Sashe 22
Heart Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba. Bata gado halin kowa cikin mu ba tsakanin ni da Haj. Nana wajen sanin abinda ya kamata a rayuwa. Halinta na son kyale-kyalen duniya sai ince a rariya Azeezah ta tsinci abinta. Yace daga Ashraf sai Aman sai ita. sai kuma autansu Saifullahi, suke nan yake dasu a gabansa yanzu. Babban dansa Walid ya jima da rasuwa a dalilin cutar koda, haka mai binsa mace Taqiyyah ta rasu gun haihuwa. Zayyan ya muskuta cikin jinjina labarin Azeezah da mahaifinta yake bashi, a cikin yanayin sautin Baba Murtala yana nuna matukar bakin cikinsa da damuwarsa akan halayen diyar tasa cikin karyewar murya irin ta mahaifin kwarai da ya damu da tarbiyyar ‘ya’yansa, ya kuma tsaya ya karancesu sosai, dukkan dabi’unta yace ko kadan baya sonsu, kuma basa masa dadi a rai, ba yadda zaiyi da ita ne, ya kasa canzata, da ana sayarda halin kwarai da ko nawa ne ya saka ya sayawa Azeezah ya canza mata halayenta, sai Zayyan yace a ransa. “Allah daya gari bambam kenan! Ita wannan komai nata ‘opposite’ din na Nana Safiyyahrsa! Sophie abinda bata so kenan wato kwalliya, gayu da kyale-kyalen zamani, Safiyyah bata damu taji dadi ba, ita dai tayi ibadah, kuma ta kan ce duk wani abu da zai janyo mata idon mutane kanta, ko ya zame mata kyalkyalin da zai ja hankalin maza a kanta, ko ya janyo idon mutane gareta wanda har zaisa suyi mata kallo na biyu, bata maraba dashi. Watau Safiyyah bata son ta burge kowa don a wurinta ido guba ne. Komai da Baba Murtala yace halin Azeezah ne sai ya ganshi kishiyar na Safiyyah in one way or the other. Duk yadda ya so ya yakice tunanin Azeezah da labarinta tun a wurin hakan bai samu gareshi ba. Har karanta wasikar jaki yakeyi shikadai. Yana comparing and contrasting halayen nasu. Yace Safiyyah mai kokari ce, kuma zaqaqura a harkar, karatu abin mamaki ita kuma wannnan Babanta yace dakikiya ce. Safiyyah mai gudun duniya wannan mai matukar son duniya, da son jin dadin dake cikinta. Yayinda Sophie ko kadan bata damu da jin dadi ba. Baudaddun halayenta da yaji daga bakin Babanta yana mai kuka dasu, shi a matsayinsa na namiji sai suka bashi sha’awa, sabida wasu exceptional characteristics ne da bai saba ji ba, akwai abin so da sha’awa a cikinsu duk da haka, is rare a samu irinta, shi sai yaga ba matsala bane halayen nata face abin sha’awa tunda mace ce. Karewa ma su suka ja masa wani sabon attraction akan Azeezah Murtala, wanda yasa ya shiga damuwa da lamarinta, madadin yaji baya sonta ko ya tsani halayen nata. Kwalliya ai abar so ce ga Da namiji, haka yake so Sophie ta koma, mace ‘yar zamani mai ji da class da gayu, amma ita kullum sai Hijabi. Yayi ta tunanin yadda yaga Azeezah take twisting jikinta in tana tafiya kamar tarwada a cikin ruwa, kai kamar da gayya take juya lafiyayyun cikakkun mazaunanta suna wani girgiza cikin tafiyar da hankalin mai kallonsu. Tunanin halittar Azeezah da ya samu kansa ciki ya kuma dinga yi masa dadi ne yasa bayan ya koma masaukinsa, sai kawai ya kwanta rigingine ya ki kunna wayoyinsa kwata-kwata, don ma kada a katse masa tunanin da yake ciki a lokacin. Yanata karfafa kansa kan me zai hana ya gwada yiwa Baba Murtala maganar ya bashi diyarshi Azeezah ya aura? Shi yana son kwalliyar, yana son kyale-kyalen nata, shine abinda ya rasa a nasa iyalin, da kuma….. Azeezah kawai ta burgeshi. Kuma ga dukkan alamu AZEEZAH MURTALA ta hada duka abubuwan da ya rasa a gidansa. Safiyyah ta fado masa a rai, a lokacin da yaji kwanyarsa ta lullube da tunanin auren Azeezah, yana ta tuna jerarrun hakoranta, kissable lips dinta. Wani irin a jere ya hau sakin ajiyar zuciya ba sassautawa, yana gayawa kansa koma wane irin tunani ne ya samu damar kutsowa cikin rayuwarsa akan wata diya mace daban bayan Safiyyah a yau, Safiyyah ce sila, ita ta bada kofa, ta bashi dama, ita ta jawo masa koma menene. Data watsar dashi daren jiya ya kwana da fushinta, ta barwa matan duniya shi akan titi suke daukar hankalinsa, taki alkinta masa sha’awarsa, sabida rigimarta na son wata haihuwa da bata isa ta baiwa kanta ba, karshe ta barshi stranded (a ragaice) bisa titi yana satar kallon ‘yammata. Hausawa ma sunce “sai bango ya tsage kadangare ke samun kafar shiga”. Don haka kara aure da diyar Baba Murtala gareshi yanzu ba zai zama laifi ba, don kare kansa daga fadawa wani hali na daban. Shi kadai yasan yadda ya wayi gari jiya da Sophie ta juya masa baya taki tallafarsa. Sophie taki ta gane shi mai tsananin son kasancewa da mace ne, haka halittarsa take, son samu matarsa Safiyyah ta daina saka kunya irin wadda ita Safiyyah ke sakawa a tsakaninsu, tayi kokarin gyara (sexual life) dinsu, ta maida hankali a kanta fiye da komai ta hakura da batun haihuwa tunda Allah bai ga damar basu ba, amma a’ah ita Sophie yanzu ba soyayyarsa ce a gabanta ba, kullum hankalinta naga kulafucin son samun Da tareda shi, ita dai ta samu haihuwa ta kowacce hanya, hankalinta ya tashi daga kan wajibinta (kula da aurenta) zuwa abinda ba wajibi ba (neman haihuwa). Haihuwa idan Allah bai ga damar bata ba wa ya isa ya bata? Yayi duk iya kokarinsa akan Sophie ta yarda da hakan abu ya faskara. A wannan lokacin Arch. Zayyan Bello, ya tabbatarwa kansa cewa yanada bukatar kara aure, musamman da yake da tabbacin kowa zai aura zata bi bayan son da yake yiwa uwargidansa Safiyyah ne. A duk yadda nature din Safiyyah yake yana son abarsa a haka, yana darajjata, yana daukaka martabar al’amarinta a duniyarsa da cikin rayuwarsa fiyeda na kowacce mace, bayan wadda ta kawo shi duniya (Mama), amma yau ya tsinci kansa dumu-dumu da son kara aure bayan Safiyyah, amma ga wani hanzari; macen duk da zai aura, zata zamo masa matar biyan bukatar gangar jikinsa ne kawai, sabida ta wannan fannin Safiyyah ta gaza, amma soyayyarsa da kaunarsa har abada suna ga “stammerer Hijabhie dinsa ta gargajiya wato Arch. Safiyyah Usman Dandume”. Sannan kowacece Allah ya rubuta zai aura, ko da kuwa Azeezah dince ko watanta, idan ta haihu Safiyyah zai kyautarwa abinda ta haifa, in sha Allahu. Wannan wani alkawari ne da Zayyan yayi da zuciyarsa yau, bayan samun kansa da sha’awar kara aure, zai haifi Da da matar ya mallakawa Sophie, in dai Dansa ne halalinsa to zai kyautar dashi ga Safiyyah. In fact, sai sun yi da wajewa/yarjejeniyar nan da kowacece Allah ya rubuta masa zai aura, kafin ya yarda ya aureta. Zai fito fili ya gaya mata shi ba don rashin haihuwar matarshi ko rashin sonta ne yasa zai kara aure ba, kawai dai…. Kawai abar kaza cikin gashinta inji Zayyan, amma ‘infatuation’ na son kara aure ya sameshi, irin wanda ka iya faruwa da kowanne lafiyayyen Da namiji, mai cikkar lafiya da cikkar kurucciya kamarsa, ga wadatar arziki da yalwar jin dadin duniya da yake ciki a wannan lokacin, yana da damar auren mace fiye da daya, da addini ya riga ya bashi, duk son da yake yiwa Safiyyah bazai hana shi cika sunnah ba yanzu, watakila yawan son da yake mata shi yake sawa Safiyyah ke ganin yana matsa mata, soyayyarsa ta yi mata yawa, shi kuma ke sakawa take garashi yadda takeso in yazo da bukatarsa gareta kamar ta samu gare-gare abin wasan yara. Ya tuna rabon da ya gaisa da Mama Fatu yau kwana biyu kenan, don haka ya kunna daya daga wayoyinsa da ba’a sanshi sosai da layin ba, don ya kira Mama su gaisa, Safiyyah kam ya riga ya bata hutu bazai ko kirata ba.Amma yana kunnawa sakonta na shigowa har guda uku a jere. A cikin sakonta na farko afujajan take tambayarsa saukarsa lafiya a jihar Ikko, da yanda ta damu da ya bude waya taji lafiyarsa suyi magana ko yaya ne. A sakonta na biyu kuma tace “tayi regretting laifinta, tana so ya bata dama ko yaya ne in ya dawo tanaso suyi magana, ya bata dama tayi repenting. A cikin sakon ta gaya masa uzurinta na ranar ‘mood swings’ ne irin na zuwan al’ada (jinin haila) amma tayi nadamar yadda ta kasa yi masa bayani ko biyar dashi ta yadda zai fahimta!” ‘I’m so SORRY Habibiyyyy!” Zayyan kasa bata amsa yayi, ya kuma kasa kiranta, yana blaming dinta da duk wani hali na sha’awar Azeezah daya riga ya tsinci kansa a ciki yanzu babu gaira babu dalili. Ya share Safiyyah bai bata amsa ba, domin hakika ta kai shi bango har fiyeda zatonta, maza zasu iya jure kowanne irin bahagon yaren matansu amma banda (sex denial). Duk da haka shi Zayyan ya tabbatarwa kansa a kowanne hali kuma cikin kowanne yanayi sunansa Arch. Zayyan Bello, mijin Safiyyah Usman Dandume, babu abinda zai canza title dinnan, balle har don tayi masa wani laifi ya canza mata shi, ko ya canza matsayinta a wurinsa…. Kullum yana gayawa kansa ya dinga yiwa Sophie uzuri, uzuri sau saba’in kafin yayi mata hukunci da tauye hakkinshi a shimfida da take yi yanzu, tunda a can baya ai ba haka take ba (while she was in her twenties). Tsananin son haihuwa data sakawa ranta a yanzu da frustration na rashin samunta, shi yake ta canza halayenta daga (normal behaviors) dinta daya riga ya shaida zuwa wasu halaye kala dabam, da sukasa ta fidda ranta akan kowa da komai har dashi kansa. Domin a halin yanzu Safiyyah ta kallafa ranta a kan son samun Da dashi ta kuma baiwa son haihuwar muhimmanci har fiye da soyayyarsu mai tarihi da kuma rayuwar auratayyarsu. Ya kira Mama ne da niyyar su gaisa kawai, don sun kwana biyu basu gaisa din ba. Mama Fatu ta amsa da farin cikin jin muryarsa, don sun kwana biyu basu yi waya ko ganin juna ba, bai je Katsina ba, Mama ta kira sunansa “Baffan Mama!” tana cewa cikin tsokana. “Ni Baffan Mama ina ka shiga ne kwana biyu ko wayarka babu balle kyallinka? Ko Hakimar taka diyar Alaramma ta murza kambu, ta hanaka zuwa Katsina wannan watan kwata-kwata?” Yace “haba dai Mama, haba don Allah, nifa dadina dake kenan, zargi da zato mara