← Book details Heart Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 29

Sashe 18

Heart Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da Mama ke musu sai kawai ta bude baki tace. “Wai ni kam Haj. Fatu, Safiyyah har yanzu bata haihu ba ko?” A gaban kawayenta Mama tace “tayani tambaya, shiru, har yanzu, tamkar Malam yaci shirwa”. Haj. Yabi ta ce “kuma kuke zaune haka baku tashi tsaye akai ba? A can kan tudu layin gidan iyaye na akwai wani mai bada maganin haihuwa, maganinshi kaifiyyan, in kunaso zan karbo mata”. Sai ta kalli Safiyyah wadda hankalinta ya soma tashi ranta kuma ya soma baci da jin zancen da suke yi a kanta, ai har abada ba ita ba sake neman haihuwa tawata hanyar balle ta hanyar malaman tsubbu, ta riga ta tuba wa Allah da Habibiy dinta, tace bazata sake ba. Haj. Yabi tace. “Diyata Safiyyah ina fatan zaki sha maganin in an amso, don magani ne me tsada. Kar na karba kizo baki sha ba”. Safiyya ta gyada kai kawai amma ko motsi da bakinta ta kasa. Mama ta zucciya da banzan data yi musu, ta daka mata tsawa a cikin mutane tace “baki ji ne ana miki magana kinyi shiru, kar ta kashe kudinta a banza a wofi ta karbo miki maganin baki sha ba. Ni ban ma cika son harkar maganin gargajiya ba Haj. Yabi, nafi yarda da asibiti, amma tunda na matsu na ga diyan Baffa gara a jarraba can din, ba’a san inda za’a dace ba, tunda anyi na asibitin duk ba nasara”. Duk sauran matan suka ce “exactly, gara a jarraba na gargajiya”. Baki daya falon sai ya karade da zancen rashin haihuwar Safiyyah har tsayin shekara goma da aure, kannen sa daga mai biyu sai mai uku, kowacce na tofa abinda take tunanin shi ya hana Safiyyah haihuwa, har da masu cewa ko PCOS gareta, don mafi akasari shi yake hana mata haihuwa yanzu. Safiyyah da kannenta duk sai sukayi jigum-jigum a zaune, suka rasa abinda ke musu dadi, ba zaginta ake ba amma hakan fallasa ne da gori a fakaice, suka rasa abunda zasu ce, duk Safiyya ta tsargu da kanta, taji kamar tayi wani gagarumin laifi ko abun kunya, wanda al’umma ta kasa yi mata uzurinsa, wani irin kuka na takaici ya taso mata. Sabah ta fahimci hakan, tayi maza ta kama hannunta suka mike suka bar falon, uffan basu ce ba. Suna fita Hajiya Yabi ta dubi Mama cikin damuwa tace, “ina fatan dai ba maganar da nayi bace ta bata ran surukar tamu?” Mama tace “oho mata, ita ta sani, daga abun kirki? Yarinya sai kafirin zurfin ciki da nuku-nuku, gata da sumumu-kasau irin nasu na ‘ya’yan Alarammomi da ka kan rasa gane zuciyarsu”. Fitarsu harabar gidan suka ci karo da shi yana kokarin shigowa da hancin motarsa bakar ‘Ford Mustang,’ Arch. Zayyan ya sha adon sallah masha Allah dashi cikin farar shaddah bugaggiyar Wagambari babbar, bugun hannu, ba karamin kyau da kwarjini da kamala shigar yau ta kara masa ba. ta kuma kara fiddo zahirin kuruciyarsa ainun. Da annuri sosai ya shigo gidan, amma yana ganin fuskarta ya gano akwai abunda ya faru da ya canza mood dinta. Suna tsaye a kofar shiga babban falon gidan itada Sabah. Ya adana motar a parking lot na gidansu a nitse, bai fito ba ya sauke glass na barin da yake zaune, sai ya yafitota da hannunsa, yace. “Sabah, ku ara min Yaya Safiyyah mana, ku shiga gida zan ganta, gata nan zuwa yanzu”. Sabah da Rayyah har suna hada baki wajen cewa “Toh! Uncle Zayyan”. Suka juya zuwa cikin gida. Ganin Safiyyah taki motsawa daga inda take tsaye bayan wucewar su Sabah ciki, sai ya fito ya kama hannunta, dole ta bishi kamar rakumi da akala zuwa motar, ya bude suka shiga gidan gaban motar ya rufe, dama glassanta duka masu duhu ne (tinted), motar tana kunne, don haka AC na aiki. Ga kamshin ‘Car fresh’ din motar mai dadin kamshi da ya hade da kamshin turaren jikin Zayyan na mazan da suka amsa sunansu (Ultraviolet), su suka hadu suka dawo da nutsuwa da salama a zuciyar matarsa Safiyyah, ta jingina kanta a jikin kujerar bayanta, ta hau sauke ajiyar zuciya a jejjere, ba tareda ta ko san tana yi ba. A hankali Zayyan ya mika hannayenshi biyu ya rungomota jikinsa, bakinshi a kasan wuyanta ya sumbaceta lightly, yace. “Sophie yaya akayi ne? Wani abu ya faru da bana nan ne? Na ganki moody”. Safiyyah tayi shiru, haka kawai taji kwalla na kara ciko mata, tace “Habiby, ina so in haihu ne, kuma da wuri!” Yace “Yaa Subhanallah! Ita haihuwar nan ba’a hutawa da yin ta? Tukunnama yaushe aka gama jegonta? Kuma shin me ya kawo zancenta?” Daga Safiyyah babu amsa, sai ma idonta daya karasa cikowa taf! Da hawaye. Kiris suke jira su sauka kan kuncinta. Zayyan yayi-yayi ta gaya masa abinda ya kawo zancen haihuwa amma Safiyyah ta ki. Kada ya zama cewa ko ta kai karar Mama da kawayenta wajensa ne. A karshema da ya dameta da tambaya sai ta kifa kai a kirjinsa ta fashe da kuka mai cin rai. Bai iya yin komai ba ko hanata kukan a wannan lokacin, banda ya rungumeta cikin kirjinsa tsam-tsam, yana shafa bayanta a hankali cikin lallashi. Ya kuma barta tayi kukanta ma’ishi, yana magana cikin lallashi, kauna da soyayyah masu yawan gaske, wadda ta bayyana kanta a zuciya da tone din furucinsa, Zayyan yace. “Ki kara hakuri kinji Safiyyah, haihuwa da samun ‘ya’ya duka lokaci ne, in kuma Allah bai ga damar bamu ba…. inaso ki sawa ranki WANI HANIN GA ALLAH BAIWA ne”. Ya fahimci an mata gorin haihuwa ne as usual. Amma kowanene bai kyauta masa ba suna cikin farin cikin ranar sallah, ranar celebration din musulmi. Sai ya kira Sabah a waya yace “ta robar, me ya faru ne da Sophie da bana nan? Kunje wani wuri ne an bata mata rai?” Yasan Rayyah ko kusa bazata fada masa ba, don zurfin cikinta irinna Safiyyah ne, kuma bata da yawan magana, amma Sabah tsaf zai ji komai, har abinda bai tambaya ba, don tasu tazo daya sosai. Sabah tace, “kawai-kawai, daga munzo falon Mama mun sameta da kawayenta mukayi musu gaisuwar sallah, shine wata mata tayi mata zancen haihuwa, nan aka fara zancen rashin haihuwarta, hadda cewa za’a karbo mata maganin gargajiya wajen mai bada maganin haihuwa”. Baki daya Zayyan ya rikice, ransa kuma ya baci, don ya tsani a kuma zancen zuwa gun malamai karbo maganin haihuwa, yace “wanene da wannan maganar?” Sabah tace “oho bansanta ba, amma tana zaune a gefen Mama, wata fara mai jiki haka”. Yace “Maman, me tace toh?” Da yake Sabah bata da tsoro sai tace “ba abunda Mama tace, illa ma cewa tayi ta tabbata ta sha maganin da matar zata karbo mata don kudi me yawa za’a saka a karbo. Tace kuma itama bata yarda da maganin gargajiya ba, kawai don ta matsu taga diyoyinka ne”. Zayyan sai ya rasa me zai ce ma. Amma ransa yafi na Sophie baci. Karshe ya kashe wayar bayan ya gama sauraron Sabah, yace “toh Sophie don Allah banda bakin baki hakuri, bani da kalmar baki hakuri, amma kiyi hakuri ki kuma kara akan naki”. Washegari da wuri ya daukesu zuwa Dandume, don kada a kara bata mata rai a gidansu. Ya kaisu har cikin gida ya shiga ya gaida Ammi da Malam. Yayi musu godiyar aron ‘yammatan gidan da aka basu na lokaci mai tsaho. Bai jima sosai ba ya fito yace ma Safiyyah ta kwana da Ammi, sai gobe zai dawo ya dauketa su wuce Abuja. Ammi kam ta san halin yaranta ta iya karantarsu su duka, da ganinsu kuma ta san wani abu ya faru a Rafindadi, amma dai bata ce komai ba, ta barsu a hakan. Suma basu tada zancen ba sai wanda ya shafesu. Yana komawa gida ya tarar da Mama tana zaune ita kadai, mai aikinta Ankudi nata tattare mata falon da bakinta suka bata. Ya shigo ya zauna a gajiye, yana ta kumburi, ya gaisheta, sai ya koma gefe yayi shiru, Mama tace “a kawo maka abinci ne?” Ya ce “a koshe nake Mama”. Mai aikin na fita yace, “Please Mama me ya faru tsakanin Safiyyah da mutanenki a gidannan?” Mama tayi salati ta sallame tace. “Koda naji! Ai dama na san za’a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Toh Sannu ubana, nace sannu ubana da ya haifi uwata, matse bakina sai in gaya maka tunda tuhumar abinda ya bata ran matarka ne ya kawo ka ba gaisheni ba. Sallamamme kawai, kaje kauye an wanke ka a minjaye an baka ka shanye, an aikoka ka mun rashin kunya ko, toh ba zan fadi me ya faru ba duk yadda tace maka hakan akayi, akwai abunda zakayi ne? Ko karya ake mata ta haihu dinne? Da ta haihu za’a yi mata zancen amso magani? Ka amsa ni mana, rasa kunya beran tanka? Ai wallahi Baffa mu zuba ni da kai, in dai jimirinka matar ka ta fada maka abu kazo ka tuhumeni to tayi kadan, ko uwarta bata isa ba. Baffa anya kuwa lafiyarka kalau?” Sai Mama ta hau matse ido tana fadin, “Safiyyah ta kai Babanta Makkah da kudinka, addu’arsa taci akanka Baffa, an janye min kai bakidaya”. Kawai yayi shiru, ranshi na kuna, yace “Mama haihuwar nan fa Allah ke bayarwa ba mutum ba, ba dabararshi ba. Babu wanda ya janye miki ni Mama, amma Mama ki dinga yi wa Sophie uzuri akan lamarin haihuwarnan, tunda dai ba dabararta ce zata bata ba. Kuma wallahi Mama ta fi ki son ta haifa miki jika, amma Mama ace bama ke ba wasu daban suna shiga cikin maganar haihuwarta saboda kin basu fuska ai bai dace ba, ina dai ce Safiyyah tayi haihuwar nan ba jimawa kowa ya shaida tana haihuwar? Allah ne yayi hukuncinsa a kai dagabaya? Shin Mama wannan bai isa wanke mata zargin rashin haihuwa da gorin ta ba?”. Mama salatinta da sallaminta ya karu, tace “yau Baffa dani kake sa’insa akan matarka, don ance za’a taimaka mata da maganin haihuwa? Ai kuwa baku so zaman lafiya dani ba. Nabi haihuwar da ta yin da gudu mai kama da babu na tattake ba takalmi a kafa ta!”. Ganin Mama ta taso gabadaya kamar zata rufe shi da duka sai ya kwantar da
Chapter 18 · 0% Book details