← Book details Kano To Jidda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 15

Sashe 2

Kano To Jidda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nanfa mutane sukai ta shigowa,bakin baffa yaki rufuwa kowa yazo se yace mishi suhaimace ta kashe uwarta.

Wata ce ta dibi ruwa ta watsawa suhaima ta farfaÉ—o,kuka takeyi gwanin tausayi,haka tanaji tana gani aka haÉ—a mahaifiyarta aka mata sallah akaje aka birne ta.

Duk me imani yaga suhaima seya tausaya mata,lokaci guda tafita hayyacinta,in banda kuka ba abinda takeyi.

Shiko baffa memakon yayiwa matarshi addua se lantar suhaima yake,wai takashe mishi mata.

Haka akaita zaman makoki har akayi arbain din innah suhaima bata koma daidai ba.

***************

Bayan wata uku da rasuwar inna,baffa ya haÉ—u da wata bazawara me suna,Lantana ya aureta.

Lantana,irin tsofaffin karuwan nanne,dan haka tana shiga gidan baffa,balai ya karu akan na da agurin suhaima.

Komai na gidan ita takeyinshi,dan har cikin dare turata dam din daurawa takeyi ta É—ebo ruwa,gashi da nisa atsakaninsu,haka zata kwana ahanya,dan ko amashin ne zaka seka biya naira dari koma fin haka,bare suhaima ga jarkunan ruwa har guda uku haka take turata.

Baffa be taɓa kallon hakan amatsayin cutarwa ga rayuwar yartashi ba,sema daɗi dayake ji.

Tuni tadena zuwa makatantar Allo,shinkafa da wake lantana take dafa mata ta turata talla.

ga suhaima me kan tallah ce tana fita yake ƙarewa,hakanne yasa lantana komawa dafa mata rabin buhu,da safe takai garin Kiru,da rana kuma takai kwanar dangora,da yamma takai yako.

ba irin wahalar da suhaima batasha,kuma duk da wannan wahala mahaifinta ko gaisheshi tayi baya amsawa,sedema yarufeta da duka,ko so ɗaya lantana bata taɓa cetonta ba.

Ana haka ne wani ƙanin lantana yazo daga garinsu,murna gurin lantana kamar me,shima baffa yayi murna da zuwan salele,ba kaɗanba.

To dama gidan É—aki biyu ne,É—aya na suhaima,É—aya kuma baffa da lantana,dan haka koda dare yayi baffa dakanshi yakai salele É—akin suhaima wai yadunga kwana aciki,kamin yatafi.

Suhaima ido kawai take warewa ganinta kwance da shirgegen ƙato a shimfiɗa ɗaya.

Koda baffa yafita adakin,salele zuwa yayi ya kulle ƙofar,sannan yazo kusa da suhaima yakwanta.

Cikin dare suhaima ta farka taga salele yacire mata riga,se matse mata kananan nashanunta yakeyi,wainda farkon fitowarsu kenan,se zafi suke mata.

Da sauri tamike zaune tace bakinta naraw.

"meyasa kakeson zubarmin da mutunci don Allah,?"

Dariya yayi sannan yasake shafota yace .

"sabida mahaifinki be nuna ke me mutuncin bace,tunda ya iya haÉ—ani dake mukwana guri É—aya"

Kuka suhaima tasa mishi tana bashi hakuri amman ina salele,se kokarin rabata da duka kayanta yake,Cikin saa suhaima ta kwace a hannunshi tafita tsakar gida tana kuka,

Da gudu baffa da lantana suka fito.baffane yace.

"dan kan uwarki meya faru kike ma mutane kuka tsakar dare?"

Baki narawa suhaima tace.

"Baffa salele ne yaciremin kaya yana son yin lalata dani"

Carab lantana ta amshi maganar.

"kaji munafuka,lokacin dakike rabawa yan tasha,ubanwa kika yiwa kuka,se yanzu dan sharri irin naki zakice wai salele,ni inbanda masifa irin ta salele ubanme zeyi dake".

Baffane yakarasa inda suhaima take yarufeta da duka,seda yamata lilis,sannan ya hankaÉ—ata É—akin da salelen yake ciki,yace.

"Bakar munafuka,kyayi kya gama,yanzu kuma sharri kika zo dashi to wlh munfi ƙarfinki,"daga haka suka juya ɗaki shida lantana suka rufo ƙofa.

Salele murna ce takamashi dan haka yanufo inda suhaima take tsugune tana kuka,itako tana hangoshi,ta kwasa aguje,tafice ma daga gidan,.

Gudu take ba kama hannun yaro,har ta isa gidansu wata hanne ƙawarta,kuma maman hannen tana da kirki,baban hannen ya rasu,

Dayake gidan kauye bakowanne keda murfi ba dan haka shigewa gidan suhaima tayi tabaje atsakar gida,koda salele yabiyota be ganta ba dan haka yakoma gida yana huci.

A tsakar gidan suhaima ta kwana ko riga babu ajikinta,da asuba maman hanne ce tafara fitowa,koda taga mutum kwance tsakar gida abunka da mutanan karkara basu da tsoro kanta tsaye taje gurin tana tambayar waye.

Farkawa suhaima tayi,ganin innar hanne ne yasa tafashe da kuka tace.

"inna nice suhaima"daga gaka takwashe komai ta faÉ—awa innar.

tsananin tausayin suhaima ne yasa inna kuka,kamota tayi ta rungume race cikin kuka.

"kiyi haƙuri suhaima insha Allahu,nan gaba zakiga amfanin rayuwarki,kibarwa Allah komai,yana sane da halin da kike ciki"

Daga haka daki takaita nan hanne taita kuka na tausayin kawar tata,kaya tabata tasauya bayan tayi wanka,tayi sallah taci dumamen tuwo,sannan tanufi gidansu.

A tsakar gida tasamesu duka suna karyawa,bawanda yadamu da ita bare yatambayi daga ina take.

kayan tallan ta ta É—auka tafice,zuwa kiru,bayan ta amshi kuÉ—in mota ahannun lantana.

Da misalin ƙarfe,goma na safe bayan tafiyar suhaima talla,hajiya zaituna me makkah me dubai,ta bayyana a garin na laminkwai.

Gida gida take bi tana haɗa kan yanmata wainda iyayensu suke da shaawar akaisu saudiyya aykatau,ayko duk inda tashiga kowa yaƙi bada yarsa,ahaka harta shigo gidansu suhaima.

Da faraa lantana ta karɓeta,koda hajiya zaituna tamata bayanin abinda yakawota ba ƙaramin daɗi tajiba,suna cikin tattaunawa,suhaima ta dawo daga tallah.

Nan take lantana tace hajiya ta tafi da suhaima ta bata,lokacin mahaifin suhaima bayanan haka lantana ta yanke hukunci.

Dubu É—ari hajiya taba lantana,ay ji tayi kamar ansata a aljanna,murna da godiya har kasa.

cikin masifa lantana tasa suhaima haɗo kayanta,kuka suhaima takeyi tana ba ta hakuri amman taki sauraronta,daga ƙarshema ta rufeta da duka.

Ganin zasu bata mata lokaci ne yasa hajiya zaituna cewa tabar kayan,insunje zata saimata wasu,

haka suhaima tanaji tana gani suka sata a motar hajiya zaituna,ita kuma takulle taja suka tafi.

Koda baffa yadawo lantana tabashi dubu hamsin sannan tace.

"dayake naga harkar ƙaruwa ce shiyasa nabada ita,nan kano zaa kaita tadunga aykatau,duk bayan wani lokaci zatazo ganin gida"

baffa ko damuwa beyiba yashiga sawa lantana albarka.

Suko mutanan gari,gaba É—aya kowa yaÉ—auka antafi da suhaima karuwanci.

koda labarin yazo kunnen baffa ko damuwa beyiba dan yasan hassadace.

Tun suhaima tana kuka har tadena,haka sukaci gaba da tafiya hajiya najanta da hira.

ga sanyin ac yana busata ay suhaima batasan sanda bacci ya É—auketa ba,har suka iso kano,anguwar hotoro kwanar maggi bata sani ba.

muje zuwa.

surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra Muhammad Mahmud

*maki gani ya kauda idonsa*

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

*umeeeeeeeeeh naga sakonki nagode Allah yabar zumunci*

*DEDICATED TO ZAHRA BUKAR*

*7-8*

Koda hajiya zaituna tayi parking suhaima bata saniba seda ta tasheta,a firgice ta farka.

Haka hajiya tajata zuwa cikin gidan,suhaima se kauyanci takeyi,sabida shine karon farko na shigarta birni.

Koda suka shiga falon yanmata ne ajere su tara,se wata babbar mace atsaye agabansu tana koya musu wani abu,koda suhaima ta lura dakyau ashe tafiyar jan hankali ake koyar dasu.

Ganinsu ne yasa matar zuwa gurinsu tana faraa tace.

"me makkah me dubai,ina kika samo mana,zuma farar saƙa kuma?"

Dariya hajiya zaituna tayi sannan tace.

"hmmm kede bari uwar mabukata,wlh can wani kauye na siyota afarashi dubu É—ari,gatanan na kawota,nasan zamu samu dubunsu ajikinta,sabida inkin lura yarinyar akwai kira,"

Dariya uwar mabukata,tayi sannan tasa hannu ta shafo gefen fuskar suhaima wacce tunda suka fara magana take ware ido kamar tsohuwar mayya,sannan tace.

"zancanki gaskiyane,nasan in ta isa birnin jiddah,duniyar sama zata gyarata dakyau kamin tasata akasuwa,dan haka yanzu kije da ita amata e pasport,dan banaso suyi sati akasa batare da an aunasu can ba,kuma kinga ƙafarta akwai kaushi,ga kanta se tsami yake,ki kaita saloon akauda komai,dan kinsan halin duniyar sama batason akaisu ahaka"

Tafawa sukayi,sannan hajiya zaituna tace.

"naga yar sudan nanan dan haka in mun dawo daga saloon din zankaita can abata kayan mata,dan ta jiƙu dakyau sabida kinsan larabawan nan,basason suji rani,sunfiso kullum cikin damuna"

wata uwar shewa sukayi sannan hajiya zaituna tayiwa suhaima umarni data taso suje,ba musu suhaima tabita sabida bata gane manufar zancensu ba.

Gurin gyaran kafa da gyaran gashi takaita aka gyara suhaima,segata tafito fes da ita.

gurin pasport sukaje nanma akayimata.

Daganan gurin me maganin mata suka dire,nan taita É—irkawa suhaima magunguna,akan dole suhaima takesha duk da batasan maanar su ba amman tanaji aranta ba abun cutarwa bane.

harda na tsugunawa seda suka mata,basu dawo gidaba se shaÉ—aya na dare.

Tunda aka kawo suhaima gidan,kullum ake koyar dasu salon tafiya,da karayraye karayraye,da fari da ido,kuma tsab suhaima dama yana daga nature É—inta dan haka be bata wahala ba ta iya.

Ba kalar fitsarar da baa koya musu ba.

sati guda tsakani,jirgi ya É—aga da su suhaima from kano to jiddah.

Dukansu a tsorace suke barinma suhaima dahar kuka tadunga yi na tausayin kanta.

Awar su huÉ—u asama,suka iso jiddah.

Dayake basu da wani kaya,basu sha wahalar komaiba,aka buga musu,stamp na shaidar sun shiga ƙasar saudiyya.

Suna fitowa,suka tarar da wata hamshakiyar hajiya wacce dagani duniya na gara mata,gurinsu ta nufa tana yatsina tace.

"sunana duniyar sama,ina fatan kune hajar danayo order?"

Dayake anfaÉ—a musu sunanta dan haka baki suka haÉ—a wajan faÉ—in.

"Eh mune"

"to ku biyoni"tabasu amsa,tayi gaba suka bita abaya zuwa gurin wata arniyar mota.

Dukansu suka shiga taja suka tafi.

Idon suhaima kamar ze faɗo sabida kalle kalle,a ɗaya ɓangaren kuma murna take zataga kabarin annabi da kuma ɗakin Allah,sabida tayiwa innarta addua.

Su suhaima manya,kowa ya faÉ—amata,a jiddah É—akin Allah da kabarin Annabi suke oho.

wani katafaren gida suka shiga.

Wanda yagaji da haÉ—uwa,suhaima har faÉ—uwa tayi gurin kalle kalle.

Abinci aka basu,bayan sunci sunyi sallah,sannan, aka kaisu makwancinsu.

Sosai abun yaba suhaima mamaki ganin É—aki É—aya amman sunfi su talatin acikinsa,kowa da jakar kayanta.

Hira suka shigayi,anan suhaima taji ashe daga gari dabam dabam aka kawosu.

A hakade har bacci ya É—aukesu dukansu,kowacce cike da kewar gida,bama kamar suhaima,da ita kaÉ—aice yar garinsu.

muje zuwa.

surbajo for life.

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra Muhammad Mahmud

*Maki gani ya kauda idonsa👇*

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

*DEDICATED TO ZAHRA BUKAR(ALLAH YA SAUKEKI LAFIYA,AMEEN)*

*9-10*

Washe gari da safe,bayan sunyi sallah,wanka sukayi sukaci abinci,sannan hajiya duniyar sama ta kwashesu zuwa wani boutique.

Suhaima se murna take ta É—auka zasu gurin Annabi ne,ganin sun tsaya abakin boutique ne yasa tagaza yin shuru tace

"Hajiya don Allah yaushe zamuje mukaiwa Annabi ziyara,naji ance anan yake?"

Wata uwar tsawa hajiya ta dakamata sannan tace.

"uban waye yace miki,duniyar sama na siyo yanmata dan suzo sukai ziyara madina,?to in mafarki kike kiyi saurin farkawa,atafiyata,nafarko baa aure,kuma baa zuwa masallacin harami,bare kuma kiyi tunanin zuwa madina,basu na kawoki kiyiba,dan haka ki kiyaye,dan duk wacce takarya dokata wlh hukuncinta haukacewane kunde ji na gaya muku"

Bayan sun shiga ta siyo musu kayanne,suna hanyar komawa gida,suhaima bata daddaraba tasake cewa.

"To hajiya me muka zo yi anan don Allah?"

"kunzo karuwanci ne"cewar hajiya tana tauna cingum.
Chapter 2 · 0% Book details