← Book details Kano To Jidda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 15

Sashe 13

Kano To Jidda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gari be gama wayeba sega hanne tazo gurin suhaimar bayan sungaisa tace mata.

"innace tace nazo na tayaki É—aukar yaran kizo tamuku wanka tun É—azu ta kwashe ruwan"

kukane ya kwacewa suhaima data tuno tata innar.

Haka suka tafi gidan su hanne.

suna zuwa toilet suhaima tashiga inna tamata wankan jego,sannan tasata ta zauna a ruwa.

Bayan sun fito inna ta wanke yaran,sannan ta É—auko rigunan data siyo musu jiya da yamma tasaka musu.

duk da rigunan bamasu tsada bane amman,sunyi musu kyau.

Daga ƙarshede suhaima a gidan ta zauna inna na kulawa da ita har seda tayi arbain.

su twins ko irin masu girman,agir dinnanne,sunyi yan lukutaye dasu abunsu,gasu da wayo.

Bayan suhaima tayi arbainne takoma gidansu,taci gaba da bauta,dan bazata juri ganin mahaifinta nayiba.

ya hanata yace tabarshi shi yayi amman fafur taki amincewa.

Ruwa kawai take barinshi yana É—ebowa,amman tallah tuni ta koma bakin aykinta.

in zata tafi,seta goya twins,É—aya agaba É—aya abaya,innar hanne ce ta koyamata irin goyon.

Se tasaka hijab É—inta ta rufesu ahaka zasuje sugama yawo arana su dawo.

Duk wani haske da suhaima tayi tuni ya dishe,sabida wahala.

Yau tun cikin dare Abdulrahman yake kwara amai,ga zazzafan zazzaɓi daya rufeshi,se kuka yakeyi,

Hankalin suhaima inyayi dubu yatashi tarasa inda zatasa kanta Allah Allah take gari ya waye.

Ayko bakwai abakin chemis din rabiu dan me gari yamata.

Duk saurinta seda ta samu layi,sabida chemis din shine kamar asibitinsu,dayake babbah ne.

Layin tashiga har yazo kanta.

Koda tashiga yagama dubashi,maganin dubu daya yarubuta mata.

kuka suhaima tasamishi akan yaymata bashi zata biyashi,buÉ—ar bakinshi se cewa yayi.

"keko suhaima din Allah haka kikaje kika gama rabawa larabawan abun kyauta basu baki komaiba se tukuicin yayan zina?"

maganar ta doketa amnan tunda neman taimako takeyi dole ta bashi amsa a saukake.

"wlh kabiru yaran nan bana zina bane,zaku tabbatar da hakanne ranar da mahaifinsu yabiyo sahunsu"

"nufinki aure kikayi acan?"

Da sauri suhaima tace,

"Aure nayi,to mijina ne yasakeni shiyasa nadawo"

"tunda yasakekine to inga takardar sakin".

dayake da handbag dinta ta tafi ba musu,ta zuge ta ɗauko katin Atm se alokacin ta lura akwai wasu takardun kanana aciki ,duka ta ɗauko ta miƙawa Rabiu.

Amsa yayi yana dubawa,yana dariya,sannan yace.

"Suhaima ay wannan ba takaddun saki bane,takardun cire kuɗine akowacce ƙasa kake inkaje zaka cire kuɗin dake cikin asusun ajiyarka"

ido kawai suhaima take warewa,dan bata yarda da batun na rabiu ba.

ganin bata yarda bane yasa yace.

"kinga bari inbaki maganin kije kibashi,anjima inkina da lokaci inna tashi daga ayki,kizo muje kano a duba miki aga ko nawane aciki,da duk wani bayani zasuyi miki"

se yanzu hankalinta ya kwanta,dan ita lafiyar É—anta yafi mata komai.

maganin yabata ta dawo gida,taba Abdurrahman,sannan taimusu wanka itama tayi,ta goyasu suka tafi tallah.

bayan ta dawone,taje gurin rabiu shima lokacin yatashi,dan haka a motarshi ya dauketa honda civic,suka nufi kano.

Tafiyar awa guda ce takaisu bakin wafer.

Da kyar suka samu suka samu wanda ze musu abinda yakawosu,baa sha wahala ba sabida a takardun harda pin number da accaunt no,dan haka,mutumin nagama dubawa ya É—ago yace musu.

"da akwai kuÉ—i aciki har kimanin naira miliyan dari dari"

"miliyan É—ari?"rabiu da suhaima suka haÉ—a baki gurin tambaya.

Tabbatar musu da hakan yayi.

suhaima sabuwar soyayyar mijintace takamata,wato yabatane dan beson tasha wahalar rayuws.

Dubu É—ari uku suhaima tasa aka ciro mata,sannan suka baro gurin.

Kasuwa tasa yakaita,nanfa ta dagargaji siyayya,tasu twins dinta,harda gidan sauro ta siya musu,da madara da cerelac,daduk wani nauin abinci na yara me gina jiki.

suturu kuwa tasiya musu su ba adadi,da pampers duk ta jidar musu,da takalma,da sabulan wanka dana gyara gashinsu,dayake gashi garesu sosai irin na larabawa.

seda takashe dubu É—ari biyu a siyayyarsu,sannan taba rabiu dubu talatin,se godiya yake mata,sabida yaji dadinsu.

haka suka kamo hanyar laminkwai,gab da magriba suka iso.

lantana na zaune se gani take ana shigo da kaya,har aka gama shigewa dasu É—akin suhaiman.

wani baƙincikine yaziyarci zuciyarta,take tasha alwashin seta sace kayan.

Bata gama tunaninba,sega suhaima dame gyaran ƙofa,tasa yasakamata kuba a kofar,ta yadda duk balai bame shigar mata ɗaki.

shiga tayi ta ware komai,sannan ta kafa musu katifunsu da gidan sauronsu.

dubu ashirin ta É—auka takaiwa maman hanne,sannan tamata bayanin komai,godiya taimata sosai gami da sa albarka.

a ƙofar gida tasamu mahaifinta,tamiƙs masa dubu arbain sannan tace masa.

"Baffa ka ɓoye kadunga cin abinci me kyau don Allah ko gobe suka kare kamin magana zan ƙara maka,kadena yiwa matarka biyayya sabida abun duniya kaji don Allah"

murnar da yayi bata da iyaka,dan azahirin gaskiya sabida kuÉ—i yake bin umarnin matarshi,dan yasamu nacin abinci.

Cikin kankanin lokaci,baffa ya sauya duk abinda yakeso yakeci,ba abinda yadameshi da girkin lantana.

su twins tuni sun fara iya zama,Abdurrahman dayake yafi ƙiriniya har yafara son yayi rarrafe.

Yanzu suhaima inzataje tallah se takaisu gurin maman hanne,dan bata dens tallan bane sabida masifar da lantana take zubawa mahaifinta.

sabida hankalin baffa ya kwantane yasa taci gaba da tallan.

É—akinta kullum arufe yake ba damar lantana taimata sata.

kuɗinta insuka ƙare rabiu ne me zuwa ya ciromata wasu yakawo mata.

amanar rabiuce tasa suhaima É—aukar miliyan guda tabashi,ya faÉ—aÉ—a chemis É—inshi.

Watannin su twins bakwai suka fara rarrafe,abun gwanin shaawa.

*******
Saudiyya

Ba irin neman da baayiwa hajiya murja a riyad ba amman baa sameta ba hankalin shureim sosai yakara tashi,

hakanne yasa ya tuno da sabuwar dabarar dazatasa abarshi yatafi nigeria

Yau wani ɗan matashin yaƙi ya balle agidan sarki.

Shureim ne ɗauke da wuƙa a hannunshi,ze cakawa kanshi,idan baa barshi yatafi nigeria ba.

duk yadda sarki yaso ya ajiye wuƙar amman ina yaki,maimakon hakama har yafara yanka hannunshi jini na zuba,ya ɗaga ze caka acikinshi kenan,sarki yakwallah kara yana faɗin.

"na amince ka shirya katafi!!!!!"

da gudu ya wular da wukar yaje yarungume mahaifinshi yana kukan farinciki.

A Ranar ofishin jakadancin saudiyya dake nigeria suka bada sanarwar,zuwan É—an sarkin saudiyya sarkin gobe da yardar Allah ze iso nigeria,.

Nan danan fadar shugaban kasa tafara shirin tarbarsa.

Shiko shureim da kyar ya amince se washe gari ze tafi,cikin dare gaba É—aya angama haÉ—a komai na tafiyarshi kama daga escote dade sauransu.

washegari da misalin karfe goma na safe jirgin sama mallakin masarautar saudiyya,ya ɗaga da shureim da maƙarabansa,daga filin jirgin sama na garin zuwa kasar nigeria.

garin masoyi baya nisa.

muje zuwa

surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra Muhammad Mahmud

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

*Kungiyar matan aure na garin bauchi naga sakonku nagode sosai,Allah yasa ku É—ore da aywatar da abunda kuka fahimta a gidajenku,na Aure Ameen*

*dedicated to zahra bukar*

*49-50*

Gaba É—aya titunan dake Abuja jamian tsarone ta ko ina,yayinda helicopters keta shawagi asama.

Ƙarfe biyar na yamma jirgin saudiyya ya sauka a airpot a Abuja.

Shureim ne yafara saukowa,sanye yake da farar jallabiya,ya ɗaura rawanin larabawa yayinda idonshi ke ɓoye cikin baƙin glass.

Tawagar shugaban ƙasace ta iso da sauri,shugaban ƙasa yatarbeshi,tare ds ambasadon saudiyya na nigeria.

Acikin tawagar shugaban ƙasa,Akwai minstan mata,hajiya salbiyya Adam itama taje tarbar shureim,Ministan kuɗi,Hassan Atk shima baa barshi abayaba,can daga gefe nahango tawagar ,Mufarka mata suma sunyo ƙungiya guda ƙarƙashin jagorancin admins ɗinsu,zinnira da Hameeda.

Kalli iya kallonka bazaka taɓa hango ƙarshen masoyan surbajo da suka cika airport din domin tarbo shureim ba.

Kai Abun rukuni rukuni ne,sanda shureim ya ɗags idonsa ya hangi yawan alumar Khaleesat hydar novels,kimanin mutum dubu sabain da uku,sunzo tarbarshi ay kawai se hawaye yafara zuba a idonshi,dan be taɓa tsammanin nigeria haka suke da karrama baƙiba,se yau.

Nanfa jamian tsaro suka kasa suka tsare suka hana kowa isa gareshi.

jerin gwanon motocine suka ɗaukesu zuwa vila,yayinda,Tafeesu novels,da m kaoje novels,da da da da da🤣suka mara musu baya da gudu.

Sabida cunkoson mutanene yasa motocin basa sauri,sun jima kamin suka samu suka isa vila.

Shureim da kyar yayi bacci washe gari ko,yace,anunamishi kano,danshi Azatonshi kusane daga inda yake.

Nande ya fayyacewa shugaban ƙasa abunda yakawoshi,sosai yatausaya masa,hakanne yasa shugaban ƙasa ya umurci minister yada labarai Hajiya Zahra Surbajo yace,tasa afara cigiyar suhaima ta kowacce kafa ta sadarwa,

Kwanaki uku aka kwashe ana sanarwa harda kyautar,kujerar makkah da maƙudan kuɗi gaduk wanda yasanar da ganin suhaima.

Shide shureim gani yake in aka kaishi kanon zefi ganinta da wuri,dan yariƙe sunan kanonne tun ranar da hajiya tabasu tarihinta.

har tsawon sati guda shuru kakeji.

Shureim duk yatashi hankalinsa.

Sabida yace a kano takene yasa aka fo tsaurara bincike abirni da kauyukan kanon.

********

Rabiune zaune A chemist É—inshi yana duba marasa lafiya,yayinda gefe É—aya kuma yake sauraron redio.

Wata murya yaji rangaÉ—eÉ—iya,tafara da cewa.

"Assalamu alaikum jamaa masu sauraro barkanmu da sake saduwa daku acikin shirinmu na filin cigiya da sanarwa,wanda ni Autar hajiya zan jagoranta,A shirin namu na yau zakuji kautukan da akasaka gaduk wand yanemo wata matashiyar budurwa me suna suhaima yar jahar kano,suhaimade ta baro saudiyyane a ranar........ Zuwa gida nigeria,suhaima farace me matsakaicin tsawo,sannan suhaima tana ɗauke da ciki a lokacin tahowar tata,ansaka kuɗi wuri na gugan wuri har naira miliyan goma,da kujerar makkah,ga duk wanda yabada sanarwar inda suhaima take,ga wanda Allah yasa yadace da ganinta,se ya tuntubi minister yada labarai akan nombobi kamar haka,08093235..🤣Allah yabada ikon ganinta akan lokaci Ameen".

jikin Rabiu har rawa yakeyi wajen zaro wayarshi a aljihu,gurin kwafe number,yana gamawa yayi dialing.

ba jimawa aka É—auka,sabida dama layin sabo aka saka sabida hakan.

Nandanan Rabiu yashaida yasan inda take,batare da bata lokaciba yabada Address.

sallamar kowa yayi yanufi gidan su suhaima.

Ayko yaci saa tafito zata tafi tallah kenan.

cikin mutunci suka gaisa,sannan yace.

"Yau kinada babban baƙo,nikuma yau nayi byebye da talauci"yaƙarasa maganar yana dariya.

Itama dariyar tayi,sannan tace.

"wanne irin babban baƙo kuma rabiu?"

"nima wlh bansaniba ammande nasan tabbas yau zamuyi baƙi a garinnan"

"To Allah yasa baƙin na Alkhairine"

"Ameen,sannan yaude don Allah ki haƙura da zuwa tallan nan ni zan siye duka"

Dariya tayi ta É—auka da wasa yake se gani tayi ya sauke abincin yafara bawa yara sadaka,yana gamawa,yaciro kuÉ—inta yabata.

Godiya tayimasa sosai,sannan ta koma cikin gida.

Lantana taji takaicin dawawor suhaima da wuri shiko baffs yaji daÉ—in hakan.

*********

Sanda labarin ganin suhaima ya isa fadar shugaban ƙasa shureim kafa ba takalmi yakwasa da gudu yafita waje dan ya ɗauka anzo da itane.

koda yaga babu ita ido kawai yake zarewa kowa se mamakin irin son da yake mata suke.
Chapter 13 · 0% Book details