Sashe 9
Heart Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
aka ce daga Asibitin gwabnati na garin Kura ne, suna tareda mai dakinsa wadda tace sunanta Safiyyah, mota ce ta bigeta akan titin garin Daka-Tsalle, taji raunuka amma da sauki. Zayyan saura kadan sityarinsa ya kwace masa ya shiga fadin….. “Innalillahi…”. Allah ya taimake shi ya rike sityarin sosai. Yace musu yanzu ya shigo Kano, nan da ‘yan mintuna zai iso asibitin Kuran ya dauketa. Cikin mintunan da basu gaza talatin ba, da taimakon kwatancen mutumin da ya buge Safiyyah ya isa asibitin kauyen. Safiyyah kasa hada ido da Zayyan tayi, ta runtse ido tana hawaye lokacin da taji sallamarsa a dakin, cikin muryarsa mai ratsa zuciyarta yace “AsSalamu alaykum” sannan ya murdo kofar dakin ya shigo cikin nutsuwarsa, a nitsensa yake tsaf bai bari rudewar tasa ya gigice ba yanzun daya ganta kwance hajaran majaran a kan gadon asibiti, makale da allurar karin ruwa a hannunta, gadon da take kwance ya nufo kai tsaye gabadaya hankalinsa ya dauku gareta. A hakan kuma yake gaisawa da jama’ar dakin. Tana ji suna gaisawa suna kuma jajantawa shida mutumin daya bugeta da kuma likitan da ya kula da ita da kuma Nas din. Ya nemi alfarmarsu kan cewa a darennan zai wuce da ita Zaria bazasu kwana ba, tunda alhamdulillah ba karaya a jikinta. Amma Safiyyah taki yarda su hada ido sam. Da taimakon ma’aikatan jinya mata aka sa Safiyyah a gaban motarsa. Zayyan yayiwa ma’aikatan da suka kula da ita alkhairi na kudi sosai. A daren wajejen karfe tara na dare suka kamo hanyar Zaria. Tsakanin Kura da Zaria, bai fi tafiyar awa daya da rabi ba, tun basu yi nisa ba ya kira Anti Dije ya gaya mata ga inda ya tsinto Safiyyah. Anti Dije ta dinga salati da sallallami, kannenta kuwa sai kuka, jin wai ta samu accident a wani kauye, ita kuwa tun hawansu titi ma tayi barcin gajiya da wahala a seat dint ana gefen damansa, sakamakon allurar barcin da aka yi mata. Kai tsaye ABUTH ya nufa da Safiyyah don a kara bincikar lafiyarta da kyau, bai yarda da kwarewar asibitin kauyen ba, ta kuma samu kyakkyawar kulawar data dace, kai shi yana tantama ma yanzu akan lafiyar kwakwalwarta, in ba haka ba me ya kaita wani kauye Daka-Tsalle, wa ta sani a can? Ko dai son haihuwa ya soma motsa masa kwakwalwar Sophie ne? Don a cikin handbag dinta da aka bashi wadda duk uban gudun da taci bata yarda ta yasar da ita ba, yaga takardun tasa-tasai (test-test) na wani asibiti a cikin jakar. Sannan tun isowarsa Kura da suka hada ido uffan bata ce masa ba, bata ma kara yarda ta hada ido dashi ba, ignoring haduwar idonsu take, don gani take daya kalli idonta zai ga tamkar Tsimbirbira ya aikata abinda ya ambata da ita. Daman dai iyalin Baba Zayyan in har ba asibitin koyarwa na Ahmadu Bello ba, basa gane kowanne asibiti, hatta daga Abuja suna tahowa suzo ABUTH idan lalura bata gaggawa bace, tun bayan rasuwar Baba Bello ya zama addicted da asibitin ABUTH. A can asibitin Anti Dije ta samesu, tare dasu Sabah su duka ukun har ita hudu gabadayansu a rude suke. Duk da ransa a mummunan bace yake da Safiyyah amma haka ya daure yayi ta hidimar lafiyarta, ya shiga nan ya fita can tare da likitocin dake dubata a A&E ko a fuskarsa bazaka ga fushin sa ko bacin ransa da Sophie ba. Har saida ya tabbatar an bincike lafiyarta sosai ba wani mummunan rauni bayan gocewar kashin da kukkujewa da buguwa. Aka bata magungunan rage zogin ciwo ta sha. Tsakanin Anti Dije dasu Rayyah kadai ake tattauna wannan abu da ya daure musu kai, ko ina Safiyyah taje a Kura da Daka-Tsalle ba tareda ta bari dayansu ya sani ba? Don Zayyan ya tabbatar musu acan ya daukota. Har lokacin Safiyyah barcinta take sadidan, an bata maganin barci don ta huta daga azabar ciwon kashi, kuma alhamdulillah iyaka abinda likitan Kura ya fada suma shi kawai suka gani. Iyaka tsinkayensu sun kasa cankar inda taje, da kuma abinda ya fitar da ita ana tsaka da bikin ‘yar Antinta wato Ni’ima. Da daddare bayan Anti ta kawo musu abincin dare tace “Zayyan kaje dakin bakin Babansu Ni’ima ka kwana ka huta mana, mu sai mu kwana da ita, akwai gajiya a tare da kai sosai”. Amma Zayyan yaki, yace da Anti Dije shi zai kwana su su tafi. Anti bata tafi ba saida ta tabbatar ta zuba mishi abincin data kawo da kanta ya ci, tuwon semo da miyar egusi, har lokacin Sophie bata farka ba, ya kai su Anti Dije gida ita dasu Rayha ya dawo asibitin, sai ya biya ya taho ma patient din tasa da Rufaidah Youghurt, don ya san tana sonta sosai, kuma ya samo mata wanda tafiso (thick and creamy) da fresh milk din Hollandia. Da duk abinda zasu dan bukata na kwana biyu a asibitin harda su brush da maclean da sabulun wanka, don an bata (bed rest) na kwana biyu. Yana tafe yana waya da Anti Dike. Inda ya hana su Anti Dije gayawa Malam da Ammi komai akan fitar Safiyyah, yace shi zai iya tackling koma menene, tunda dai bata taba yin hakan ba. Kuma tunda alhamdulillah ba mummunan rauni sosai a jikin ta, to ba sai sun ji ba, don kada a daga musu hankali. Daga shagon Rufaidah masallacin asibitin ya nufa yayi sallar magriba da isha da suka subuce masa, ya rokawa Safiyyah lafiya, a ransa yana addu’ar Allah yasa alkhairi ne ya fidda Safiyyah daga gida. Wanda ya bigeta ya tabbatar masa a Daka-Tsalle ya buge ta kuma da ganin ta ba cikin hayyacinta take ba, da gudun gaske ya ganta tsakiyar titi a gabansa. Sai ya soma karfafa tunaninsa na anya kwakwalwarta lau take? Hakan kuma bai danne fushinsa ba, amma ya danne fargabarsa. Sanda ya dawo dakin wajejen karfe goma sha daya na dare ne Safiyyah ta farka. Yana shigowa suka hada ido, ba yadda zata yi tayi ignoring ya riga ya ga idonta biyu. Sai ta tsayar da idanunta suna kallon nasa cike fal da hawaye. Ya dauke kai kamar bai kula ta farka din ba shima, kwarai yaga razana da rashin gaskiya a tattare cikin idanunta, sai ya ja kujerar dake gabanta can daga saitin kanta ya zauna, ya bude lemun da ya shigo dashi na gongoni na ‘Schweppes’ ya soma sha. Sosai Zayyan ya share Safiyyah, a ransa yana kissima irin ‘silent punishment’ din da zai yi mata, har sai ta fallasa abinda take boye musu da bakinta, yayi kamar bai ankara da cewa ta soma sakin sassanyar kukanta cikin in’inarta na nuna nadama ba, ga firgicin tuno Tsimbirbira. Data rufe ido shi take hangowa ya biyota. Jikinta ya hau rawa da kyarma. Rashin ganin fuska daga Zayyan yau, da yadda yayi murtuk da ita ya hade giran sama da na kasa shi yafi komai tsoratata da kara sakata a damuwa. Ga mamakinsa shi kansa, yau kukan Safiyyah ko kadan bai sosa ransa ba, don ya san na rashin gaskiya ne, duk da babu abinda ya tsana irin kukan Sophie, balle kuma bacin ranta akan komai, amma yau kwarai ta yi abinda bai taba zato ba, (satar fita) zai kira abun ko cin amanar yardar da yayi mata? Har shaidan na kimsa masa ko tun yaushe Sophie take yin hakan gareshi bai sani ba? Kuma ina da ina Sophie take zuwa in tace masa zata je Zaria gun Anti Dije? Har sai yau da Allah yayi niyyar nuna masa, shine yasa mota ta kadeta, yadda bata da damar komawa gida bai ganewa idanunsa inda taje ba? Da yake shi Ubangiji ya san bashi da hakkinta, duk wata kyautatawa da trust dinsa ya mallaka mata su. Ransa ne kawai bai cire ya baima Sophie don soyayyah, kauna da yarda ba. A irin yardar da yayiwa Sophie, da nagartattun halayenta daya riga ya shaida, da tarbiyyar da yake da tabbacin ta taso a cikin ta, baiyi zaton abinda zuciyarsa ke zargi yanzu a kanta ba gaskiya bane, amma fisabilillah bai taba kawowa a ransa Sophie zata iya ketare iyaka a cikin aurensu ko ta ha’ince shi ba. Tunda ta san ko me take so in ta nemi izninsa bazai hanata ba, gashi yanzu taje tana neman salwantar da rayuwarta a banza. A zahiri Sophie bata taba bata masa rai ta bakanta masa, ta kuma sa masa zato da shakku akanta irin yau ba. Wani matsanancin kishi da bai san yana dashi a kan matar tashi ba sai yau yake fiddo kansa sarari, cikin fushin da yayi da Sophie. Tun Safiyyah na kuka kadan kadan har kukan nata ya fito fili. Ta soma rera masa shi kamar ana busa sarewa ko yaji tausayinta ya saki fuskarsa. Sau tari ta san Zayyan baya bata bakinsa wajen cewa kayi masa ba dai-dai ba. Kuma baya son kayi masa laifi kayi ta bashi hakuri. Shiru yake yi ya dafa mutum da manyan idanunsa da shirunsa har sai ka gwammace ya bude baki yayi maka balbalin fada, ko ya zane ka da bulala fiyedawannan long silence din da zaiyi maka. Don zafin kallon data ke gani cikin idanunsa yafi na bulala radadi a jikinta da zuciyarta. To irin abunda yayi mata yau ma kenan. Da kukan nata ya fara damunsa sai ya mike ya shiga toilet yana daura alwala don dare ya nausa yanaso yayi nafila, kasancewar a (amenity room) suke su biyu kacal, ya gama alwala ya wanko bakinsa da brush da maclean dinda ya sayo musu na ‘Longrich’ sannan ya fito ya fice daga dakin. Ya bar mata kamshin ultraviolet dinsa kadai a dakin asibitin. Can anjima sai gashi ya dawo tare da nurse mace guda daya. A lokacin tana tsane hawayen idanunta tana harhada kalaman da zata yi masa bayani dasu a ranta, don kawar da zargi data lura ya samu muhalli a zuciyarsa da wanke laifinta. Suka shigo shi da nurse din, ganin ta farka kuma ruwan da aka saka mata ya kare sai Nurse din ta cire mata ruwan da allurar dake hannunta don ta huta. Tace “to kukan na menene kuma Mrs. Safiyyah Rafindadi? Bayan gaki ga Oga a gefenki, tunda ya kawo ki ko sau daya bai zauna ba, yanata