← Book details Heart Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 29

Sashe 29

Heart Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Sannan ta kara ja ma Sophie kunne a kan kada ta sake ta tanka su ko me za su ce mata, giyar farin ciki ke dibarsu. To Allah na kowa ne, kuma zai iya mata abin da ta kasa.
Sai da ‘yan kawo amarya suka ware Aunty Dije ta kada kan su Sabah su ma suka wuce guest house din da aka yi musu masauki a nan cikin Sunset Estate. Suka yi sallama da ita a kan cewa da safe ba za su shigo ba, sammako za su yi su juya gida abinsu.
To shi ne fa Zayyan bai shigo gidansa ba sai can dare kamar yadda ya faru a farkon littafin, fatansa shi ne Allah ya sa wannan auren da yayi bai zamo (biggest mistake of his life) ba, wato bai zamo babban kuskuren sa a rayuwa ba, maimakon nemo mafita ga matsalarsu shi da Safiyyah.

Kiran sallar asubahi ne ya dawo da shi daga 'down memory lane' din da ya tafi, wanda ya kunshi gwagwarmayar kuruciyarsu data soyayyarsu data rayuwar aurensu shi da Safiyyah. Da kuma ranar yau, wato ranar da "Azeezah Murtala" ta tare a gidansa.
Azeezah ta iso cikin rayuwarsu da fatansa na zata zamo maslaha ga matsalolinsu.
Da ya dawo kuma ya dade zaune cikin motarsa saida ya tabbatar 'yan kawo amarya sun watse, kuma maimakon ya tafi dakin uwargida yayi mata sallama ya wuce gun amarya sai ya zabi ya wuce masterbedroom dinsa, yayi tunanin rayuwar sa da Safiyyah tun farkon fari, because he lacked all the courage na dosar inda Safiyyah take a wannan daren.
Zayyan ya kwanta ne kawai rigingine a gadonsa yake wannan dogon tunanin. Don yanzu da Azeezah ta zama mallakinsa, bakin alkalami ya riga ya bushe sai yake jin kamar yayi kuskure, kuma kamar bai kyautawa Safiyyah ba. Kamar wannan shine kuskure mafi girma daya aikatawa rayuwarsa, maimakon kawo maslaha.

Mu duka ni da ku masu karatu dai mun san cewa "not all that glitters is gold". Azeezah nada duk abinda yake so a diya mace, while soyayyarsa naga Safiyyah diyar Malamai, amma kuma muna sane da cewa Zayyan ya manta cewa babu yadda za’a yi ka samu rayuwa dari bisa dari daidai da ra’ayinka da burinka, dole kowa yana da irin nasa nakasun a wurin abokin rayuwarsa.
A rayuwa, sau tari idan Allah ya baka wannan zai iya hana maka wancan kamar yadda Safiyyah ta kasance, duk dan Adam tara yake bai cika goma ba, ba duk abinda mukeso daga abokan rayuwarmu muke samu dari bisa dari daga garesu ba.
Duk da haka Zayyan yana da kyakkyawan fatan cewa ‘Azeezah Murtala', will meet all his dreams in a woman, his expectations and beyond.

Mu biyo Arch. Zayyan da matansa Safiyyah da Azeezah a littafi na uku. Yanzu ne zamu fara labarin Zayyan da Safiyyah. 1&2 shimfida ne.
SUMAYYAH ABDULKADIR -Takori
07030137870
(WHTSP only)
01/04/2025
(Wannan littafi na sayarwa ne, GUNDARIN LABARIN ZAIZO A MANHAJAR TELEGRAM KADAI)
Chapter 29 · 0% Book details