← Book details Kano To Jidda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 15

Sashe 10

Kano To Jidda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suhaima tun tana daurewa,kawai seta nufoshi tana kuka tana dukanshi tana faÉ—in.

"Au dariya ma kakemin ko?,kaci amanata da tsohuwar budurwarka amman shine dan ka rainani kazo kasani agaba kana dariya"

Rungumeta yayi yana cigaba da dariyar yana bubbuga bayanta,ita ko kwantar da kanta akirjinshi tayi tana ci gaba da kukanta.

kan kujera yajata suka zauna,sannan ya ɗago fuskarta data jiƙe da hawaye yace mata.

"wlh habibati,ba amanarki naci ba,yakamata ki shaideni akoina ne,ke da kike mazaunin matata,ban kusancekiba,se wata?haba don Allah kizamo meyimin kyakkyawan zato dan girman Allah"daga haka ya kwashe yadda akayi ya sanar da ita.

Rungumeshi tayi tana bashi hakurin fushin data dunga yi dashi.

Harshe yasa afuskarta ya siÉ—e hawayen tas sannan yajata suka nufi kan gado,wasa yashigayi da ita,wanda sun kwana biyu rabonsu da hakan.

Suhaima ita har mamakin yadda shureim yakeson boobs É—inta takeyi,kowanne motsin idonshi da hannunshi na kansu.

seda suka jiyar da junan su daÉ—i ta hanyar wasannin da sukeyi sannan suka fito falo inda suka tarar kafilat tayi kaca kaca da fulo É—in kan kujerun,gyarawa sukayi,sannan suka nufi dinning shureim yaciyar da suhaima abinci.

Bayan sunyi sallar ishai gidan su shureim suka nufa,cikin shiga ta ƙasaita,seda suka tsaya ahanya suhaima tasashi yasiya mata turarukan da zata ba sarki da ummi.

Mahaifiyarshi tayi murna da ganinsu,se nan nan takeyi da suhaima,da suhaima ta bata turaren data siyo mata baƙaramin daɗi tajiba.

sunjima suna hira da ummin sannan suka shiga gurin sarki,shima yayi murna da ganin su sannan yacewa shureim

"kai ni jiya mahaifin kafilat yakirani yana cemin wai tun washegarin auranka,kafilat ta shaida mishi wai ka kira ta akan cewa wai tazo ta taya matarka zama agidanta kamin tasaba da gidan,meye gaskiyar maganar,gab É—aya kaina ya kulle".

Daga Shureim har suhaima suma kan nasu ya kulle,da kyar shureim yace.

"Abba wlh ba haka bane,muma ganinta kawai mukayi tazo,koda n tambayeta me yakawota,cewa tayi ta tambayi mahaifinta zata zo hutu gidana shine ya amince mata,nikuma jin da yardar mahaifinta tazo ne yasa ban koreta ba,yanzu haka tana gida mun barota"

"wannan ay shashancine,a ina aka taɓa yin haka,katuwa da ita zataje ta tare agidanku,to maza maza in gari yawaye kace injini nace tabar gidan ta koma ƙasarta ko kuma na fayyacewa mahaifin nata gaskiya game da ƙaryar datai mishi"

"Abba tunda kaga tazo ta zauna damu dan raayin kanta inaga abarta ta tafi dan kanta base an koreta ba"cewar shureim.

"Ban aminceba,sam ni ban yarda da zamanta agidanka ba,sabida ina jiye maka karta haddasa maka tashin hankali da rigima acikin gidanka kaida iyalinka"

"insha Allahu ba abinda ze faru,kawai abarta,ni banso ayi abinda ze janyo kace nace ne kabarta kawai Abba,zanyi iya bakin ƙokarina gurin kiyayewa"cewar shureim.

Shuru Abba yayi naÉ—an likaci sannan yace.

"yace to shikenan Allah ya kauda fitina,amman lalle ka kula da kyau"

daga haka hira suka É—an taba ganin dare yayi ne yasa suka masa sallama,shima da suhaima ta bashi turaren sosi yaji daÉ—i yadunga samusu albarka.

koda suka isa gida tana zaune a falo kamar mayya.

Tunda ta amsa sallamarsu batacemusu komaiba,suma basu cemata ba suka haura sama abinsu zuwa É—akin shureim.

muje zuwa.

Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra Muhammad Mahmud

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION.

*Dedicated to Zahra Bukar*

*39-40*

Koda suka shiga ɗakin kan kujera shureim yaje ya kwanta hannunshi riƙe da marar shi ya runtse ido.

Kwanaki biyu kenan yanajin alamun ciwonshi ze tashi,ga suhaima kullum cikin jin tsoronshi take,shiyasa kawai yake daurewa.

Suhaima kayan jikinta ta rage sannan ta shiga toilet ta haÉ—a musu ruwan wanka tafito ta nufeshi.

Zama tayi kusa dashi,tun kan tayi magana,taji hucin zazzaɓin daya rufeshi.

Da sauri takai hannunta jikinshi,tana tambayarshi abinda ya sameshi.

"habibati,wannan ciwon shekara guda kenan ina fama dashi,likitoci sun shaidawa mahaifina se anmin aure tukuna zan warke,shine dalilin dayasa Abbana ya auramin ke amatsayin matata"shureim ya faÉ—i da kyar.

👀suhaima ta waresu,tsorone ƙarara ya bayyana akan fuskarta,bakinta har rawa yake gurin faɗin.

"to ay gashi ammaka auran meyasa yatashi kuma yanzu?"

"ay badaga auran zan warkeba sena sadu da matar sannan zan samu sauƙi,don Allah kibani hakkina suhaima kicire jin tsorona ki tallafeni don Allah"ya faɗi yana rungumota jikinshi.

Da sauri ta kwace daga riƙon daya mata tamiƙe tsaye,tana faɗin.

"wato idan na fahimceka auran kauda shaawa aka yimana nida kai,danƙari,ayko anyi abanza,dan baze yiwu na amince dakaiba daga baya ka gujeni,tunda bukatarka ta biya"

Idon shureim tuni sun kawo ƙwalla sabida azabar ciwon dayakeji,ga kuma ɗacin da kalaman suhaima suka masa.

Da kyar yace.

"ina last stage ne suhaima,kiyiwa girman Allah kizo gareni"ya ƙarasa maganar hawaye na zuba a idonshi,

Mirsisi suhaima tayi bata da niyyar zuwa dan gani take kawai in ya kusanceta ze saketa ne.

Ganin suhaima bata da niyyar zuwane yasa shureim miƙewa da kyar,yana haɗa hanya yanufi hanyar ficewa daga ɗakin.

Da sauri suhaima tasha gabanshi tace.

"To kai da baka da lafiya,ina kuma zakaje cikin darennan"

Rai aɓace yabata amsa.

"ba ke kaɗai bace me abin bani nasamu sauƙi,kinfi kowa sanin akwai kafilat agidan nan,kuma nesa ba kusa ba nasan tafiki sona,bazata so taganni awannan halin bata taimakeniba,zanje gurinta ta biyamin buƙata,bantaɓa aykata zinaba,amman yau ke matata ta aure kince naje nayi,to zani amman ki tanaji amsoshin da zakiba Allah ranar da kika isa gareshi"be jira me zata ce ba yayi yunkurin ficewa aɗakin.

Da wani mahaukacin sauri suhaima ta ruƙoshi tana kuka tana faɗin.

"wlh bazakaje gurintaba,wlh bazaka ba"

"zaki bani naki ne?"

"nide bazan bakaba amman kuma ita ma bazaka gurintaba"

"ayko ba abinda ze hanani zuwa wlh matukar ba naki kika bani ba"

"wayyo Allah na,to kai kayi haƙuri kaɗaure mana,da safe sekaje asibiti"cewar suhaima

"mutuwa zanyi inna haƙura,gashi ni kuma ban shiryama mutuwa yanzuba,dan haka kisakeni in wuce"

Tawul ɗin dake jikinta ta kwance ya faɗi ƙasa,tana kuka tana faɗin.

"na amince sede inka gujeni bazan yafe maka wlh Allah se yasakamin"

wani daÉ—ine yakama shureim,dan dama koda ta barshi yafita ba gurin kafilat zashiba É—akinta zeje ya kwanta,sanin tana da kishine yasa yayi amfani da sunan kafilat.

"ni mesonkine,bazan taɓa gudunkiba har abada insha Allahu"

Tundaga haka labarin yafara canjawa,yafara kissing É—inta har suka isa kan gado.

wasa yake da duk wata gaba ta jikinta,sannu a hankali yake surcking boobs ɗinta,yana shafo ƙasanta at the same time.

suhaima dirar hannun shureim kasanta,sosai takejin daÉ—in hakan,dan haka tuni duk wani tsoro wannan daÉ—in ya kauda shi.

biye mishi tayi suna ta wasa da juna,bata fargaba seda taji shureim abakin boda yana shirin tsallakawa,azabar datajine ya fargar da ita.

ihu tasa mishi,tana roƙonshi ya kyaleta,kanshi ya ɗora kan fuskarta ya haɗe bakinsu guri ɗaya,yayi maganin ihun nata.

Sannu a hankali yake shigarta sabida gudun yajimata ciwo,itako,duka yakushi,babu wanda batayimasa ba amman yaki saurara mata,dan ita É—auka tayima mutuwa zatayi.

Buƙatar maje hajji sallah,shureim ya angwance da suhaimarsa,cikin daɗi,yayin da itako,inbanda kuka ba abinda take masa,sabida ita kaɗai tasan azabar dataji,take kan jima.

Shureim tunda yasamu natsuwa ko motsi yakasa yi,kwance yake yayi rub,da ciki kukan suhaima na shiga jikinshi so yake ya rarrasheta,amman abun yaci tura.

Da kyar yamika hannu yajawota jikinshi yarungume yana jijjigata.

ko a lokacin bata dena kaimishi duka ba,hawayene ke fita a idanun shureim na godiya ga Allah daya halatta aure,da kwanciyar aure,abinda yaji game da suhaima bakinshi baze iya faÉ—i ba,illah iyaka yashiga samata albarka,

Yayinda gefe É—aya kuma wata zazzafar kaunartace tasamu matsuguni scikin zuciyarsa,yanajin baze iya rayuwa ba inbabu ita.

ÆŠaukarta yayi yaje ya wanketa tsaf shima yayi,sannan sukayi wankan tsarki suks fito.

Kan kujera ya ajiyeta sannan ya kwashe zanin gadon da suka ɓata,ya shimfiɗa musu wani,ya ɗauketa yamaida ita kan gadon,ya kwantar da ita,ya rufa mats bargo.

Shiko sallah yashigayi na godiya ga Allah,yajima yanayi,sannan yashafa,yamike yacire doguwar rigar daya saka,yaje yashige cikin bargon yajanyota jikinshi,suka ci gaba da baccin.

koda gari ya waye,zazzabine ya rufe suhaima,idonta duk sun kankance.

Hankalin shureim atashe yakira doctor É—inshi yamishi bayani.

Amsa yabashi da gashinan zuwa,gida yadubata.

Su suhaima iyayen raki bare kuma an taɓota,ayfa hawaye kawai take,koya yatabata seta sake rushewa da kuka da ƙyar ta yadda yayo mata wanka yazo yashiryata acikin doguwar riga,yasa mata hula akanta.

shima wankan yashiga agurguje,yafito dan beso yabarta ita kaÉ—ai,shiryawa yayi shima yakoma bakin gadon ya É—ago suhaima ya kwantar ajikinshi,se albarka yake sa mata.

Doctor yana isowa da kafilat yaci karo a falon,gabatar mata da kanshi kawai yayi,sannan yashaida mata megidanne yace yazo.

waÆ´a yaciro yakira shureim ya shaida mishi gashi yazo.

shureim miƙewa yayi ya ɗauki suhaima suka sakko ƙasa,

idon kafilat kamar zasu faÉ—o gurin kallon su shureim.

Bayanin komai shureim yasake yiwa likitan,nan take likitan yaÉ—an gwada yanayin zafin jikin yabata magunguna harda wanda ze rage mata zafin da takeji.

Sallama yamusu yawuce,shiko shureim ko ta kan kafilat be biba ya É—auki matarshi,suka haura sama.

Tashin hankali baa samaka rana,kafilat sabida tsananin bacin rai,gashin jikinta har tashi yake,idanunta sukayi ja.

kuka takeyi tana faÉ—in.

"kunyi naku saura nawa,narantse da wanda yabusamin numfashi sena rabaku,koda kuwa hakan na nufin yankewar numfashina a duniyane"

tofa🤔

muje zuwa

surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra Muhammad mahmud

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

*Dedicated to Zahra Bukar*

*41-42*

Tundaga wannan lokacin shureim ya É—auki son duniya ya É—orawa suhaima,

Koda ya koma bakin aykinsa,tare da ita yake tafiya,dan gani yake in bayanan kafilat zata cutar masa da ita,dayake office dinshi kamar gida haka akayi tsarun to,seta zauna aciki shikuma yaci gaba da aykinsa,baya minti ashirin seya leƙata.

Kafilat ji take kamar ta kashesu kowa ya huta.

Da kyar suhaima ta lallaɓa shureim yadunga kyaleta agida,da kyar ya amince.

Soyayya ko nunama junansu sukeyi ko a inane,yanzu suhaima abincin shureim kawai take dafawa,dan tuni shureim ya ayka an kawo musu mata guda uku masu ayki,É—aya ta dafa abinci,É—aya shara da mopping,É—aya kuma wankin kayan suhaiman da guga.shureim namijine ke masa nasa.

Kafilat ganin Suna shirin samata hawan jinine yass ta rage zama inda suke.

Daga ƙarshema seta dena wuni agidan,suko ko ajikinsu.

A wannan tsakankaninne suhaima tafara laulayin ciki,tunda shureim yasamu ƙabarin cikin yakoma wawa akan cikin,dan ze iya kwashe awa guda yana magana da abinda yake cikin,so da kaunar da yake nunawa cikin ta wuce tunanin me karatu.

Tunda tasamu cikin se yakasance batason shureim ya kusanceta,shureim bedamuba,dan yasan ciki nasa mata suyi abinda yafi hakama.
Chapter 10 · 0% Book details