Sashe 20
Heart Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
haihuwa zai ke sa in yi ba…..”. Ta fada masa hakan cikin kuncin rai, tareda kankame jikinta waje daya, har da kyallin hawaye cikin idonta da yake iya gani ta dan hasken fitilar dim light. Wannan maganar data fada ne tasa ya fusata, ransa ya baci, komai ya fita kansa, saiya janye jikinsa ya juya mata baya, yayi rub da ciki bisa cikinsa ya rungume hannuwansa a kirjinsa, domin Sophie ta gama kular dashi. Zayyan ya rufe idanunsa yana yaki da zuciyarsa mai cewa ya saka karfinsa na da namiji yau a kan Sophie kawai, ta haka ne zai goge rainin da ya fahimci ya fara samun muhalli a tsakaninsu, wato ya kwaci hakkinsa kota wane hali jikin Safiyyah tunda dai Allah shaida ne kan bashi da wata matar sai ita, baida inda zai je ya sauke wannan bukatan sai gurinta. Ga tafiya ta sati har biyu a gabansa. Wata zuciyar na tankwarashi da cewa “Sophie ce, His alter ego! Matsayinta ya wuce (marital rape) a gareshi, kada Allah ya nuna masa ranar da zai sakama Safiyyah karfi, don biyan bukatar ransa ko saboda hutun gangar jikinsa, yace a ransa wato lamarin mace babu abinda ya kaishi ban takaici da ban haushi wani lokacin, musamman idan kayi saken da ta san karfin soyayyarta a ranka. To daga sannan ka gama shiga uku, ka gama yawo a hannunta. Yace a ransa to ita Safiyyah bayan sanin weak point dinsa data riga tayi, cikin lamarinta na yanzu harda rashin godiya, tunda ta ina ya rage ta ko ya kuskure ma nata bukatun data kasa haihuwar, har da zata gaya masa bakar magana haka, wai tarayyar su ta auratayya kullum bata sakawa ta haihu? Wannan maganar ce tasa ya hakura, ya juya mata baya shima amma ya kasa ko runtsawa a daren har goshin asubahi. A takaice Zayyan shi kadai yasan irin azabar da ya dandana shi da zuciyarsa a daren yau. Amma Safiyyah ko a jikinta, tace banda sawa da yake tayi tana jika gashinta yana kakkaryewa kullum saboda yawan wanka, ita wahala abin yake bata yanzu, saboda bata yin komai cikin dadin rai kamar can baya. Hankalin ta ya bar kan soyayyar miji, kacokam ya koma na soyayyar samun Dan kanta. Abin ya fita kanta kwatakwata tunda bai sawa ta samu cikin haihuwa. Kamar akan dole take bashi hakkin nasa yanzu, tun bayan haihuwarta. Wanda hakan ya jefa shi a damuwa da rashin samun satisfaction da ita yanzu, idan ma ta kyale shi din kenan, baya samun yadda yake so daga gareta, don ta dauke zuciyarta daga kan sexual life dinsu, ta mayar kacokam kan son haihuwa. Da safe ta hada masa breakfast amma ko kallonta bai yi ba itada tebirin breakfast din nata, ya dau wanka da karin guga, ya murza hadaddiyar hular ‘Tonak’ a saman goshinsa, kai sai ka rantse da Allah ba shine ya kwana begging matarshi yana matse ciki tana jansa a kasa ba sabida yadda yabi ya daure fuskar nan tam. Ta gaisheshi, karo na farko da yaki amsa gaisuwar Sophie ta safe, a tsayin shekarunsu goma da aure. Bata damu ba, ta hau gyaran dakin da suka kwana tana fadi a ranta Zayyan sai da haka, in ba haka ba tsofeta zaiyi da kwarzaba irin tasa don baya gajiya, tun bata ajiye masu yi mata addu’a ba. Ya dauki ‘brief case’ din shi ya fice, sai ta ‘text messege’ ya gaya mata ya kama hanyar Lagos, a takaice ya gaya mata zasu fara project din da ya gaya mata shi da Baba Murtala. Bata ga text din nasa ba sai bayan ya jima da barin gidan, har ya shiga jirgi lokacin, jikinta kuma sai yayi sanyi lokacin data karanta, bata san tafiya ce dashi ba, ta kuma ga rashin kyautawarta ga Habiby dinta koda ace ba tafiya zaiyi ba, wannan ne karo na farko daya taba yi mata sallamar tafiya wani gari a waya. Ta ji babu dadi har ranta, anya Zayyan ya cancanci unfavourable treatment din da take masa a satinnan, don kawai bata jin dadin zuciyarta kan rashin haihuwa sai ta huce komai a kansa? Kada dai ya kasance shaidan ne yake yi mata ingiza mai kantu, don ta zama butulu, ungrateful ga ni’imomin Ubangiji a gareta, ta zama mara godiyar Allah da rashin gode masa bias alfarmar mijin kwarai daya bata? A take jikinta ya kara yin la’asar, ta yi maza ta shiga kiran layukan wayarsa, amma cikin rashin sa’a a lokacin Zayyan ya shigar da wayarsa ‘flight mode’ don ya shiga jirgi ha ra zarga belt, ya kashe dukkan wayoyinsa. Bai kunna ba har saida ya sauka a filin jirgin Murtala Mohammed, inda ya tarar da “Seyi”, direban gidan Baba Murtala kenan ya na jiran saukarshi. Seyi ya dauke shi da trolly dinsa zuwa gidan Arch. Murtala Babangida dake Ikoyi, da bacin ran Safiyyah fal ransa. **** **** ****