cikin d'aga murya yay maganar. Karasowa gurin yayi yana watsama yazid wani disguise looking. "Meye kake kokarin yi haka, bayan yanzu ba marka bace!." Shima yazid din wani kallo yawatsa masa "kila kaika datse mana aurenko!?." "I think divorce paper kakawo mata!?." Wani murmushin rainin hankali yazid yasaki "tsakanin aurena da zahra basaki ciki..I want u to know dat nazo tafiya da matata ne!." "Kayi kad'an! Baka i'saba dole kasaketa..at dat time nikeda i'ko da ZAHRA! ba kaiba!. so dole sai yadda nayi..kaikafa buga game din amma nikeda ikon tsaidashi.. dis is just to beginning!.. Yanzu akafara kick din!.."
"Haka kace!?." "Haka nafad'a!." "Muzuba mugani zanga wazaiyi wining!" Murmushin gefe Yusuf yasaki "U shall see!." Daga haka yaja hanun zahra sukayi ciki. Serere akabar yazid gun yama rasa abunyi, jiki a matukar sanyaye yaja kafarsa da kyar yashiga mota ajibt yaja sukabar gidan.

*👄habiebah luv👄*
[3/29, 11:25 AM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝KARUWA CE💝.......65/66*

_Writing by_
*👄habiebah Luv👄*

_Editing by_
*💅Sadnaf💅*

_Kuyi hakuri da wannan bayawa...don banjin dadi..._

💝💝💝💝💝💝💝💝💝

Runtsa idonsa yayi dak'arfi yanajin zuciyarshi kamar zata fito..."meye wannan Yusuf din kenufi ne!?." Ganin bazai iya samo amsarba yasa yabude idonsa dasuka dawo kamar gaushi don jaa yasauke kan ajibt wanda shima kallonsa yake. Dafa kafadanshi ajibt yayi "kakwantar da hankalinka frnd insha Allah komai zai dawo dai2..kuma kasan me?." Kai yazid yagirgiza batare dayace komai ba. "In dis week daddy will come back from Cairo kaga saikawai mufada mishi dakansa zaije yama abban su Yusuf din magana.." "Gud idea frnd ngde Allah yasaka..." "Noo ..u deserved it ea.." Key ajibt yama motar suka fita daga gidan .

Kusan cin karo sukayi da aunty dake bakin kofar falo kusan duk abinda sukayi a idonta, fuska a matukar daure take kallon Yusuf.. "Shige ciki.." Tafada zahra jiki a sanyaye tawuce kamar wanda kwai yafashema a ciki haka take tafiya , gaba daya takasa gane condition din datake ciki. "YUSUF!." Aunty takira sunanshi bayan sunkara sa falon sun zauna , sauke kansa k'asa yayi batare daya amsaba "kanakishin zahra ne!." Kamar saukar aradu haka yakejin maganar aunty. "I'm asking u nd u keep silent.." Dagowa yayi yakalleta still he can't say anything.. " U can go..tunda kazama kurma.." Da kyar ya'i d'aga kafarsa yafita gaba daya tunaninsa ya cakub'e. Tashi aunty tayi tashiga dakin zahra, gamamakinta hangota tayi kwanshe gado tana hararar hawaye..gada daya tausayinta ne yakama aunty , tarasa gane gaskiyar ta tanason mijin tane koya?." , gakuma wani lamari datake ganowa kamar zahra nada ciki.. Karasawa tayi tad'agota ta rumgumeta tana pitting bayanta "kiyi shiru daughter, its okey.." Tsit tayi sai ajiyan zuciya datake saukewa . "ZAHRA!." "Naam aunty" har kiboyemin komai, take me as ur mother fad'amin kinason yazid ne!?, kinason komawa gidanshi..!?." Zabura tayi tad'ago saikuma tamaida kanta tasaki kuka. "Aunty ni basonsa nakeba, kawai dai yaban tausayi ne ...." Tafad'a cikin kuka..."to ya'isa, shikenan..kiyi shiru." Lallashinta tarinkayi harsaida tai bacci. Tsayawa kallon tayi nakusan minti goma tana kissima abubuwa a ranta, daga karshe fita takoma bedroom dinta.
Yazid nazaune kan gado gabanshi da system yana dannawa, shikuma ajibt nakwance yana waya. Bayan yagama wayarsa ya dago yana kallon yazid , seriously yafara mishi magana "kagani Dr ne ko Yazid!?." Dagowa yayi yana kallonsa da mamaki "ca akwai maka bansaniba!?." "To alhmdllh tunda kasani..as my observation nagano matarka! ZAHRA! Nada ciki!." Wani uban zabura yazid yayi yajuyo yana kallon shi. "Ajibt CIKI!?." "Yeah,sure ciki!." Rasa gane condition din da ke ciki nayi, kamar wanda aka zabura yatashi yadauki makullin mota yay hanyar fita, fixgoshi ajibt yayi yana watsa masa wani kallon. "What are u trying to do?." "Bansaniba, dalla sakeni ..zanje in dauko matata ne ta haihu a gurine..inkuma sunce bazata biyoniba sai sucire cikin suban abina!, tunda ninayi!." Wani mugun dariya ajibt yasheke da "wato ance matarka nada ciki harka samu abin gadarako?, to wllh kamaida hankalinka inkace zakai masu wautar 'yan fari duka zasuk'i badata..gara kabi a sannu.
Dawowa yayi yazauna yana sosa geya, wani irin farin ciki yakeji mara misaltuwa wanda baitaba jiba!.

Kano...
Karfe goma faruq yashigo gidan yazid , da spirykey yatoho yabode falon yashiga . time Zubaida nasaune kasa tabuga uban tagumi , karasowa yayi yazauna gefenta sai a lokacin taji mutum, a razane tadago tana kallon shi tayi tunanin yazid ne saikuma taga faruq ne. Kallon dataga yakemane yasa tasauke kanta kasa " tashi inkaiki gida.." Kamar jira takekuwa tamika tai hanyar waje.. Murmushi furuq yayi yabi bayanta...rufe falon yayi yashiga motar dama zuby kam tuni tashige. A haka suka isa harcikin gidansu yakaita , tunda akashigo idonta yafara tara kwalla, godiya sosea tamishi tashige ciki da gudu tana sakin wani kuka. Tausayinta yagama cikishi saida yaga shigewarta kana yaja motarshi yafito.
Momy tana zaune falo ga abinci gaban takasa ci gaya tabuga wani uban tagumi . kamar daga sama take jiyo kukan zubaida , idonta takai kan kofa dai2 isonwan zubaida kenan.. wani irin super momy tayi ta rungume zubaida suka saki wani irin kuka....

*👄habiebah Luv👄*
[3/31, 11:56 AM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝KARUWA CE💝.....67/68*

_Writing by_
*👄habiebah Luv👄*

_Editing by_
*💅Sadnaf💅*

_Dis page is 4 u 🌹Ayshah🌹, tnku for diffusion my book._

💝💝💝💝💝💝💝💝💝
Chapter 21 · 0% Book details