← Book details Kano To Jidda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 15

Sashe 9

Kano To Jidda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shigarta É—akin yayi daidai da fitowar shi daga wanka shima É—aure da tawul.

A fusace yake kallonta.yace.

"ke mahaukaciyar inace zaki shigomin É—aki ahaka?"

Murmushi tayi sannan tace.

"Don Allah kayi haƙuri saurine yasa namanta nataho ahaka,kaga har na gama wanke kaina se hand drayer ɗin takiyi,shine naje gurin suhaima tabani nata to ashe itama natan yasamu matsala,shine nakeso don Allah ka aramin naka nayi da ita"harda marairaicewarta.

Harga Allah ya É—auka da gaske takeyi danhaka guri yabata,yaje tashiga toilet din ta É—auko,ayko shigewa tayi ta jima tana É—an waige waige,shi kuma ruwan jikinshi yashiga tsanewa.

Daga cikin toilet É—in kafilat tace,"kaga wlh bangantaba kode idonane,don Allah kazo kabani"

Tsaki shureim yaja sannan yanufi toilet ɗin,dan ya ƙosa tazo ta fice mishi daga ɗaki,yana shiga ya ɗauko mata ya bata.

Shigarshi toilet É—in yayi daidai da shigowar suhaima,É—auke da injin shara,tazo share É—akin.

tana shiga shi kuma yafara fitowa daga toilet ɗaure da tawul,binshi tayi da kallo,zuwacan sega kafilat ta fito itama ɗaure da tawul kanta ajiƙe,tana dariya tace.

"Shine kuma zaka fito kabarni,aciki,bayan kasan kaine kace na shiga"yi tayi kamar bataga suhaima ba,tana kaiwa ƙarshen maganar ta kalli shashin da suhaima take kallonsu baki a buɗe,nunawa tayi irin ta razanannan harda dan ɓoyewa abayan shureim

Shiko shureim gabs É—aya kunya ce tagama kamashi,dan yasan suhaima ba yarinya bace da zata yarda hand drayer kafilat tazo amsa,runtse ido kawai yayi yadafe kai,ko kaÉ—an beji daÉ—in ganin data mishi ahaka shida kafilat ba.

itako suhaima tuni hawaye yagama wanke mata fuska,da gudu ta juya tabar É—akin tana kuka kamar ranta ze fita.

muje zuwa.

surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra Muhammad Mahmud

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

*Kausar luv group naga comments É—inku jiya nasha dariya,Allah yabarmu da masu sonmu na gaskiya,nagode sosai*

*Dedicated to zahra bukar*

*35-36*

Da sauri kafilat ta fice daga É—akin,farinciki fes zuciyarta,sabida tarkonta ya kama kurciya.

Shureim kasa yin komai yayi,dan haka kan gadonshi yanufa yazauna yayi tagumi yama rasa abinda yake masa daÉ—i.

Suhaima É—akinta ta nufa,tana shiga ta faÉ—a kan gado tashiga rusa kuka me tsuma zuciya.

"Dama ashe da ita yake kwana shiyasa ya hanani zuwa É—akinsa,?"ta sake fashewa da kuka.

"yazanyi da wannan kafilat É—in?mezanyi na rabata da gidana da mijina?mezanyi?" ta faÉ—i tana dukan kanta ,gaba É—aya ta hargitsa gashin kanta,fuskarta tai ja abunka da farar mace,se gunjin kuka takeyi,gami da dukan kanta akan yafaÉ—amata abinda zatayiwa kafilat.

Wuni tayi aÉ—aki bata fitoba in banda kuka ba abinda takeyi,bata ganin laifin kowa sena mahaifinta,acewarta,zagin dayake matane,yake jefata cikin mawuyacin hali.

"na tsaneka nima baffa,bana sonka"shi take furtawa cikin kuka abun gwanin tausayi.

Tana nan tanata tunani,zuwacan ta tuno da wata matar aure da aka aurota daga Kiru,aka kawota garinsu me suna hauwa.

In tafita da shinkafa sanda tana nigeria tana biyawa ta gidan.

Na farko de hauwa me tsafta ce,gata ta iya abinci,sannan bata barin kowacce mace tana kallar mata miji,da zaran yadawo ko waye agurin da gudu take zuwa ta rungumeshi,kuma in ta rakashi É—aki,tana jimawa bata fitoba,

Hakade taita tuno halayen hauwa,da yadda take rayuwarta.

Se bayan laasar ta gamsu da natsuwar zuciyarta,wanka tashiga ta jima tana wanke jikinta sannan ta fito,ta zauna tayi kwalliya.

kayan ta ta buÉ—e na aure,wani akwatin english wears ne kawai aciki.

Zubesu tayi duka akan gado tashiga gwadawa,harde tasaka wanda yafi kwanta mata arai kuma ta gamsu da sunmata kyau.

Rigar maroon ce doguwa har ƙasa me hannun base,daga gefen cinyoyinta guda biyu,tsagune tundaga ƙasa har zuwa daidai kugunta,daga dede cikinta na rigar zuwa,kasan boobs ɗinta,net ne me manyan huda,daga saman rigar kuma lace ne wanda rabin boobs ɗinta kawai yarufe sauran suna waje, daga bayan rigar,gaba ɗaya abuɗe yake daidai setin boobs ɗintane ta baya akwai gurin makalewa kamarde bresia.

Gashin kanta doghnut É—inshi tayi,sannan taÉ—an zubo da wani ta gaban goshinta.

Takalmi tasaka me tudu sosai shima marroon,kuma me irin igiyar nanne da se an naɗe kusan rabin ƙafar da shi.

ɓarin turare tayiwa kanta,tsayawa tayi gaban mirror tana kallon kanta,ita da kanta ts burge kanta,wata kunyace takamta,data kalli,yadda fararen cinyoyin suke a waje,da rabin boobs ɗinta,ta baya ma data juya ta kalli mazaunanta abun kunya yabata.

Kasa fita kuma tayi tana tunanin in taje me kuma zata yi,da kyar de ta amince ta fice daga É—akin.

Hips É—inta na rawa haka mazaunanta,boobs shima baa barshi abayaba,yanayin tafiyar suhaima kenan,sweet 16.

Shureim da kyar yasaka doguwar riga,yafito yanufi ɗakin suhaima domin ya rarrasheta,sede yana zuwa bakin ƙofar,jin yadda take kukane yasa yakasa shiga,sabida yasan duk abinda ze faɗi ba yarda zatayiba,hakanne yasa yakoma falo ya zauna yana jiran yaga ko zata fito amman shuru,

Kafilat ganinshi afalo ne yasa tazo falon tana janshi da hira,ji yake kamar ya kasheta amman se ya daure,sabida hukuncin ba nashi bane,na suhaimane.

Suna nan zaune,ƙamshin turarentane yafara kawo musu tsegumin sunada baƙo,zuwacan suka fara jiyo sautin takalminta.

Gaba ɗaya hankalinsu yakoma gurin step ɗin sun ƙosa suga waye,sunfi tunanin may be baƙuwa tayi.

*Suhaima gimbiyace,daya jiran dubu,end of discussion,full option,duk wanda yasamu yagama zabi,me akwai ce ita komai yaji,yaran nigeria,masu abun mamaki,baka sanin darajarsu,se sun baka mamaki,haka suke,ku dade ku jima kui karko yan nigeria,kishi daku sede ku,amman wacce bakuba bata iyawa,kissa ajininku take,one luv yan nigeria*

Bullowar suhaima,seda ganin kafilat ya É—auke na wani lokaci sannan ya dawo.

Shureim ko numfashinshine ya riƙe,miƙewa tsaye yayi kawai baki buɗe yana kallonta.

Tunda ta gama sakkowa daga kan stairs din,ta fara doka musu murmushi,hakanne yaba dimples É—inta fitowa,gamida kyakkyawar wushiryarta,takuntama ta sake sauyashi.

Kafilat jikinta har rawa yakeyi,bata taɓa sanin kyan suhaima yakai har haka ba,take taji ta raina kanta.

Suhaima ko tans ƙarasowa ko kallo kafilat bata ishetaba,kai tsaye gurin shureim ta nufa,wanda ke tsaye kamar gunki.

Tana zuwa rungumeshi tayi,ay besan sanda shima ya rungumeta ba,se ɓoye fuskarshi yakeyi dan gaba ɗaya kunyarta yake ji,itako ɗago fuskarshi tayo ta haɗa bakinta ta nashi,taɗanyi kissing ɗinshi ns ƴan mintuna.

Bakinshi na rawa ya haɗa hannayenshi biyu yana son bata haƙuri,da sauri ta riƙe hannayen,sannan ta ɗora ɗan yatsanta akan lips dinshi tace.

"shshsh,bakamin komaiba bare kabani haƙuri,najima da sanin waye mijina,dan haka kada wannan ƴar dramer da aka shirya ta dameka,ko ɗazu dakaga nafita da gudu ina kuka,to ay nasan dramer irin wannan yadda nayi ɗin hak dama akeso star ɗin film tayi to nayine sabida na ƙawata wasan,dan haka kar ka damu,matarka ɗaya aduniya kuma nice,dagani ba ƙari har bada,nawane ni kaɗai koba haka bane habibi"

Bakin shureim har rawa yakeyi gurin faÉ—in.

"hakane hakane habibati"

Rungumeshi tayi sosai suna dariya,ɗan sakin shi tayi tana kare mishi kallo sannan tafara dira ƙafa a ƙasa tana kuka tace.

"meya hanaka yin wanka yau,da zaka zauna da doguwar riga tun safe?"

Rarrashinta zeyi sekuma ta dakatar dashi da cewa.

"koda yake ba laifinka bane,ni me maka wankance banzo nayi maka ba,dan haka muje nayi maka"

Shureim farincikin dayake ciki baya misaltuwa,sanda yakai dubansa gurin kafilat yaga ruwan hawaye na ambaliya a fuskarta.

Suhaima ko ko kallon inda take batayiba,É—aukarta shureim yayi kamar jaririya yana faÉ—in.

"muje nima na wankeki da kaina,dan banason ki sake yiwa kanki wanka"

a haka suka haura sama zuwa É—akin shureim.

Wata ƙara kafilat ta saki ta shiga dukan kanta tana kuka tana faɗin.

"ƙarya kike suhaima shureim nawane ni kaɗai wallahi sena tabbatar miki da hakan"da gudu tanufi ɗakinta tana kuka zuciyarta namata ƙuna,baa taɓa ɓata mata rai irin na yauba.

muje zuwa.

surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra Muhammad Mahmud

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

*Dedicated to Zahra Bukar*

*37-38*

Suna shiga ɗakinsa ta kwace daga hannunsa,ta wuce toilet ta haɗa masa ruwan wankan sannan tafito rai aɓace tace.

"ka shiga kayi wanka"

Kallo yabita dashi,gaba ɗaya jikinshi yayi sanyi,yanason yin magana amnan ganin ba fuska dole haka ya haƙure yashige toilet ɗin.

Be jimaba yafito,a bakin ƙofar toilet ɗin yasameta riƙe da towel,yana fitowa tafara tsane mishi ruwan jikinshi.

Seda ta tabbatar ya shirya fes sannan ta fice daga É—akin ta nufi kitchen.

Abinci ta haÉ—a me rai da lafiya ta jere a dinning,sannan ta nufi É—akinshi.

A zaune ta sameshi yayi shuru,bata ce komaiba illah.

"abinci na jiranka a dinning"tana kaiwa nan ta juya ta fice daga É—akin.

Haka yatashi shi kaÉ—ai yanufi dinning É—in.

Kafilat jin ƙamshin abincine yasa tamiƙe tashiga toilet ta yi wanka tafito ta cakare da english wears masu kyau sannan tanufi dinning dan ta tabbatar angama.

Itako suhaima ɗakinta ta shiga,wanka itama tasakeyi sannan ta fito ɗaure da towel,gaban mirror taje,tagama iya kwalliyar dazatayi,sannan ta ɗauki bresia tasaka sede bata saka maɓallinba,ta zura silifas ta nufi dinning ɗin.

Lomar abincin da kafilat takai bakinta tace ta tokare mata maƙoshi,yayinda ta hangi suhaima ɗaure da tawul da bra ta nufosu.

Suhaima ko ko kallo bata isheta ba,kai tsaye gurin shureim taje ta haye cinyarshi tana kukan shagwaɓa,cikin kukan take faɗin.

"Habibi nidama nace maka ban iya sakawa ba kace na ƙoƙarta nasaka gashi tunda muka fito daga wanka nake ta fama da bra ɗin yaƙi sakuwa,ni kasamin"ta faɗi gami da juya mishi baya yasaka mata.

Carab kafilat tai ƙarfin halin cewa,

"Haba ke kuwa,me makwan ki kirani nasaka miki,ay ba se kin fito ahakaba,da se nazo har É—aki nasaka miki"

wani kallo suhaima ta watsa mata sannan ta yi murmushi tace.

"kafilat kenan,ay dillalin wada shi yasan kuɗin jariri,kuma kowa yaci ladan kuturu se yamasa aski,ta inda aka hau tanan ake sauka,shi yaciremin kinga ko dole yamayarmin,kuma dadin dadawa koni bansan daidai inda zan maƙala tamin daidaiba,shiko dayake kullum cikin taammali yake dasu yajima da sanin daidai inda zesamin ta zauna bata matseni ba,da badan haka ba ayke zan kira ki samin ta wajena"ta ƙarasa maganar tana dariya.

Makwat!!!!abincin da kafilat takeci yawuce zuwa cikinta.

gaba ɗaya ta daburce tama rasa me zata sake cewa ranta yayi masifar ɓaci.

shiko shureim tsab ya sakawa suhaima bra É—in yana gamawa tace.

"to muje ka ƙarasa shiryani,danni wlh duk nagaji gurin yimaka wanka da shiryaka"

miƙewa yayi ɗauke da ita a hannunshi,yayinda mamakinta ya cika shi,tunaninsa wai dama can haka takene ko yaya,?kode da gaskene yan nigeria hakan suke?.

Da wannan tunanin suka shiga É—akin,suna shiga direwa tayi daga hannunshi taje taci gaba da shirya kanta,ko kallonshi bata yiba.

Abun sosai yaba shureim dariya dan haka dariya yashigayi harda ƙyaƙyatawa.
Chapter 9 · 0% Book details