← Book details Kano To Jidda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 15

Sashe 14

Kano To Jidda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dakyar ya kimtsa,aka hsɗashi da jamian tsaro suka hau jirgi zuwa kano,daga kano gomnatin kano tashirya mishi motoci na alfarma,ana bugamasa jiniya,ƙarƙashin rakiyar minister yada labarai zahra surbajo,da shi kanshi gomnaɓ kanon,suka nufi garin lamin kwai.

muje zuwa.

Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra Muhammad Mahmud

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

*Wayyo masoyana kuyi haƙuri surbajo nasonku aduk inda kuke,nafeesa Abdullahi,baze yiwu surbajo tasa numberta a page ba sede ke ki rubuto taki kituro, da yardar Allah zata iso gareni,bama keba duk wani masoyina dayakeson hulɗa dani ya rubuto numbersa yaturo,zasu iso gareni kuma insha Allahu zan nemeku,banaki saka number na bane dan tsoroba kawai de dan jaddada tsarone nagode*

*dedicated to zahra bukar*

*51-52*

Duk inda suka wuce kallonsu akeyi,sabida motocine sunkai guda Ashirin jere akan titi.

Sannu a hankali suka iso garin na laminkwai,dan haka sauka sukayi akantiti,sukabi jar ƙasa zuwa cikin garin.

Wuyan shureim kamar ze tsinke sabida ƙara masa tsawo dayakeyi.

Yan garin sunga abun da basu taɓa ganiba,sabida suna hawa titin jar kasar lamin kwai ɗin,

Escote suka firfita daga motocinsu suna gudu aƙafa,motar da shureim yake ciki kuwa,escote ɗin larabawa kowa sanye da bakaken suit,fuska manne cikin bakin glass,kunne maƙale da bluethood,hannu ɗaya cikin riga riƙe da bindiga.

Wallahi koni tsarin yaminni.

Mutanan garin kiÉ—imewa sukayi,ganin fararen fata a ayarin tafiyarne,yasa alumar garin fara rawar murna.

Domin a tunaninsu man fetur ne a garin nasu,shine akazo a haƙo,yayinda wasu kuma tunaninsu yafi karkata akan service ne ya faɗo garin.

Hakanne yasa kowa ya shiga adduar Allah yasa agidansa ya faÉ—o.

acikin masu tunanin service É—inne harda lantana,addua tayita ba adadi akan Allah yasa a gidansu ya faÉ—o.

Suna isa garin ƙofar gidan me gari suka tsaya,dama tuni rabiu yana binsu abaya.

me gari rawaninshi har yana faɗuwa sabida kiɗima,danshi azatonshi yan taadda aka gano a ƙauyen nasa.

Nan aka buɗew su Shureim ƙofa suka firfito,shureim kallon garin kawai yake yana mamakin ta yadda suhaima zata iya rayuwa acikinshi.

Number rabiu aka fara kira da sauri yafito tsakiyar filin,yana É—aga hannunsa.

kofar fadar me gari kuwa tacika damƙam da mutane yan ganin kwakwaf su lantana ne agaba gaba,ta baro suhaima gadin gidan.

Shiko baffa bayanan yaje É—aurin aure kwanar É—angora,na yarinyar abokinshi.

Shureim ganin rabiu amatsayin wanda yasan inda suhaima take da sauri yakamosu ya riƙe yana tambayarshi tana ina.

Duk yadda akaso ya kwantar da hankalinshi abun yaci tura,dayake gurin akwai hayaniya shiyasa baa ji me suke faÉ—iba.

Ba musu Rabiu yamiƙe yayi gaba,su shureim suka mara masa baya,escote sojoji yan sanda,duk sun rufu akan shureim haka suka nufi gidan su suhaima aƙafa dayake ba nisa.

Suma zugar jamaar gari sesuka mara musu baya,dan gani karshen alewa.

Ay lantana tunda taga anyi hanyar gidansu ta runtuma da gudu har faÉ—uwa take tana tashi dan ita duk azatonta service É—inne ya faÉ—o a gidan.

Har suka iso ƙofar gidan tun kan,ayi magana lantana ta ware murya tana faɗin.

"Allah mungodema service a gidanmu,to gaskiya mude ba siyar muku zamuyiba sede mubaku haya duk shekara"

ba wanda yabi ta kanta,Rabiu nashirin shiga gidan kiran suhaima se gata ta ɓullo daga wata kwana ta dawo daga gidan su hanne ɗebo shanyarta.

Shureim yatambaya to ina takw.

Rabiu cike da faraa yanuna masa suhaima dake tafiya kanta aƙasa burinta kawai ta shige gida,.

Ay ko acikin mayen giya inyaganta ze ganeta,da gudu yaje yasha gabanta escote nabinshi abaya,suhaima bata luraba sekawai jinta tayi aƙirjin mutum.

ƙamshin turarensane ya shaida mata ko waye ya rungumetan amman sabida ta tabbatar ne yasa ta ɗago idonta dan ganin shiɗinne ko kuwa.

Tana É—ago ido ta saukesu akan fuskar shureim dake zubar da kwallah,aruÉ—e take kallonshi,tana tunanin tayadda akayi yazo.

Kamin tayi wani yunƙuri se ganinshi tayi tsugune akan guiwarshi agabanta,ya haɗa tafin hannunshi guri guda yana kuka yana neman yafiyarta.

Jikintane yakama bari bakinta narawa sanda ta waiga taga dubban mutanen dake gurin,dansu yasmin tafeesu da sally da queen aeanah,da bilkisu u hamza,kan wata karamar katanga nahangosu suna kallon ikon Allah.

Suhaima tausayin shureim ne ya ziyarci zuciyarta,ganin yadda bedamu damasu kallonshiba,bedamu da matsayi da mukinsaba yazube akan jar ƙasa agabanta yana kuka.

itama tsugunawa tayi,ta haÉ—a goshinta da nashi suna kukan,a haka shureim yake neman gafarar ta kai kawai take É—aga mishi alamun ta yafe mishi,sabida tsnanin murna jawota yayi jikinshi ya rungume yana kukan murna,a hankali yake shafo cikinta,jin hakan ne yasa ta fahimci cikin jikinta yake nema.

Hannunshi tajs suka shige cikin gidan.

wayyo lantana rasa abunyi tayi,har bigewa takeyi gurin bin bayansu zuwa cikin gidan.

Tawagar gomna fadar megari suka koma,suko sauran mutane so suke suji waye shureim agurin suhaima.

Ayko nafa rabiu yashiga masallaci yasa lasifika yana shaida musu mijin suhaima uban yayantane shureim,

lantana seda cikinta ya karta dan kiÉ—ima.

Suhaima riƙe da shureim har zuwa ƙofar ɗakinta inda su twins ke zaune a tsakar ɗakin suna wasa da kayan wasansu.

suna zuwa taimasa nuni dasu.

Suko kamar sun sanshi atare dukansu suka rarrafo zuwa gareshi.

kallon suhaima yake yana kallonsu,jikinshi kamar mazari yazube aƙasa suka ƙaraso jikinshi.

rungumesu yayi ƙanƙam ajikinshi,sannan ya kife kanshi aƙasa yayiwa Allah sujjada,yana kuka yana fadin.

"Astagafiruka wa atubu ilaika ya ilahil alamin,"

kuka yake sosai a sujjadar,seda su twins suka fara kukan sungaji sannan ya É—ago.yana jijjigasu,suko se shafa bakinshi suke irin wasannan na yara.

Sumbatarsu kawai yake yana dariya.

lantanace tazo ta tsaya akan su ko kunya babu,ganin hakane yasa suhaima taja shureim suka shige cikin ɗakinta ta turo ƙofar,.

muje zuwa

In banga dogon comments ba anan zan tsaya

surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra Muhammad Mahmud

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

*ATTENTION‼*

*DA WACCE TAYI DAME SHIRIN YI YANZU,SHARE NA HOTUNANA,WALLAHI DUKANKU BAN YAFEMUKU BA,INA ROKON ALLAH YA DORAMA DUK WANDA YAYI MASIFAR DATA FI KARFINSHI,SABIDA KUN CUTAR DANI CUTARWA MAFI MUNI,WALLAHI BANYAFE MUKU BA KUMA BAZAN TABA YAFEWA BA,ALLAH WADARAN MUNAFUKI ME FUSKA BIYU,KODA DAGA YANZU KUNDENA KARANTA LITTAFINA,ZAN MAIMAITA,ALLAH YA ISA BANYAFEBA,BURINKU BE CIKABA SABIDA SON DA MIJINA YAKEMIN BABU DIGON MUNAFUNCI ACIKI,NABARKU DA RABBUL ARSHIL AZIM,ALLAH KABIMIN HAKKINA😭*

*dedicated to zahra bukar*

*53-54*

Wani bakin cikine ya tokari zuciyar lantana,

Memakon tabar gurin kujera tajawo ta zauna ta kasa kunne abakin kofar dan taji me zasuce.

Shiko shureim bin dakin kawai yake da kallo yana tunanin dkin kwanane koko dakin aje tarkace,kasa yin shuru yayi dubansa yakai gurin suhaima yace.

"Habibati me kukeyi anan bakya tsoron ginin ya fado akanku zaki barsu anan?"

Murmushi tayi sannan tace.

"wannan dakina kenan,tunda ka koreni acikinsa nake rayuwa,har zuwa sanda na haifi yayanka muka ci gaba da rayuwa tare aciki"

Ajiye su twins yayi ya jawota jikinshi ya rungume yana kuka,yana kar neman gafarar ta.

"hbibati ki yafeni,na cutar dake sosai wannan dakin da garin da jahar da kasar gaba daya basu dace dake ba,ko baki fadamin ba habibati jikinki ya nunamin kina cikin wahala da kunci na zamanki anan,ki gafarceni"

Itama kukan takeyi,suna rungume da juna,

Bakinciki karuwa yayi agurin lantana sabida abun da taso ji takasa jin sabida bada hausa suke .maganarba.

Su twins ganin iyayensu na kuka ne yas suma suka fashe da kukan.

Da sauri suka saki juna suka daukesu suna musu wasa.

Ranar gari ko ina yaÉ—auka suhaima mijinta yazo dan sarkin makkah.

koda tawagar gomna da minister suka buƙaci shureim yataho su tafi fafur yaki acewarshi,se ya ɗandana irin zaman da iyalinshi sukayi agarin.

Hakanne yasa aka baza jamian tsaro lungu da sako na garin,kofar gidan su suhaima ko cincirundon jamian tsarone.

Se da magriba baffa yashigo garin,ganin jamian tsaro ta koina har tsoratashi yayi,sanda ya iso kofar gidanshi ko ba karamin mamakine yakamashi ba,ganin an tsaidashi ana checking dinshi sekace barawo.

Seda suka gama bincikeshi tas sannan suka barshi yashiga cikin gidan.

A tsakar gida yasamu lantana,se safa da marwa takeyi.

Tana ganin shi tayi sauri ta nufeshi tana fadin.

"Gwanda da Allah yakawoka,to ga yarka nan da wani kato acikin daki suna iskanci,nayi nayi su bude kofar sunki"

Cike da mamaki yake kallonta,dan shi gaba daya kanshi ya kulle.

suhaima jin sallamar baffane yasa ta shaidawa shureim ga mahaifinta yadawo,dan haka buÉ—e kofar sukayi suka fito,gurinshi suka nufa.

Baffa ido kawai yake warewa na ganin balarabe a gidanshi,kallonshi yake kallo irin na kurullah,take ya hango kamannin Jikokinsa a fuskarsa,baki na rawa yace.

"suhaima ko baki faÉ—aminba wannan shine uban su yan biyu wanda yamiki cikinsu"

Cike da faraa tace.

"Baffa wannan shine babban dan sarkin saudiyya,kuma shine ake sa ran zamanshi sarkin kasar bayan mahaifinshi,aykatau naje gidansu,mahaifinsa ya haÉ—ani aure da shi har muka smu cikin su twins,to wata yar rashin fahimtace ta shiga tsakanina dashi,shine dalilin dayasa nadawo gida,to gashi yazo nemana da kanshi yanzu"

"kan bura uba,wlh da sake,karya kike bakar munafuka,mu zaa munafunta,agidan ubanwa balarabe yake aurar bakar fata,ay dan sarki ko na lamin kwai ne yafi karfinki bare na kasar da babu irinta,kice kawai farkankine yayi kewarki yabiyo bayanki"cewar lantana tana wani jijjige jijjige

Akaro na farko da suhaima tayi shaawar ba lantana amsa,inda tace

"To ay dama lantana inkika dubi tsarina,shi kanshi dan sarkin laminkwai din yasan nafi karfinshi,ki dubeni da kyau ko amasarautar kano sede kaddara,dan srkin saudiyyan de shine daidai dani,kamar yadd kika gani,kuma koda ace farkanane shi,ay ina ga ya cancanci yabo tunda har yasan mutunci bariki ya iya biyoni har nan koda kuwa kowa be yaba masa ba kede yadace ki yabs,sabida ya nuna sanaarki tada tana da muhimmanci"

Lantana tsananin mamakin suhaimane ya hanata magana binta kawai take da ido.

Shureim gaida baffa yayi suhaimace ke fassara masa,cike da mutunta juna suka gaisa.

lantana dakinta tashige jiki a sanyaye dn bata taɓa tsammanin suhaima tasan ita tsihuwar karuwa bace,gaba daya ji tayi ta gama tozarta.

Se dare suka bar gurin baffa suka nufi É—akin suhaima,shureim dama shi duk ya kosa subar gurin,sabida wasu kwari dasuke cizonsa dabesan kona meneneba(sauro)

suna shiga dakin pampers suhaima ta sauyawa su twins tasamusu over roll ta kwantar dasu akan katifunsu masu gidan sauro,dama tun suna gurin baffa suka fara jin bacci dan haka suna kwanciya baccinsu sukayi.

Shureim duk inda suhaima tayi binta yake da ido,wata zazzafar shaawartace ta kamashi,yakos yajita ajikinshi.

katifarta ta fara gyara musu tan É—aura gidan sauro sabida sauro tagama daura gidan sauron kenan shureim yagaza hakura,ya jawota ta fado jikinshi.
Chapter 14 · 0% Book details