← Book details Heart Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 29

Sashe 26

Heart Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Yadda Mama Fatu ta dauki zancen auren Azeezah da matukar muhimmanci kamar dama a jirace take bai kamata ya bashi mamaki ba, amma hakika ya bashin. Don kafin ma ya baro Lagos Mama da Zubaidah sun gama hada lefe na gani a bada labari kamar diyar gwamna za a kaiwa, akwatuna dozen, masu matukar matsayi, babu ce kurum babu a cikin lefen da Zubaidah ta hada.
Ana i-gobe zai baro Lagos, shida Azeezah ido ya raina fata, sukayi wata irin sallama ta soyayya saura kadan suyi runguma yayi maza ya fice, zuciyar sa na balli balli. Da kyar ya kwanci kansa daga zarce iyaka. Mama ta gayawa Hajiya Nana cewa suna so su kawo lefe washegarin dawowarsa gida.
Abin dai tamkar tatsuniya ko kuwa almara. Komai da komai ya faru tamkar kiftawar ido, neman auren da bayarwa da saka rana duk sun faru ne cikin abin da bai gaza sati uku ba.
Ranar da ya koma Abuja bai ko gayawa Sophie yana hanya ba, bai tashi jin kunyar kansa da kansa ba, sai da ya yi tozali da Safiyyah.
Damuwar da ya jefa ta a ciki ashe har kwantar da ita zazzabin sati guda ta yi, ta rame ta yi fiyat, kamar da ka bushe ta zata fadi, amma kyawun nan na Safiyya yana nan daram, duk da muguwar ramar da ta yi.
Ya ji kunya in ya ce kunya, yana nufin kunya ta karshe da bai taba ji a rayuwarsa ba, don Sophie ba ta ma san da dawowarsa a ranar ba.
Tana kitchen tana dafa ruwan ‘tea’ da za ta saka a hantar cikinta dake raurawa, ta ji motsin shigowarsa falon, ta hanyar amfani da nashi safayan makullin gidan.
Safiyya ta juyo da sauri jin motsin shigowarsa da kamshin turarensa. Suka hada ido, sai ya ji kunyar da bai taba ji ta diya mace ba ta lullube shi, hade da wani irin 'guilt'.
Fuskar Sophie kadaran-kadahan, wato ba yabo ba fallasa ta ce, “Sannu da zuwa”. Sannan ta juya tana ci gaba da juye ruwan zafin da ta kammala tafasawa a karamin ‘tea flask’. Tana kokarin hadiye hawayen da ke son gangaro mata.
Zayyan ya canza gabadaya har wata kuruciya da fresh fatar jikinsa ta kara, alamu ne na yana cikin mabayyanin kwanciyar hankali, hutu da jin dadin zamansa a Lagos, bai ma san halin da ya jefa ta ba. Ta sa dan yatsanta ta dauke hawayen da ya gangaro ta karshen idanunta.
Zayyan ya tako har inda take cikin shanye kunyar tasa, ya sanya hannayensa ya sakalo kugunta ya dora habarshi saman kafadunta yana sakale da waist dinta, ya ce cikin muryar rarrashi.
“Sophie I’m back, me ya faru da ke haka, irin wannan rama haka my Dear Safiyyah?”
Safiyyah ba ta taba hararar Zayyan bisa saninta ba sai yau, ta zabga masa harara ta zare hannayensa daga kugunta ta dau tea dinta da kofin mug ta bar wajen.
Haka ya biyo ta falon cikin karfin hali irin na Da namiji, ya ce.
“Laifuffukana ba za su lissafu ba gare ki Safiyyah, na sani. Amma ki gafarce ni yanzun ki fara ba ni abinci ba don halina ba, I terribly miss your cooking”.
Hawaye suka sulmiyo daga idon Safiyyah, wani weak point dinta kenan guda daya shima ya sani, ba ta iya barin Zayyan da yunwa, don haka shayin da bata sha ba kenan duk da itama yunwar take ji. Sai ta koma kitchen ta shiga hidimar girka masa abinci.
Shi kuma ya bi ta kitchen din ya zauna a kan granite yana ta baibaye ta da kalaman ban-hakuri da amsar laifi. Shi kansa ya rasa hujjarsa ta kin neman Safiyyah ko amsa wayarta har ya je Lagos ya dawo.
Gani ya rika yi yana daga wayarta ko tana jin muryarsa za ta gane ya fada komar wata macen ba ita ba, amma ba don laifin da ta yi masa a ranar da zai tafi ba.
Ta kammala dafa masa jallof din cous-cous da ya ji veggies da hanta sosai, ta zubo a faffadan tray ta kai masa kan dining din dake cikin kitchen din.
A nan ya zauna yana ci, yana yima girkin Sophie cin yaushe gamo da kewa mai yawa.
Ya yi- ya yi ta zauna su ci tare ta ki tsayawa don in ta ci gaba da tsayuwa a wurin rauninta bakidaya da take boyewa zai bayyana kansa. Ta ji ciwon abin da ya yi mata, domin ya zarta hukunci a kan laifinta, a ganinta ya koma zalunci kuma ya dauki hakkinta.
Tunda ta bar kitchen din shima ya ji ba zai iya ci gaba da cin abincin ba, tashi ya yi ya biyo bayanta zuwa dakinta.
Tana canza kayan jikinta, tana kokarin daura towell don shiga wanka Zayyan ya zagaye ta cikin hannayensa, ya kai mata sumba a wuya, ta goce da zafin nama. Ya sake kai mata a bakinta, nan ma ta kwace, amma Zayyan bai bata damar hakan ba domin tuni ya samo bakinta ya soma yi mishi tsotson yaushe gamo. As usual duk yadda ta so bijire ma Zayyan a wannan fannin da wuya ta ke samun nasara. Wuyarta ya soma kissing bakinta da nasa
Kuka ta saka masa, shi kuma ya soma lallashinta har da roko. Bai sakaya mata yadda bijirewarta gare shi ya saka shi sha’awar kara aure ba. Duk da bai fito fili ya fada mata har auren ya nema ba, an kuma bashi, amma kuma Safiyyah duk ta sha jinin jikinta.
Wanda hakan ya sa ta kara jin bacin ranta ya ninka na baya. Wani abu da Zayyan bai taba yi ba shi ne, tursasata kan ta yarda da shi, amma yau? Yadda yake so haka ya sarrafa Sophie, alhalin taki amincewa, yace saidai duk su mutu amma bazai iya hakurin ba, tana kuka tana gaya masa ta tsaneshi ta kuma tsani auren bakidaya. Ko a jikinsa, nemawa kansa nutsuwa kawai yake. Duk sha’awar Azeezah da ya kwaso a Lagos a nan ya sauke ta tas.
Sai da ya samarwa kansa nutsuwa yadda ya kamata sannan ya sassauta mata. Ya koma gefe hannunsa cikin tarin lallausar sumar kansa, ya rasa abinda ke masa dadi kuma. Yau shine da marital rape ga Sophie, amma ai ita ta jawo! Sama da sati uku kenan rabonsa da ita.
A kasalance ya dube ta tana kokarin suturta kanta da towel dinta da ya jefar gefe don ta shiga wanka ya ce,
“Safiyyah, ashe soyayya na komawa kiyayya saboda rashin haihuwa?”
Saura kadan Safiyyah ta zagi Zayyan yau, to kuma durawa soyayyar ashariya, amma ‘Yan gidansu basa zagi sam. Ta galla masa harara idanun sun yi jazur da danshin hawaye, ta shige toilet.
Ya sanya shorts dinsa ya bita har toilet din, tana wanka a shower tana kuka, nan ma sake nanikarta yayi, suka yi wankan tare, ya nado ta a tawul ya dauko ta suka fito, ya shiga goge mata jiki da karamin towel, sannan ya dauki lotion dinta na Nivea ya soma wani irin shafa mata a dukkan jikinta, tana ki tana komai sai da ya shirya ta tsaf, ya sanya mata bakar jallabiyyarsa, ya tarairayo ta ya aza bisa cinyoyinsa, sannan ya ce.
“Now tell me, me ye matsalarki Sophie? Ko kin daina sona ne Safiyyah?”
Ya dago habarta ya dube ta cikin ido, sai ta rufe idanun nata da ke zubar da hawaye har a lokacin. Ba zai gane irin ciwon da ta ke ji a ranta ba a kan rashin haihuwa da shi, haka ba zai gane yadda biris din da yayi da ita har tsayin sati biyu ya kassara zuciyarta ba.
Duk ma ba wannan ba, Zayyan bai taba iya wuni guda bai kirata a waya ba, amma yau kwana dai-dai har goma sha hudu! Zayyan ya kwashe ba ta ko ji muryarsa ba. Alhalin yana lafiya sumul kalau. Jikinta ya gama ba ta (something is fishy) don wannan ya zarce punishment kan duk wani laifi da yake ganin ta yi masa.
Ya yi rarrashin duniya yana rokonta ta yafe masa, wani abu ne ya kutso cikin rayuwarsa a wannan tafiyar da yayi, da ya hana shi kiranta.
Yayi ta zagaye-zagaye, ya kasa gaya mata komai, har dai ya samu ta ce masa ta hakura ta kuma yafe, amma don Allah tana rokon alfarmar su kara yin IVF ko ta samu sanyi a zuciyarta kamar kowacce mace.
Ya tuno da gargadin Mama a kan sake yin IVF, in ya gaya mata Mama ta hana kuma zai zama tamkar ya kara hada gaba tsakaninta da Mama, dama Ya Allah cika. Don haka ya samu gangara ya ce.
“Safiyyah tuni na samo mana solution a kan wannan matsalar, IVF mun yi shi a baya, wannan karon na canza shawara, na ce me zai hana in kara aure?
Mu yi fatan Allah ya kawo rabo na gaggawa?
Safiyyah na miki alkawarin ko me matar ta haifa na farko danki ne halak malak dinki, ko shayarwa in kin so ke za ki shayar da shi”.
Safiyyah ta yi yunkurin mikewa daga cinyoyinsa ya sake maida ita ta zauna, don ta fara tunanin ko Zayyan ya fara shaye-shaye ne? Kalmar zai kara aure a wannan lokacin ita tafi komai bata mamaki, ba almararsa ta wata ta haifi Da ya kyautar mata ba.
Ta yarda da aka ce duk wadda ta ce namiji uba ne za ta kwana marainiya!
Haka kuma duk inda mijinki ya kai da sonki, kada ki dauka akwai bambanci tsakaninsa da sauran maza, duk sunansu MAZA!
Ta tsaya ma tana asarar hawayenta ya zama asara ko faduwar da babu tashi. Don haka Sophie ta share hawayenta, ta dube shi da idanun rahma ta ce.
"In kana ganin wannan shi ne mafita, kuma zai samar min sa’idah a wurin Mama da ‘yan uwanka, sannan zai sayo min soyayyar Mama ta yarda ban mallake ka ba, kamar yadda kullum suke cewa, sannan hakan zai ba ka farin ciki Zayyan, sannan baza'a kara yimin gorin haihuwa ba, to (you have my full support) ka kara aurenka”.
Ya yi sak da zuciya da idanu, yana kallonta kamar mai son karantar gaskiyar da ke cikin zuciyarta. Don bai taba zaton al’amarin zai zo masa haka cikin sauki daga Safiyyah ba. Ita ma ta dube shi cikin ido, yau babu kallon soyayya, ta ce,
“Yes, I mean it”.
Ya ce, “Amma na ji wani suna daga bakinki wanda bada shi kika saba ambatar sunan mijinki ba, anya Safiyyah har zuciyarki kin amince in kara auren?”
Safiyyah ta buda hannuwa irinna matsalar taka ce ba tawa ba tace, “Habiby, na fada na kara Habiby, Habibiy, shikenan ko?
Ka yi hakuri tuntuben harshe ne nayi nace Zayyan!”.
Amma ita a kasan zuciyarta ta san soyayyar ce ta ragu, ta yi flat a kasa daga wannan lokacin.
**** **** ****
Chapter 26 · 0% Book details