Sashe 28
Heart Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Zayyan yayi ya shige toilet. Wajen wankan ma ita ta surka masa ruwan wankan, ta zuba turaren wanka mai dadin kamshi na desire dunhill a cikin ruwan, sannan ta ajiye masa bath gel dinsa na Cien a gefe da farin tawul, ta juya za ta ja masa kofar, sai ya riko hannunta cikin marairata da karaya. “Sophie, karasa ladanki mana ki cuda min baya… na rantse ba ni da karfi yau”. Dariya ta yi ta ce a ranta, za ka ji karfin sai zuwa dare inta iso”. Wani abu kamar daci-daci a makogaronta ya taso mata, wani tukuki ya turnuke zuciyarta, don haka ta yi saurin janye hannunta daga cikin nasa ta fice ta rufo masa kofar, tana neman hadiye abin nan da ya yi mata tsaye a makogaro, amma ta kasa. Tana bude baki don yin magana kuma ta san fashewa za ta yi da kuka, ko harshenta ya lankwashe ko ya karye gabadaya, don haka yi masa shirun ta fice da gudu-gudu shi ne mafi alkhairi a gareta. Ya yi wankansa tsaf, ba karsashi ko na kwabo a jikinsa, musamman saboda shirun da Safiyyah ta yi masa. Ta kuma yi tafiyarta daga toilet din ko kallonsa bata kara yi ba. Yana shiryawa a dakinsa cikin wata sabuwar bugaggiyar shadda ‘yar ubansu wadda Baba Murtala ya dinka masa don fitar daurin aure. Yana so ya kira Sophie ta daura masa links na hannun rigarshi da maballin wuyansa yadda ta saba, ya ji nauyin hakan ya kyale ta. Ko ba komai ta yi masa kokarin da ‘psyche’ dinsa bai taba bashi ba. Da ya kammala shiryawa ya same ta a dakinta tana faman fiddo kaya daga wardrove tana shiryawa duk don ta maida kanta busy, ta hana kanta zama shiru balle wani mugun tunanin ya sarke ta. Daga bakin kofa ya tsaya hannayensa biyu zube cikin aljihu, ya yi kokarin su hada ido, amma Safiyya ta ki. Ta cigaba da ninke kaya. Ba ya son ya taba jikinta kada ya jangwalo rauninta, don haka ya yi magana daga inda yake tsaye. “Mun wuce Masari daurin aure sai wajen dare kuma in taron mata ya watse zan dawo Sophie”. Safiyyah ta hadiye miyon bakinta ta ce. “Ällah ya sa a daura a sa’a, Allah ya sa abokiyar arzikinmu ce, Allah ya bada zuri’a mai albarka da ake nema..…” Wadannan kalaman na karshe ta karasa su ne cikin rawar muryar da ba ta so rauni ya fito a cikinta ba. Shi kansa ji ya yi ya kasa daurewa, don haka ya shigo cikin dakin sosai ya karasa ya rungume ta, ya ce. “Ina rokon Allah ya sa zuri’ar nan ta fara samuwa daga gare ki Sophie, ina kara rokonSa ya fidda ni kunyarki wajen adalci. Ina jaddada rokona gare shi da Ya ba ni zuri’ar nan tare da ke komai rashin yawanta. Kada Allah ya nuna min ranar da zan fifita wata a kanki, a dalilin haihuwa…” Su duka jikinsu da muryoyinsu rawa suke yi, Safiyyah na amsawa da "ameen". “Allah ya fara kwantar da babyna a nan..." (ya sanya hannu kasan mararta) kafin kowacce mace ta samu wannan babbar alfarmar…...” Fatar bakin Safiyyah na rawa ta kara amsawa da "ameen". Da tsakanin mutuwar jiki Zayyan ya bar dakin Sophie, yayin da Safiyyah ta yi zaune dirshan a gefen gadonta ta sanya fuskarta cikin tafukanta rike da singlet dinshi da ya cire, ta cukuikuiye fuskarta a cikin singiletin, amma ba kuka ta ke yi ba. Karfe hudu na yammacin ranar waliyyai suka daura auren Arch. Zayyan Bello Rafindadi da Azeezah Murtala Babangida, bisa sadaki na burga, wanda Mama ta bayar na wara-waran zinare manya guda uku. Daga nan aka wuce reception na maza, already amarya tana Abuja tun jiya gidan mahaifinta da ke Katampe. Sai yamma lis ya dawo Abuja, kuma ko da ya sauka a Abuja bai shiga gidansa ba Park din cikin Estate din ya nufa ya tsaya a jikin ‘railer’ yana tunani, daga baya ya wuce gidan amininsa Habibu Nahuce, daidai lokacin da aka kawo amarya Azizah dakinta. Abin kunya har da Yaya Zubaida aka yi shimfidar gadon amarya, su Zaitoon kuwa sai yada ma Safiyyah habaici ake ana cewa, uwargida sai kin yi hakuri fah, ah toh Azeezah ‘yar babban gida ce shi ya sa za ki ga komai nata daban. Kada ki ga furnitures ubansu ‘yan Dubai ki dauka Yaya Baffa ne ya saya mata. Kin san da uba ake ado ba da miji ba”. Kasancewar Aunty Dije ta zo ma Safiyyah dannar kirji a ranar, ta kuma ji me suka ce, sai ta tashi zaune daga kishingidarta, a ranta tace lallai Zahra da Zaitoon basu da kunya, sai ta ce musu, “Kun manta kuma wani lokacin abin an ce abin fini uba in fiki miji ne? Allah na tuba Safiyyah tun asalinta ba ta son tarkace ita, dan English parlon nan nata ya ishe ta, tunda ba ‘yar sarki ba ce, ba 'yar gwamna ko shugaban kasa ba, a'a ita diyar magada Annabawa ce, wadanda duniya bata gabansu”. Zaitoon ta shaka sosai sai ta bar dakin. Aunty Dije ta ce, “Marasa kunyar yara kawai, Allah ya hada ku da dangin miji masu irin halinku”.