Sashe 8
Heart Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Motocin da ke tahowa daga bayansu duk suka yi wucewarsu babu wanda ya tsaya, yamma tayi sosai, burin kowa ya kai gida ko gari mafi kusa kafin shigowar dare. Sai tsirarun mutanen da abin ya faru akan idon su ne suka kawo agaji, suka rufu akan Safiyyah da aka wancakalar a gefen titi, suka taimaka masa aka saka ta a motar wanda ya bigeta din. Wani dattijo ya shiga gaban motar don nuna musu asibiti mafi kusa. Safiyyah kwance a bayan motar, aka doshi babban asibitin garin Kura da ita. Da kyar likitocin suka yarda suka amsheta saboda babu report din ‘yansanda, wanda ya buge tan yace basu hadu da police ko daya ba daga Daka-Tsalle har suka iso Kura, don haka asibitin ne suka kira police aka rubuta report, shikuma ya biya kudin duk treatment din da ya kama za’a yi mata. An yi sa’a Sophie bata samu karaya ba amma dai akwai gocewar kashin kafa dana hannu, sai kananun raunika da kukkujewa, abinda ya daukesu har bayan isha’I ana mata treatment kafin Safiyyah ta fara dawowa hayyacinta. **** **** **** A can kuma Tudun wadar Zaria, wato gidan Anti Dije, hidimar biki data jama’a bata sa Antin ta gane Safiyyah bata nan tun sassafe ba. Sai bayan azahar da Rayyah kanwarta ta gane rashin dawowarta gidan, ta tuno tun safe data ganta tana shiryawa lokacin su Sabah suna barci ita kuma ta farka tace mata zata dan fita ne, amma yanzu zata dawo, to bata dawo din ba. Kuma har la’asar ta kawo kai Safiyyah bata dawo ba wanda hakan yasa kannenta da suke tare a daki daya duk suka damu, suka soma kiran wayarta ana cewa “not reacheable”. Daga bisani Sabah ce taje ta samu Anti Dije cikin kawayenta cike da damuwa, a lokacin ana shirin tafiya Mother’s Eve. Tace. “Anti Dije, ko Yaya Safiyyah ta gaya miki inda zata je ne? Tun safe fa data fita bata dawo ba, kuma bata gaya mana ina zata je ba”. Anti Dije ma sai a lokacin ta ankara tun safen itama bata ganta ba, jama’a ne suka sa hankalinta bai kai wurin ba, tace “to ina Safifi zata je haka tun safe bata gayawa kowa cikinmu ba? Amma kira Zayyan ki tambayeshi, bazai kasa sanin ina taje ba, babu inda zata je bada saninsa ba, in kin bibiya ma suna tare”. Sabah ta kira Zayyan, bugu daya ya dauka suka gaisa yana ta tsokanarta da amaryar robarsa, yadda ya saba tsokanarta don ita ke bin Safiyyah a haihuwa, amma bata biye shi a wasan ba yau, cikin damuwa tace, “Yaya Zayyan, aunty Safiyyah ta gaya maka inda zata je ne in bi bayanta?” Yace “kamar yaya? Ba kuna gidan Anti Dije ba?” Sabah ta kara shiga cikin rudu, ta ce “eh, duk muna can, kuma tare muka kwana da ita a daki daya, amma da safennan tace ma Rayyah zata dan fita bazata jima ba, amma har zuwa yanzu karfe hudu bamu ganta ta dawo ba, kuma wayarta bata shiga, Anti Dije tace watakila kuna tare a kiraka a ji”. Shima ya tuna da safe wajen karfe goma sun yi waya da ita, lokacin isarta Standard Hospital kenan, tace masa “she will call him back” bata jinsa sosai, saboda tana cikin mutane, sai ya dauka ‘yan bikin gidan Anti Dije take nufi. Nan kuwa a lokacin tana magana da kawarta ta kan layin asibiti Ammara ne. Tun daga lokacin kuma bata kira shi din ba, shima kuma yaje Batsari gidan Yayarsa Zubaida ta tsare shi da zance irin nata na kullum, wato na kushe rashin haihuwar Safiyyah har yau. Don ma har yau basu san wanene mara haihuwar tsakanin shi da ita ba, da bai san ya zai kare dasu ba. Zubaidah tace “sun lura Safiyyah ta tsare gabansa da bayansa, ta hana shi auren diyar kowa, ta shiga rigar arziki tana wadaka son ranta, tana bakin cikin kada wata tazo ta ci, ta hanashi auren da zai karu dashi sai tatse shi suke itada iyayenta kamar hanji. Ita kuma Safiyyar ta kasa tsinana masa komai tunda har yau ta kasa mayar da shi Uba, cikakken namiji mai iyali kamar kowa. Tace “kwarai zan so sanin me Safiyyar nan ta taka da take juyaka har haka Baffa, ita ba wani shahararren kyau ba, ita ba aji ba (class) ita kuma ba iya kwalliya ba, kullum ka ganta cikin ragga, wai ita me addini, ko sabida sun saka sunanka a minjaye sun wanke sun baka ka shanye ta bakin Mama?”. Tsaki yayi “mtssw!”. Ya mike yayi bakin kofa ya hau saka takalmansa. A karshe dai basu yi rabuwar dadi ba shi da Yaya Zubaida, don har yace mata ba zai kara tako kafarsa gidanta ba, shi zumuncin Allah ne ya kawo shi baizo don ta aibata masa mata ba. Ire-iren yadda yake kare martabar Safiyyah dinnan a wajen danginsa, yana matukar kara mata bakin jini a wurin ahalinsa bakidaya, ba tun yau ba. Bacin ran Yaya Zubaida ne yasa bai kara kiran kowa a waya ba ranar, har itama Sophien, ya juyo zuwa gida Katsina, inda cikin rashin sa’a kafin ya kai ga isowa Rafindadi Yaya Zubaida ta kira Mama Fatu ta mata korafin ya yi mata rashin kunya akan bakarariyar matarsa, don kawai tace yazo Batsari ya ga ‘yammata gasu nan fululu, ya auri mai haihuwa. Shine ya zageta tatas (a cewarta). Don haka yana dawowa Mama ma ta dira a kansa, tace matsayin Zubaidah agareshi yafi na duk wani kwashe-kwashensa da zai zageta sabida mace, Mama ta kara masa zafi bisa zafi, bai samu sararin sake kiran Safiyyah ba saboda kuncin ran da suka hadu suka saka shi. Da faduwar gaba a ransa kadan yace da Sabah “yana zuwa”. Sai ya kashe nata kiran, ya soma kokarin gwada kiran layin Safiyyah. Abinda dai ake gayawa su Rayyah din shima shi aka shiga gaya masa wato “not reacheable” wanda hakan yayi matukar tada hankalinsa, domin ba abinda ya zo ransa a lokacin sai kidnapping. Dama dai yau tun safe yake fama da faduwar gaba, don haka jikinsa ya gama bashi ba lafiya ba, jikinsa har tsuma yake a lokacin, yace Sabah ta hada shi da Anti Dije. Sun dade suna magana na cankar ina zata je, don itama Anti Dije duk da tana cikin sabga yanzu hankalinta yafi daukuwa ga ina Safiyyah ta shiga, ta tabbatar masa bata san ina Safiyyah taje ba, kuma bata da kawaye a nan Zaria. Cikin fara shiga damuwa Zayyan yace, to gashinan tahowa Zariyan yanzu, su hadu su san abin yi, in cigiya zasu bada su bada cigiyarta, da report ga ‘yan sanda. Kwarai hankalinsa ya soma tashi. Don haka akan hanyarsa ta zuwa Zaria daga Katsina, tuki kawai yake amma hankalinsa baya jikinsa. Da tunanin ina Sophie zata je babu sanin sa, ba izninsa? Yaushe suka fara ‘yar haka shida Safiyyah? Me take boye musu shi da ‘yan uwanta da Antinta? Babu irin tunanin da bai yi ba akan ina Safiyyah zata je haka ba tareda ta gaya masa ko kannenta ko Antinta ba, a dai wannnan rayuwar da muke ciki ta kasarmu Nijeriya, ta insecurity da insurgency (rashin tsaro da ta’addanci)? Amma ko kusa bai kawowa ransa cewa Safiyyah zata iya zuwa wani wuri ba tareda izninsa ba, yardar da yayi mata da amincin dake cikin aurensu masu yawa ne, don haka ko kusa Zayyan bai kawo a ransa bata ji nasiharsa ba, da yace su dauki tawakkali akan maganar haihuwa, cewa da yayi sun rufe batun haihuwa da gaske yana nufin hakan baka da zuci, bai zaci ta saka kafa ta wofantar da zancensa ba. Ko yaya Zayyan zai ji a ransa, in yaji cewa Safiyyah ta yi kunnen uwar shegu dashi ne ta kama hanyarta ta fita duniya neman haihuwa ta kowacce hanya??? **** **** **** Sanda Safiyyah ta dawo hayyacinta ta kuma fahimci a inda take kwance asibiti ne, tana kuma jin ciwo ko’ina a jikin ta, ba karamin firgici ta shiga ba. Likita da Nas din dake duba ta suka dinga kwantar mata da hankali, har suka ce ta godewa Allah da babu karaya, shi kuma wanda ya buge ta ya dinga bata hakuri, da kyar suka samu ta nutsu, tace dashi babu komai ai tsautsayi ne. Nan suka tabbatar mata an gyara gocewar kashinta na kafa dana hannu. Kuma mutumin yayi settling bill din gabadaya, aka ce ta bada lambar wani nata a kira su a gaya musu halin data ke ciki suzo su kula da ita, don bazata iya tafiya gida a yau, kuma cikin wannan halin ba. Sai a lokacin Safiyyah ta tafi ga tunanin ainahin abinda ya faru, da kuma sanadin afkuwar hakan, tabbas gagarumin laifi ta yiwa Zayyan. In fact, ta ci amanar aure, bayan ta fita babu iznin mijinta yanzu da bokannan ya samu nasara akanta fa, itada Zayyan shikenan ko! Aurensu ya lalace kenan! Yanzu gashi alhakin Zayyan da Allah yasan bashi da hakkinta, yasa mota tayi awon gaba da ita, don Allah ya nunawa Zayyan bata ji wa’azinsa da ban bakinsa ba, har gashi yanzu bata san ranar warkewarta ba, babu kafar yawon asibiti neman haihuwa data zuwa gidan Malaman tsubbu, balle ayi maganar kafar komawa gida. Kawai sai Safiyyah tasa kuka, ta soma yinsa kadan kadan da sheshsheka. Sannan with a heavy heart ta fado/rattabo musu lambar wayar Zayyan, wadda ke kwance a kokon kanta tamkar karatun sallah. ‘Guilt’ ne dai gashinan duk ya lullubeta, don hakika taci amanarsa (tayi satar fita) abinda bata taba yi ba tun aurensu, har anyi kokarin yi mata fyade da aurenta. Tunda sai da yace mata tayi tawakkali ta hakura da batun haihuwa in dai don shi take nemanta, amma kafiya da ci da zuci irinnata yasa taki ji. Wani ikon Allah Zayyan yana shiga garin Kano inda daga nan zai dauki titin da zai kai shi Zaria, wajejen karfe takwas na dare wata bakuwar lamba ta kira shi. Zayyan bai ko kalli wayar ba saboda halin da yake ciki, yana tuki yana azkar, da fari kamar bazai amsa kiran ba don baya cikin yanayi na iya amsar wayar mutane, amma ganin nacin mai kiran a karo na uku yasa ya daure ya dauka, murya a dashe. Nan aka yi masa sallama,