← Book details Heart Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 29

Sashe 6

Heart Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

haihuwa wane irin hukunci zasu yi mata? Tunda dai taji ana daga baya sai ta tuba ta shiga rudani. Amma as a desperate and hopeful as she is da haihuwa, sai tace bari dai ta daure, in har zata samu haihuwa shi Allah Gafurun Raheemu ne. Daidai lokacin da suka isa dan karamin kauyen, daga can nesa Ammara ta faka motar tace gangarawa zasu yi cikin gonar can dake gabansu, har su tadda waccan bukkar da suke hange daga nesa. Haka suka dage zannuwansu sabida duwatsu suka soma taka tudu da gangare suna shiga cikin gonar. Cikin sa’arsu basu sha wahalar samun dogon layi bama, mata biyu suka tarar akan layin, don haka suka zauna har suka gama suka fito kafin suma suka saka kai a bukkar. Jikin Safiyyah ya soma sanyi da ta yi arba da irin abubuwan dake cikin bukkar, da babu kwana-kwana ko wani shatale-tale sun fi kama da kayan tsafi. Babu Ayar Alqur’ani ko daya ko Gafakarsa, irin na shigifar mahaifinta, wanda shima yake amsa sunan malami kuma ake zuwa wajensa neman taimako. Nan Qaho ne da kawunan matattun dabbobi, can korrai ne da busassun matattun tsuntsaye, da fatun namun daji babu kyan gani sai doyi suke, korayen cike da wasu bakaken abubuwa marassa kyawun gani a cikin kowacce kwarya suna motsi, wanda hakan ya baiwa bukkar smell mara dadi mai hamami da wari, daga saman bukkar kuma an sakale konannen kan Damisa, abun dai zallah kyankyami. Saida ta hadiye numfashinta. Wani dukunkunannen mutum ne zaune a kan fatar Akuya, dan tsurut dashi kamar (Dwarf) wato (Wada). “Ku koma ku shigo da kafar hagu, kuma kada ki kara yi mana sallama. Tuni ai Tsimbirbira ta san da isowarki Safiyah ‘yar Usmanu da Hafsatu matar Zayyanu”. Bokan yace da Safiyyah cikin fushi. Saura kadan Sophie ta saki fitsari a wando, ko ta taka da gudu ta koma. Ammara ta gane hakan, sai ta rike hannunta cikin karfafawa ta jata suka koma suka yi yadda yace din. “Maraba – lale da uwargidan Zayyanu. Magajin Bello Rafindadi masu kashin arziki na gidaje har ‘ya’ya da jikokinsu. ‘Ya’ya tsakaninki da Zayyanu akwai su, saura taki kadan su riskeku. ‘Ya’Ya fal! Har sai kince sun isheki”. Safiyyah ta kara tsurewa, jin ya ambato sunan wadanda suka haifeta da Zayyan, kuma har sana’ar gadon gidansu Zayyan din ya sani, zuwa yanzu ta fara gayawa kanta gaskiyar lamari gidan BOKA ta kawo kanta, bama na malaman Tsubbu ba, irin masu aiki da aljanu da rauhanai don gani har hanji, wadanda kullum Malam yake gaya musu ziyartarsu don neman biyan bukata halakace babba. Domin mu’amala dasu “shirka ne”. Suka yi zaman Rakuma a gaban sa, kamar masu neman gafara. Ammara tace da shi “itama dai ba sai na fada ba na sani, tazo neman haihuwa ne itama. Allah ya taimaki Tsimbirbira a taimaka mata, saboda yadda naji dadin taimakon da aka yi min na cika alkawarina na kawo duk mai bukata. Itama gata na kawo ta Tsimbirbira ta share mata hawaye (wa’iyazu billah). Haihuwa kawai take so, walau mace walau namiji, da gaggawa”. Tsimbirbira ya fashe da dariya yace “tuni ai labarinta ya iso garemu da bukatarta tun kafin isowarta. Abu daya zuwa biyu muke bukata daga gareta; jan zakara da jar kaza (fingi-fingi) da za’a hada kwanciya, sai kuma kwan haihuwarta da maniyyin mijinta. Za’a yanka bunsuru a baiwa Tsimbirbira jinin, mu zamu dauki kwan haihuwarta da kanmu, bayan kwana biyu kuma zata dawo ta kawo mana na mijinta, wanda shine mahadin da za’a hada maganin da zan bata. Shekara bazata zagayo ba sai ta haifi ‘yan biyu maza biyu zar”. Safiyyah was shocked and frightened yanzu kam, don ta gama amanna ta kusa fita daga addinin musuluncima gabadaya, saboda rashin tawakkalin ta da Zayyan ya jaddada mata karba da muhimmancin yinsa ga musulmi. Kamar yaya ta bada kwan haihuwarta ta ina za’a dauke shi? Da sperm din Zayyan kuma, ko ta wace hanya hakan zata yiwu? Don haka ta juya a firgice ta dubi Ammara da fuskar tsoro da firgici mai yawa. Nan Ammara ta kashe kunya tayi mata bayanin da a baya bata yi mata ba dalla-dalla. Ta yi mata ‘yar rada (whisper) a kunnenta. “Ai dama na gaya miki sai an dan kauce hanya, sannan za’a samu biyan bukata, ke zaki san yadda zakiyi ki kawo masa duk abinda ya bukata, na jikinki kuwa zaku shiga daga cikin shigifar can ne ya dauka, ta hanyar saduwa dake! Mijinki ba ganewa zaiyi ba”. Safiyyah ido ya raina fata. Boka ya mike ya shige dan dakin wai yana jiranta, ta bishi da kallon razana da firgici mai yawa cikin kyawawan idanunta. Ammara ta shiga convincing dinta cikin kyakkyawan lafazi cewa “is just a simple thing, bai fi ya tara dake na ‘yan mintunan da basu gaza biyar ba, kokari zaki yi kawai ki jure ki daure warin jikinsa, don kin ganshi dan tsurut dinnan amma ba karamin fitinanne bane, and you will enjoy him morethan your husband…..”. A wannan lokacin ne Safiyyah ta samu kalmar “Innalillahi wa’inna Ilaihi Rajioun” ta fado cikin kwakwalwarta, bakinta kuma yayi maza ya kama, ya furtata a fili.
Chapter 6 · 0% Book details