Sashe 3
Heart Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sophie? Haba Nana Safiyyah! Da ilmiki na addini kike damuwa akan abinda kinsan nufin Allah ne? Ko na taba ce miki na damu ki haihu yanzu?” Ido fal hawaye Safiyyah ta dago tana kallonsa da takaici, ba tun yau ba ta san shi ba abinda ya dameshi da rashin haihuwarta, most important abinda yafi baima muhimmanci shine ‘soyayyah’ da kuma a inganta masa shimfidar aurensa, tunda kullum yana samun yadda yake so dinnan kuma a shimfidarsu, batareda wani cikas din ciki ko hayaniyar yara ko kailular dake cikin shayarwa ba kuwa me zai dameshi? Ko kuma don ba shi ake cewa “Barren Lady” ba. Amma tana kirge da cewa aurensu ya tasarma shiga shekaru takwas bata taba ko batan wata ba, sai a wannan lokacin da period dinta ya dan yi delaying. Itama da farko ai bata damun ba, amma banda yanzu da take neman kaiwa shekaru talatin, don data kokantawa Ammi damuwarta kan matsalar rashin haihuwar nan a can baya Ammi cewa tayi wai “lokaci ne”. Ta kuma kara da cewa komai data gani a duniyar nan yanada lokacinsa, in Allah ya nufa. Ta cigaba da gayawa Allah kawai, amma kada tasa damuwa a ranta, ta kuma saka a ranta ba haihuwa ce kadai farinciki ko alkhairin rayuwar aure ba, zama lafiya ma cikin soyayyar miji wani abu ne, ba kuma itace kadai ke samar da zaman lafiyar aure a duniya ba, sannan ba ita ce zata kaita aljannah ba”. Wadannan kalaman na Ammi suka sa tun daga lokacin Safiyyah ta sanyawa ranta salama, amma kwanan nan abun ya zo yana barazana ga kwanciyar hankalinta, musamman saboda gorin ‘yan uwan mijinta, da uwar mijin kanta, duk sanda ta tuna shekara takwas ba ribar aure tsakaninta da Zayyan, wanda shi zai zama sanyin idaniya a garesu, ya kara dankon soyayyar tasu, sai taji wata irin damuwa ta lullubeta. Musamman saboda habaicin da Mama da ‘ya’yanta suke sakar mata directly and indirectly. Ta jima tana sayen PT Strip a boye, bada saninsa ba tana gwada kanta, in taga babu komai haka zatayi kuka a toilet ta gaji ta wanke fuskarta ta fito, ta shiga harkokinta. Ya zamanto cewa Safiyyah ko dan ciwon kai take yi ko zazzabi sai ta roki Allah yasa laulayin ciki ne. Haka zata shige toilet yin PT, amma kullum amsar daya ce “negative”. Safiyyah ta fara tunanin ko bata gamsar da mijinta ne shiyasa ta kasa daukar ciki? Gashi ita bata yarda da wani abu wai shi maganin mata ba. A hankali abin har ya zamar mata tamkar ‘desperation’ ba tareda sanin Zayyan ba, don ba kowanne lokaci damuwar take zuwar mata ba, musamman in suna tare, sai idan ta kadaice ko tana tare da danginsa. Na yau ne kadai Allah yasa ya ritsa da dawowarsa. Don haka Zayyan yau ya sha mamaki don bai taba ganin Safiyyah cikin wannan yanayin ba, jage jage da hawaye gashin kai a hargitse zaune dirshan a tayal din toilet. A saninsa matarsa Safiyyah macece jaruma, mai tawakkali kuma, da iya shanye damuwa komai girmanta. Da kyar ya samu ya lallabi Safiyyah ta daina kukan amma ta bullo da sabuwar rigimar cewa dole suje asibiti a binciki lafiyarsu. Tace duka tsararrakin aurenta daga mai ‘ya’ya uku sai mai biyu. Hatta Zaitoon da Zahra da aka aurar a bayan bayanta sun haihu wannan shekarar. Zayyan sai ya fara harzuka, ya dago da mamaki ya dubeta, yace. “Safiyyah ban fahimce ki ba, haihuwar abin competition ta koma? Ko kuwa don ace kema kin haihu kikeson haihuwar? Ban sanki da haka ba sam. Kada shaidan ya samu gurbi kuma. Don idan don dayan biyun wannan ne kike son zuwa asibitin, to ni ba inda zanje, sai kije su rakaki inda aka basu nasu maganin haihuwar ki karbo naki”. Haka suka kwana a ranar baram-baram kowa zuciya a kusa, a ganin Safiyyah Zayyan bai damu bane sam da rashin haihuwarsu, saboda bashi ake yiwa habaicin yana cika masai da kashi ba. Rashin nuna damuwar tasa akai ya kara ninka tata damuwar, don a ganinta damuwar ba tata bace ita kadai, tasu ce su duka, inda alkawari. Haka ya jefa filo akan center carpet na dakin barcinsu yayi kwanciyarsa ya rabu da ita. Yanata sake-sake a ransa. Ko dai wani yayi musu labe ne yaji kalaman Mama Fatu shine yazo ya tseguntawa Safiyyah ta waya ya daga mata hankali? Kalmar Mama ta ‘bakarariya’ ko shi tayi masa babu dadi. Yana wannan tunanin ya ganta ta cikin dan hasken dim light din dakin, ta mike a hankali ta shige toilet, ta dauro alwallah ta fito, ta canza sutturar jikinta daga rigar barci zuwa hijabin sallahrta, ta shafa turaren ‘musk’ a hannayenta. Safiyyah ta fuskanci gabas ta tada sallah. Yana daga cikin manyan dabi’un Sophie dake burgeshi. Suke kuma kara mata matsayi a ransa. Cikin halin farin ciki ko akasinsa, bata bari shaidan ya jagoranceta ko ya rinjayeta tayi wani abu ba daidai ba. Tafi gane tayi sujjadah ta gayawa Allah kukanta. Haka yaga ta raba dare a kan abin sallarta, shima kasa barcin yayi, yana jin tsigar jikinsa na tashi da kukanta, tana kuka tana yiwa Allah kirari, tana kambama shi cikin sujjadarta ta hanyar kururuta girman izzarsa da buwayarsa, cikin rokonsa itama ya bata haihuwa, kamar yadda yake baiwa daukacin bayinsa. Ta san ba wai ya manta da ita bane”. Daga kwancen da yake Zayyan ya tayata amsawa a ransa da; “Ameen, idan alkhairi ce a garemu da addininmu Safiyyah Allah ya bamu!”. Ganin yau bata da alamar sanya hakarkarinta a katifa har goshin asubahi, balle kuma yasa ran zata bi ta kansa, yanzu tafi son samun ‘ya’ya akansa ma kenan, humm. Mata iyayenmu! Hakan yasa ya ji kishi a ransa na ko ta haihu ‘ya’yansu zatafi so a kansa. Duk kulawar da take masa kansu zata koma. Shi kuma ta rage kulawar da take bashi, haka ya hakura yayi barcinsa ya kyaleta yana tunani mara hujja. Ya manta ko inji ne yana son hutu musamman idan bashi da service. Washegari suna karya kumallo ya daga kai daga kurbar tea kadan ya dubeta da kulawa, sai yaga duk ta zabge a dare daya, saboda daurawa kanta damuwar da ya kira ta babu gaira babu dalili. Yaga cewa shi dai a karan-kansa da bakinsa bai taba cewa “Sophie, meyasa baki haihu ba har yanzu? Ko sai yaushe zaki haihu min? Ko me ya hanaki haihuwa, ko ni Zayyan ina son haihuwa” ko ire-iren accusations dinnan marasa dadi makamancin wadannan da ake yiwa wadda ta samu jinkinrin haihuwa koda wasa bai taba hadashi da ita ba, to na menene zata bi ta damu kanta shima ta saka shi a damuwa rana daya? Domin sanin kanta ne rashin walwalarta tabbas ta san dole zaiyi tasiri akan tashi walwalar. Tana ta faman juya cokali a cikin tea ta dan dago, jin yayi clearing voice dinsa, sai suka hada ido, kuma duk sai ta bashi tausayi. Ganin ta ko kasa kurbar ruwan shayin da ya hada mata, sai juya cokali take a cikinsa. Zayyan ba tareda dogon tunani ba yace. “Na yarda, muje asibitin a duba mu Sophie. In dai shine abinda zai baki kwanciyar hankali, na lura dake jiya ko runtsawa bakiyi ba. Don haka on one condition zamu je gaban likita; duk abinda sakamako ya nuna, inma nine da matsala ko kece da matsala kada ki daga min hankalinki ki yi tawakkali ki karbi kaddara”. Ai kuwa ga mamakinsa nan da nan Sophie ta ware. Ta kurbe shayin da gaggawa har tana kone bakinta. Ta furzar da ruwan zafin a gefe da sauri, yayi mata sannu. Tace “Habiby nagode, tashi mu tafi”. Yace “dole ki gode min mana Sophie, tunda kin ci ni da yaki. Ni Zayyan ban taba fatan zuwa teburin likita wai da sunan neman haihuwa ba, because I believed time ne bai zo ba. Kuma nasan dukkunmu lafiyarmu kalau tunda kina regular period”. Safiyyah bata saurareshi ba tuni tayi daki ta hau shiryawa. **** **** **** Zayyan da Safiyyah ne zaune a gaban teburin Dr. Muwadda a ABUTH. Duk wata babbar lalura ta rashin lafiya kota ‘medical check-up’ iyalin Baba Bello sun fi ganewa zuwa ABUTH, sun fi yarda da kwarewarsu. Da wuya ka ga sun canza asibiti sai ‘on emergency case’. Don haka takanas Zaria suka taho daga Abuja, bayan samun appointment na ganin kwararriyar likitar mata Dr. Muwadda Abdullahi Shinkafi. Likitar ta yi ma Safiyyah duk wani bincike da bature ya tanada ta hanyar tasatasai (test-test), sannan ta koma kan Zayyan shima ta bincike lafiyarsa tsaf. Kwana uku a jere suna zarya a asibitin ana gwaje-gwaje da aune-aune, inda sukayi masauki a Zaria Guest Inn, kafin fitowar sakamakonsu. Ranar da aka tattaro sakamakon suna waiting room na ganin likitar, kafin a kirasu ofishin likita Safiyyah saida ta zaga bayi ya kai sau uku, saboda fargabar abinda likiciyar zata ce mata. Shikuwa Zayyan ko a jikinsa, don ya riga ya sakawa ransa haihuwa ba ita kadai ce farin ciki tsakanin shi da Sophie ba. Akwai tsantsar soyayya mai haddasa farin cikin da walwala, wadda ta riga ta haifar da fahimtar juna mai girma a rayuwar aurensu. To na meye zai damu kansa kan abinda Allah bai ga damar basu ba??? Sakamako dai ya nuna cewa Safiyyah ce mai matsala bashi ba, tanada lalurar PCOS (polycystic ovary syndrome). Likita Shinkafi, ta kira matsalar Safiyyah da suna ‘unexplained infertility’ na sanadin matsalar PCOS. Ta dorata kan treatments masu kyau na masu lalurar pcos, da magunguna masu tsada wadanda zasu iya taimaka mata tayi conceiving idan tanada rabo. Tun a hanyarsu ta dawowa Abuja Safiyyah ke fakar idonsa tana dauke kananan hawaye a idonta, alhalin yana tuki. Ya saka musu karatun Al’qurani a cikin motar cikin qira’ar Salah Bukhatir, a cikin karatun ne Sheikh Bukhatir yazo ayar da take addu’ar samun zuri’a dayyibah cikin Suratul Furqan. Ya karanto ayar nan cikin qira’arsa ta hafsu mai dadin sauraro; “Wallazeena yaquluna Rabbana hablana min azwajina wa zurriyyatana qurrata a’ayunin wa ja’alna lil muttaqeena imaama…”. Sai kukan Sophie ya kasa boyuwa a wannan gabar, domin ta kasa cotrolling dinsa, ta soma sheshshekarsa a fili tana bin Ayar tana maimaitawa cikin kuka. Kuka sosai Safiyyah ke yiwa Zayyan a cikin motar har saida kukannata ya soma rikitashi, yace cikin rawar murya. “Safiyyah