← Book details Heart Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 29

Sashe 25

Heart Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

son aurenki bisa yarda da amincewarki”. Maganganun nasa sun ki zauna mata daidai a kwanyarta, don jinsu ta ke tamkar rainin wayo. Amma me? Zayyan din ya zo da karfin chemistry din da ya fizge zuciyarta nan da nan zuwa gare shi, har ta ke jin ba za ta iya ce masa dole sai ya takura kansa ya furta mata abin da ta ke son ji ba, tunda dai ya ce babu namijin da zai zo neman aure a inda babu burbushin soyayyar mace a ransa. Zayyan ya katse mata tunanin da ya jefa ta da cewa, “Can I go ahead Azeezah? Kin yarda iyaye su shigo cikin lamarinmu, in sanya ki cikin iyalina?” Azeezah ta juyar da kai gefe, zuciyarta na bugawa da shigar SO farat daya, babu bata lokaci zuciyar tace itafa ta yi na’am da dan mutanen Rafindadi. Ko ma dai me yake nufi da cewa ta yi masa uzurin jinkirin kalmar soyayya zuwa wani lokaci za ta yi wannan uzurin, domin ta tabbata wuyarta a yi auren, tunda har ya kawo kansa ya yi confessing na neman amincewarta da bakinsa. Tana wannan tunanin, ya sake maimaita tambayarsa na neman yardarta har ya ce, “Kamar yadda ki ka gani ni ba yaro ba ne Azeezah, ba zan iya long dating dake ba, I truly admire you, ki ba ni yardarki”. Sai ta samu kanta da gyada kai kawai, ta kuma tambaye shi ko yaransu nawa shi da maidakinsa Safiyyah? Zayyan ya dan ciza lebensa cikin ‘yar damuwa kafin ya ce. “Muna fatan Allah ya kawo su nan gaba. In kuma daga wajenki Allah ya bamu, ina neman alfarmar ki baiwa Safiyyah ko me ki ka haifa na farko. Na tabbatar miki za ta yi masa rikon da ko ke ba za ki yi masa ba tunda Da na ne. Za ta yi masa tarbiyyah irin wadda ko ke ba za ki yi masa ba. Za ki yi mana wannan alfarmar Azeezah?” Wani abu a halin Azeezah shi ne, ba ta boye abin da ke ranta. Ita ma bata so a boye mata. Ko kuma tarin kuruciya ne ya debe ta a wancan lokacin? Har ta yi masa alkawarin yi masa wannan alfarmar. Ta ce, “Allah da Ya halicce ni bai yi ni da son hidima da hayaniyar yara ba. Amma zan so in san kai da ita din waye mai matsalar haihuwa, don ka ce min kun yi kusan sama da shekaru goma tare?” Wani abu da ba zai iya ba shi ne, yin zancen nan da wani, wanda ya kasance sirrinsu shi da Safiyyah, don haka ya ce da Azeezah, “We are all fit and healthy Azeezah, muna jiran hukuncin Ubangiji a kai. Now, tell me about your samari? Su nawa ne?” Azeezah ta yi wata ‘yar shashashar dariya ta ce, “To me ye ruwanka da su "Dan Daddy?" (sunan da ta sa masa kenan, wato dan Babanta Alhaji Murtala, don Baban ma ce masa yake Dan wajena, tun ba su hadu ba ta sha jin yana ma mamansu Hajiya Nana zancensa), tunda dai kai Allah ya kashe ya baiwa Azeezar?” Sai bayan ta fadi hakan cikin subutar baki sai ta ji kunya sosai, shi kuma Zayyan sai kansa ya kumbura. Abinka da namiji a hannun wayayyar yarinya, tuni Azeezah ta sa ya sake da ita, ta bashi labarin ita cikin masu sonta mutum daya ne soyayyarsu ta yi nisa a makaranta, wato wani mai suna Faris. Sun hadu ne a Cyprus. Bayan dawowarsu daga karatu ya zo nan gidansu zance, Baba ya ganshi da wani (haircut), wanda bai masa ba. Tun daga ranar Baba ya saka masa karan-tsana, wai askin ‘yan iska ne akansa kada ya kara zuwar masa gida”. Dariya sosai Zayyan ke yi, Azeezah ta dauki hankalinsa sosai da salon maganarta ta 'yan gayu, ga iya Hira, musamman yanayin yadda ta ke magana cikin rangwada da karya kai, har da yada hannuwa cikin salo mai daukar hankalin da namiji. Ya ce, “What I want to know now (abinda nakeson sani yanzu?), ke kina son Faris din, ko kuwa Babana yayi miki kancal ne daya koreshi?” Ta yi masa wata hararar love, ta ce, “In ma na so shi, to kafin in dora ido a kan Dan mutanen Rafindadi ne, shi kam sharp shooter ne, tuni ya sa na manta da kowa har ni da kaina ina mamaki”. Zayyan ya mike ya iso inda ta ke zaune, ya dan tsugunna kadan saman kanta, ya dafa hannun kujerar da ta ke zaune yana murmushi. Azeezah ta shaki ultraviolet dinsa sosai, wanda ya riga ya kama jikinsa da ya fesa ko bai fesa ba, har ta kusa shidewa a wurin don wata soyayyarsa mai dadi data kara kamata. Ya ce, “Insha Allah ni kuma na yi miki alkawarin ba za ki yi nadamar zaben Dan Rafindadi a matsayin abokin rayuwarki ba. In dai za ki girmama min Sophie, za ki taya ni lallabata da martaba ta to in sha Allah zamu zauna lafiya. Ina tabbatar miki za ki same ni fiye da yadda kike so, ko kike burin samun abokin rayuwarki”. Tun daga ranar soyayyar shi da Azeezah ta kullu a gidan mahaifinta, kullum suka dawo aiki shi da Baba, to a falon da aka ware musu yake yada zango can Azeezah za ta kai mishi abincin ranar shi dana dare. Tuni Hajiya Nana ta daina hada mishi kwano da Baba, har ranar Baba Murtala ke masa tsiya da cewa, Azeezah mai yankan kauna, haka kawai ta raba mishi kwano da dan wajensa. Baba Murtala da Mama Fatu sun fi kowa farin cikin wannan al’amari, don kafin ya gama kwanakin aikinsa a Lagos Mama da Azeezah sun gaisa a waya a gabansa ya kai sau uku. Hajiya Nana kam bata so ba, musamman jin Zayyan yana da mata, amma ganin yadda ‘yar da uban duk suka mika wuya, sai ta sallama musu. Amma kwarai ba ta son Azeezah da auren mai mata, don ita kadai ta rayu a gidan Alhaji Murtala tun daga kuruciya har girma. Kuma Azeezar nan ita kadai ta rage musu mace a gabansu. Sai dai ta san Hajiya Fatu irin farin sani, a matsayinsu na matan abokan juna tun kuruciya, ta san Mama Fatu tun Architect Bello na raye, kuma a saninta ba ta da wata matsala da mijinta da al’umma, wannan ne ya yi convincing amincewar Hajiya Nana Aisha, don Mama ta kira ta officially ta ce ba jimawa za su kawo lefe. Namiji kenan, duk inda yake sunansa namiji in dai a kan mace ne, ko idan ya so kara aure. Shi kansa yana mamakin wannan al’amari domin bai taba planning dinsa a kamus din rayuwarsa ba. Rabonsa da ya kira Safiyya, ko ya saurari kiranta da sakonninta tun saukarsa a Lagos, da tozalinsa da ‘yar Babansa Alhaji Murtala. Kullum da dare kusan kwana yake yana questioning kansa, yana mai kalubalantar kansa a kan wannan hukuncin da ya yanke. Amma ba ya bari tuhumar ta yi nisa yake kare kansa ta hanyar gaya wa kansa hakan shi ne kadai solution ga dukkan matsalolinsa da Sophie. Allah sarki Safiyyah, tana can Abuja amma ruhinta yana Lagos, cikin damuwar canjin farat daya data samu daga Habiby dinta, wai yau Habiby ne ko wayarta ya daina dagawa kuma bai kara nemanta ba har kwana takwas da tafiyarshi, a kan laifin da a ganinta bai kai ya kawo ba. Shin me ta yi masa haka ma da zafi ne? Ba yau ta soma rejecting dinsa a auratayya ba, amma bai taba daukar abin da zafi irin wannan karon ba. Ba ta da masaniyar yana can Lagos yana banzar soyayya da diyar ubangidansa, wadda cikin dan kankanin lokaci ta kunce masa lissafi, ta sauke masa hadda. Ba ya ko tunawa sosai da Sophie sai ya zo kwanciya bacci, to yanzun ma saboda wayar tsakar dare (midnight call) da suka tsiri yi shi da Azeezah ba ya ko samun lokacin da zai yi missing dinta cikin dare. Abun da ya sani shi ne, son Safiyyah a zuciyarsa daga Allah ne, babu mai maye gurbinta. Babu mai tumbuke matsayinta, amma ya rigada yazama attracted and highly infatuated ga son auren Azeezah.
Chapter 25 · 0% Book details